Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 26

Allah Wanda Yake da “Hanzarin Gafartawa”

Allah Wanda Yake da “Hanzarin Gafartawa”

1-3. (a) Wane kaya mai nauyi ne mai Zabura Dauda ya ɗauka, kuma ta yaya ya samu lallami ga wahalar zuciyarsa? (b) Idan muka yi zunubi, wane nauyi ne za mu ɗauka domin wannan, amma menene Jehovah ya tabbatar mana?

“KURAKURAINA sun sha kaina,” haka mai Zabura Dauda ya rubuta. “Kamar kaya mai-nauyi sun fi ƙarfina. Na yi suwu, na ƙuƙuje ƙwarai.” (Zabura 38:4, 8) Dauda ya san yadda lamiri mai laifi yake da nauyi. Amma ya samu lallami ga wahalar zuciyarsa. Ya fahimci cewa ko da yake Jehovah yana ƙin zunubi, ba ya ƙin mai zunubi idan wannan ya tuba da gaske ne kuma ya guje wa tafarkin zunubi. Da cikakkiyar bangaskiya cewa Jehovah yana shirye ya yi jinƙai ga wanda ya tuba, Dauda ya ce: “Kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa.”—Zabura 86:5.

2 Sa’ad da muka yi zunubi, mu ma za mu ɗauki nauyin lamiri mai ciwo. Wannan yin nadama tana da kyau. Za ta sa mu yi ƙoƙarin gyara halinmu. Amma, da akwai haɗarin nauyaya domin zunubi. Zuciyarmu mai hukunci za ta iya nacewa cewa Jehovah ba zai gafarta mana ba, ko yaya muka tuba. Idan muka ‘nitse’ cikin baƙin cikin laifi, Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya sa mu fid da rai, ta jin cewa Jehovah yana ganinmu marasa amfani, waɗanda ba su cancanci bauta masa ba.—2 Korinthiyawa 2:5-11.

3 Haka ne Jehovah yake ɗaukan al’amura? A’a! Gafartawa ɓangare ne na ƙauna mai girma ta Jehovah. A cikin Kalmarsa, ya tabbatar mana cewa idan muka nuna tuba ta gaskiya daga zuciyarmu, a shirye yake ya gafarta. (Misalai 28:13) Domin mu guje wa jin cewa gafarar Jehovah aba ce da ba za mu taɓa samu ba, bari mu bincika abin da ya sa yake gafartawa da kuma yadda yake gafartawa.

Dalilin da Ya Sa Jehovah Yake da “Hanzarin Gafartawa”

4. Menene Jehovah yake tuna game da yanayinmu, kuma ta yaya wannan yake shafar yadda yake bi da mu?

4 Jehovah yana sane da kasawarmu. “Ya san tabi’armu; Ya kan tuna mu turɓaya ne,” in ji Zabura 103:14. Ba ya manta cewa mu halittu ne daga turɓaya, masu kumamanci, domin ajizanci. Furcin nan ya san “tabi’armu” yana tuna mana cewa Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehovah da maginin tukwane mu kuma an kwatanta mu da tukwanen yumɓu da ya gina. * (Irmiya 18:2-6) Maginin Tukwane Mai Girma yana sauƙaƙa yadda yake bi da mu bisa ga kumamancinmu na zunubi da yadda muka amsa kuma da yadda muka ƙi bin ja-gorarsa.

5. Yaya littafin Romawa ya kwatanta ikon danƙewa na zunubi?

5 Jehovah ya fahimci yadda zunubi yake da tasiri. Kalmarsa ta kwatanta zunubi da cewa iko ne mai ƙarfi da ya danƙe mutum. Yaya ƙarfin danƙewarsa? A cikin littafin Romawa, manzo Bulus ya yi bayani: Muna “ƙarƙashin zunubi” kamar sojoji ƙarƙashin kwamandansu (Romawa 3:9); zunubi ya yi “mallaka” bisa ’yan Adam kamar sarki (Romawa 5:21); yana “zaune,” cikinmu (Romawa 7:17, 20); “shari’a” nasa tana aiki a cikinmu kullayaumi, watau, yana ƙoƙarin ya ja-goranci tafarkinmu. (Romawa 7:23, 25) Lalle zunubi ya danƙe jikinmu ajizi!—Romawa 7:21, 24.

6, 7. (a) Yaya Jehovah yake ganin waɗanda suke biɗan jinƙansa da zuciya mai nadama? (b) Me ya sa ba za mu ɗauki jinƙan Allah dalilin zunubi ba?

6 Jehovah ya sani cewa cikakkiyar biyayya ba za ta yiwu ba, ko yaya muke so mu kasance da cikakkiyar biyayya a gare shi. Ya tabbatar mana cikin ƙauna cewa sa’ad da muka nemi jinƙansa da zuciya mai nadama, zai gafarta mana. Zabura 51:17 ta ce: “Hadayu na Allah karyayyen ruhu ne: karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” Jehovah ba zai taɓa ƙin, ko kuma ya kori, zuciya da ta ‘karaya ta ƙuƙuje’ domin nauyin alhakin laifi ba.

7 Wannan yana nufi ne cewa za mu ɗauki jinƙan Allah banza, dalilin yin zunubi? A’a! Ba motsin rai ba ne yake rinjayar Jehovah. Jinƙansa yana da iyaka. Ba zai taɓa gafarta wa waɗanda suke zunubi domin taurin zuciya ba, ba sa nuna tuba. (Ibraniyawa 10:26) A wani ɓangare kuma, idan ya ga zuciya da take nadama, yana shirye ya gafarta. Bari yanzu mu ga wasu kalmomi da aka yi amfani da su a cikin Littafi Mai Tsarki wajen kwatanta wannan ɓangare na ban sha’awa na ƙaunar Jehovah.

Jehovah Yana Gafartawa Gabaki Ɗaya Kuwa?

8. Menene Jehovah yake yi sa’ad da yake gafarta mana zunubanmu, kuma wane tabbaci ne wannan yake ba mu?

8 Dauda da ya tuba ya ce: “Na ɗauki zunubina a gabanka; ban ɓoye muguntata ba . . . kai ma ka gafarta muguntar zunubina.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 32:5) Kalmar nan “gafarta” ta fassara kalmar Ibrananci da ainihi take nufi “ɗaga” ko kuma “ɗauka.” Amfani da ita a nan tana nuna ɗauke “alhakin laifi, saɓo, zunubi.” Watau, Jehovah ya ɗaga zunubin Dauda ne, ya kawar da su. Wannan babu shakka ya sauƙaƙa alhakin laifin da Dauda yake ɗauke da shi. (Zabura 32:3) Mu ma za mu iya kasancewa da cikakken tabbaci ga Allah wanda yake ɗaukan zunubin waɗanda suka nemi gafararsa bisa bangaskiyarsu ga hadayar fansa ta Yesu.—Matta 20:28.

“Zunubanku . . . za su zama kamar [dusar ƙanƙara]”

9. Yaya nisan yadda Jehovah yake kawar da zunubinmu daga gare mu yake?

9 Dauda ya yi amfani da wani furci ya kwatanta gafartawa ta Jehovah: “Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Zabura 103:12) Yaya nisan gabas daga yamma yake? Nisan gabas daga yamma ba ta da iyaka; waje biyun ba za su taɓa haɗuwa ba. Wani manazarci ya lura cewa wannan furcin yana nufin “yadda nisan ya yiwu; nisan da za mu iya tunaninsa.” Hurarrun kalmomin Dauda sun gaya mana cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, yana kawar da zunubanmu da nisa yadda ba za mu yi tsammani ba daga gare mu.

10. Sa’ad da Jehovah ya gafarta mana zunubanmu, me ya sa bai kamata mu ji cewa muna ɗauke da tabon wannan zunubin ba a duk rayuwarmu?

10 Ka taɓa ƙoƙarin cire datti daga farar riga? Wataƙila duk da ƙoƙarinka dattin ya kasance ana gani. Ka lura yadda Jehovah ya kwatanta yawan yadda yake gafartawa: “Ko da zunubanku sun yi kamar mulufi, za su yi fari kamar [dusar ƙanƙara]: ko da suna ja wur kamar garura, za su zama kamar auduga.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ishaya 1:18) Kalmar nan “mulufi” tana nufin launi ja mai haske. * “Garura” tana nufin launi mai duhu na kayan rini. (Nahum 2:3) Ba za mu taɓa iya cire tabon zunubi ba ta wajen ƙoƙarinmu. Amma Jehovah zai iya ɗaukar zunuban da suke kama da mulufi da garura ya mai da su fari fat kamar dusar ƙanƙara ko ulu da ba a rine ba. Sa’ad da Jehovah ya gafarta mana zunubanmu, ba ma bukatar jin cewa muna ɗauke da tabon wannan zunubi a duk rayuwarmu.

11. A wace hanya ce Jehovah yake yar da zunubi a bayansa?

11 A waƙar godiya da Hezekiah ya yi bayan an ceci ransa daga ciwon ajali, ya ce wa Jehovah: “Ka yarda zunubaina duka a bayanka.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Ishaya 38:17) A nan an nuna cewa Jehovah yana ɗaukan zunuban masu laifi da suka tuba ya yar da su a bayansa inda ba zai gansu ba ko kuma ya lura da su. In ji wata majiya, za a iya furta abin da ake nufi haka: “Ka mayar da [zunubai na] kamar ba su taɓa faruwa ba.” Wannan ba yana da ban ƙarfafa ba?

12. Yaya annabi Mikah ya nuna cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, Ya ɗauke zunubanmu dindindin?

12 A cikin alkawarin maidowa, annabi Mikah ya furta tabbacinsa cewa Jehovah zai gafarta wa mutanensa da suka tuba: “Wanene Allah makwatancinka, . . . wanda ya rufe laifi na ringin mutanen gadōnsa? . . . za ka zubarda zunubansu duka cikin zurfin teku.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Mikah 7:18, 19) Ka yi tunanin abin da kalmomin nan suke nufi ga waɗanda suke a zamanin Littafi Mai Tsarki. Zai yiwu ne a maido da abin da aka riga aka jefa “cikin zurfin teku”? Saboda haka, kalmomin Mikah sun nuna cewa sa’ad da Jehovah ya gafarta, ya ɗauke zunubanmu dindindin.

13. Menene ma’anar kalmomin Yesu “Ka gafarta mana basusuwanmu”?

13 Yesu ya yi amfani da dangantaka da ke tsakanin mai ba da bashi da mai cin bashi ya kwatanta gafartawa ta Jehovah. Yesu ya aririce mu mu yi addu’a: “Ka gafarta mana basusuwanmu.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Matta 6:12) Saboda haka Yesu ya kwatanta zunubi da bashi. (Luka 11:4) Sa’ad da muka yi zunubi mun zama “mabarta” ga Jehovah. Game da kalmar Helenanci da aka fassara “gafarta,” wani littafin neman bayani ya ce: “A ƙyale, a bar bashi, ta wajen ƙin neman a biya bashin.” Watau, sa’ad da Jehovah ya yi gafara, ya yafe bashin da yake binmu ne. Saboda haka masu zunubi da suka tuba sai su ƙarfafa. Jehovah ba zai taɓa neman a biya bashin da ya yafe ba!—Zabura 32:1, 2.

14. Furcin “domin a shafe zunubanku” yana sa mutane su yi tunanin me?

14 Gafartawar Jehovah an ƙara kwatanta ta a Ayyukan Manzanni 3:19: “Ku tuba fa, ku juyo, domin a shafe zunubanku.” (Tafiyar tsutsa tamu ce.) Wannan kalmar ta kusa da ta ƙarshen ta fassara aikatau na Helenanci da yake nufin “gogewa, . . . kashe ko kuma halaka.” In ji wasu manazarta, ma’anar furcin na goge rubutun hannu ne. Ta yaya wannan zai yiwu? Tawadar da ake yin amfani da ita a zamanin dā ana yin ta ne da gawayi, ƙaro, da kuma ruwa. Ba da daɗewa ba bayan rubutu da wannan tawadar, mutum zai iya ɗaukan jiƙaƙƙen tsumma ya goge rubutun. A cikin wannan akwai kwatanci na jinƙan Jehovah. Idan ya gafarta mana zunubanmu, kamar ya ɗauki tsumma ne ya goge su.

Jehovah yana so mu sani cewa yana da “hanzarin gafartawa”

15. Menene Jehovah yake so mu sani game da shi?

15 Idan muka yi waswasi bisa waɗannan kwatanci dabam dabam, ba a bayyane yake ba cewa Jehovah yana son mu sani cewa da gaske yana shirye ya gafarta mana zunubi tun da ya ga mun tuba da gaske? Ba ma bukatar mu ji tsoro cewa zai riƙe mu domin waɗannan zunuban a nan gaba. Wannan ya bayyana a wani abu da Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da jinƙai mai girma na Jehovah: Sa’ad da ya gafarta, ya manta.

“Ba Ni Kuwa Ƙara Tuna da Zunubinsu Ba”

16, 17. Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Jehovah ya manta da zunubanmu, menene yake nufi, kuma me ya sa ka ba da wannan amsar?

16 Jehovah ya yi alkawari game da waɗanda suke cikin sabon alkawari: “Zan gafarta muguntarsu, ba ni kuwa ƙara tuna da zunubinsu ba.” (Irmiya 31:34) Wannan yana nufi ne cewa idan Jehovah ya gafarta ba zai iya tuna da zunubai ba kuma? Da ƙyar ya zama haka. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da zunubai na mutane da yawa da Jehovah ya gafarta, har da Dauda. (2 Samu’ila 11:1-17; 12:13) A bayyane yake cewa Jehovah har yanzu yana sane da zunubi da suka yi. Tarihin zunubansu, da kuma tuba da gafarar Allah, duka an adana domin amfaninmu. (Romawa 15:4) To, menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce Jehovah ba ya “tuna” zunuban waɗanda ya gafarta musu?

17 Aikatau na Ibrananci da aka fassara “zan tuna” yana nufi fiye da kawai tuna abin da ya wuce. Theological Wordbook of the Old Testament ya lura cewa ya haɗa da “ɗaukan mataki da ya dace.” Saboda haka, a nan, “tuna” zunubi ya haɗa da ɗaukan matakin gāba da masu zunubin. (Hosea 9:9) Amma da Allah ya ce “ba ni ƙara tuna da zunubinsu,” yana tabbatar musu ne cewa da zarar ya gafarta wa masu zunubi da suka tuba, ba zai ɗauki mataki ba gāba da su domin wannan zunubin. (Ezekiel 18:21, 22) Mantuwa da Jehovah yake yi ita ce watau ba zai sake ta da batun ba domin ya tuhume mu ko ya yi mana horo dominsa sau da yawa. Ba abin ƙarfafa ba ne mu sani cewa Allahnmu yana gafartawa kuma ya manta?

To Yaya Batun Hakkin Zunubin?

18. Me ya sa gafartawa ba ya nufin cewa mai zunubi da ya tuba ya wanku daga hakkin zunubinsa?

18 Kasancewar Jehovah a shirye ya gafarta tana nufi ne cewa mai zunubi da ya tuba ya wanku daga dukan hakkin tafarkinsa na saɓo? A’a. Ba za mu yi zunubi ba kuma mu yi tunanin ba abin da zai same mu. Bulus ya rubuta: “Iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” (Galatiyawa 6:7) Za mu fuskanci wasu hakkin halayenmu. Wannan ba ya nufin cewa bayan ya gafarta mana Jehovah zai sa bala’i ya faɗo mana. Sa’ad da masifa ta faɗo, kada Kirista ya yi tsammanin cewa, ‘Wataƙila Jehovah ne yake yi masa horo domin zunubinsa na dā.’ (Yaƙub 1:13) A wani ɓangare kuma, Jehovah ba ya kāre mu daga sakamakon munanan ayyukanmu. Kashe aure, cikin shege, cututtuka daga jima’i, da kuma rashin yarda ko kuma daraja—dukan waɗannan abin baƙin cikin da za su iya kasancewa sakamakon da ba makawa ne na zunubi. Ka tuna cewa bayan ma ya gafarta wa Dauda zunubinsa game da Bath-sheba matar Uriah, Jehovah bai kāre Dauda daga sakamako na bala’i da ya biyo baya ba.—2 Samu’ila 12:9-12.

19-21. (a) Ta yaya doka da take rubuce a Leviticus 6:1-7 ta amfani wanda aka cuta da wanda ya yi cuta? (b) Idan zunubinmu ya ɓata wa wasu rai, Jehovah zai yi farin ciki idan muka ɗauki wane mataki?

19 Zunubanmu za su kasance da ƙarin hakki, musamman ma idan abin da muka yi ya ɓata wa wasu rai. Alal misali, ka yi la’akari da abin da ke Leviticus sura 6. A nan Dokar Musa ta yi magana ne bisa yanayi da mutum ya yi zunubi mai tsanani ta wajen ƙwace kayan ɗan’uwansa Ba’isra’ile ko ta wajen fashi, zamba ko damfara. Kuma mai zunubi ya musanta laifinsa, har ya kai ga rantsuwar ƙarya. Inda kalmar mutum ɗaya ta saɓa ne da ta ɗayan. Amma, daga baya sai mai zunubin lamirinsa ya dame shi ya yi ikirarin zunubinsa. Domin ya samu gafarar Allah, yana bukatar ya yi abubuwa uku: ya maida abin da ya ɗauka, ya biya wanda ya ɗauki abin sa diyyar kashi 20 na abin da ya sata, kuma ya ba da rago domin hadaya ta zunubi. Sai dokar ta ce: “[Firist] kuma za ya yi kafara dominsa a gaban Ubangiji; za a kuwa gafarta masa.”—Leviticus 6:1-7.

20 Dokar tanadi ne jinƙai daga Allah. Tana amfanar wanda aka cuta, wanda aka mai da masa da kayansa kuma babu shakka zai samu sauƙi sa’ad da mai laifin ya yarda da laifinsa. Har ila kuma, dokar ta amfani wanda lamirinsa a ƙarshe ya motsa shi ya yarda da laifinsa kuma ya gyara halinsa. Idan ya ƙi ya yi haka, to babu wata gafara dominsa daga wajen Allah.

21 Ko da yake ba ma ƙarƙashin Dokar Musa, Dokar ta ba mu fahimi cikin azancin Jehovah, haɗe da tunaninsa game da gafara. (Kolossiyawa 2:13, 14) Idan zunubinmu ya ɓata wa wasu rai, Allah zai yi farin ciki idan muka yi iyakar ƙoƙarinmu domin gyara halinmu. (Matta 5:23, 24) Wannan zai haɗa da fahimtar zunubinmu, yarda da shi, da kuma ba wa wanda ya cutu haƙuri. Sa’an nan za mu yi addu’a ga Jehovah bisa hadayar Yesu kuma mu samu tabbacin cewa ya gafarta mana.—Ibraniyawa 10:21, 22.

22. Menene zai raka gafarar Jehovah?

22 Kamar uba mai ƙauna, Jehovah yana yin gafara tare da ɗan horo. (Misalai 3:11, 12) Kirista da ya tuba zai bukaci ya tuɓe matsayinsa na dattijo, bawa mai hidima, ko kuma mai wa’azi na cikakken lokaci. Zai kasance da zafi a gare shi ya yi rashin gata da yake so ƙwarai. Amma irin wannan horo, ba ya nufin cewa Jehovah ya hana gafara. Dole ne mu tuna cewa horo daga Jehovah tabbaci ne na ƙaunarsa. Karɓa da kuma yin amfani da shi domin amfaninmu ne.—Ibraniyawa 12:5-11.

23. Me ya sa bai kamata mu kammala ba cewa ba mu kai Jehovah ya yi mana jinƙai ba, kuma me ya sa ya kamata mu yi koyi da gafararsa?

23 Lalle yana da wartsakewa mu sani cewa Allah yana da “hanzarin gafartawa”! Duk da kuskure da muka riga muka yi, kada mu kammala da cewa ba mu kai Jehovah ya yi mana jinƙai ba. Idan mun tuba da gaske, mun ɗauki matakai mu gyara halayenmu, kuma muka yi addu’a domin gafara bisa jinin da Yesu ya zubar, to za mu tabbata cewa Jehovah zai gafarta mana. (1 Yohanna 1:9) Bari mu bincika gafararsa a sha’aninmu da juna. Domin ma, idan Jehovah wanda ba ya zunubi, ya gafarta mana cikin ƙauna, bai kamata mu mutane masu zunubi mu gafarta wa juna ba?

^ sakin layi na 4 Kalmar Ibrananci da aka fassara “tabi’armu” an yi amfani da ita ga tukwanen yumɓu da maginin tukwane yake ginawa.—Ishaya 29:16.

^ sakin layi na 10 Wani manazarci ya ce mulufi “launi ne da ba ya wankewa. Ba raɓa, ba ruwan sama, ba kuma wanki ba, ko kuma yawan amfani da zai iya ya fid da shi.”