Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 3

Wanda Ya Halicci Dukan Abubuwa

Wanda Ya Halicci Dukan Abubuwa

Waye ya yi dukan abubuwa masu rai?

NA SAN wani abin mamaki. Za ka so ka ji wannan?— Ka dubi hannunka. Ka naɗe yatsunka. Yanzu ka ɗauki wani abu. Hannunka yana abubuwa masu yawa, kuma yana yin su daidai. Ka san wanda ya yi hannayenka?—

E, shi ne Wanda ya yi bakinmu, hancinmu, da kuma idanunmu. Allah ne, Uban Babban Malami. Ba ma farin ciki cewa Allah ya ba mu idanu?— Muna ganin abubuwa da yawa da su. Muna iya kallon furanni. Muna iya kallon ciyayi kore shar da kuma sama shuɗiya. Muna iya ganin ƙaramin tsuntsu ma yana cin abinci kamar wanda yake hoton nan. Lallai, yana da kyau da muna iya ganin irin waɗannan abubuwa, ko ba haka ba?—

Amma waye ya halicci waɗannan abubuwa? Wasu mutane ne suka yi su? A’a. Mutane suna iya gina gida. Amma babu mutumin da zai iya yin ciyawa da take girma. Mutane ba za su iya yin ɗan tsuntsu ba, ko fure, ko kuma wani abu mai rai. Ka san da haka?—

Allah ne Wanda ya yi dukan waɗannan abubuwa. Allah ya halicci sammai da ƙasa. Ya halicci mutane ma. Ya halicci namiji da tamace na farko. Yesu, Babban Malami, ya koyar da wannan.—Matta 19:4-6.

Ta yaya Yesu ya sani cewa Allah ya yi namiji da tamace? Yesu ya ga Allah yana yi ne?— Hakika kuwa. Yesu yana tare da Allah sa’ad da Allah ya yi namiji da tamace na farko. Yesu shi ne wanda Allah ya yi da farko. Yesu mala’ika ne, kuma ya rayu a sama da Ubansa.

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ya ce: “Bari mu yi mutum a cikin surarmu.” (Farawa 1:26) Ka san wanda Allah yake magana da shi?— Yana magana ne da Ɗansa. Yana magana ne da wanda daga baya ya zo duniya ya zama Yesu.

Wannan ba abin mamaki ba ne? Ka yi tunani! Idan mun saurari Yesu, wanda yake tare da Allah sa’ad da Allah yake yin duniya da dukan abubuwa shi ne yake koyar da mu. Yesu ya koyi abubuwa da yawa wajen aiki da Ubansa a sama. Babu shakkar da Yesu shi ne Babban Malami!

Kana tsammani Allah ba ya jin daɗi ne shi kaɗai kafin ya halicci Ɗansa?— Yana jin daɗi. To, idan yana jin daɗi, me ya sa ya yi wasu abubuwa masu rai?— Ya yi wannan ne domin shi Allah ne na ƙauna. Yana son wasu su rayu su mori rayuwa. Ya kamata mu gode wa Allah da ya ba mu rai.

Dukan abin da Allah ya yi ya nuna ƙaunarsa. Allah ya yi rana. Rana tana ba mu haske kuma tana ɗimama mu. Kome zai yi sanyi kuma rai ba zai kasance ba a duniya ba idan ba domin rana ba. Ba ka farin ciki ne cewa Allah ya yi rana?—

Allah ne yake sa a yi ruwan sama. Wani lokaci ba ka sonsa ma domin ba za ka iya fita waje ba ka yi wasa. Amma ruwan saman yana taimakon furanni su yi girma. Saboda haka idan muka ga furanni masu kyau, waye za mu yi wa godiya dominsu?— Allah. Kuma wa za mu yi wa godiya sa’ad da muka ci ’ya’yan itace da ganye da yake da santi?— Ya kamata mu yi wa Allah godiya domin ranarsa ce da kuma ruwan samansa ne suke sa abubuwa su yi girma.

A ce wani ya tambaye ka: ‘Allah ne ya yi mutum da kuma dabbobi?’ Me za ka ce?— Daidai ne ka ce: “E, Allah ne ya yi mutum da dabbobi.” Amma idan mutumin bai gaskata cewa Allah ne ya yi mutum da gaske ba fa? Idan kuma shi ko ita ta ce mutum ya zo ne daga dabbobi kuma fa? A’a, Littafi Mai Tsarki bai koyar da wannan ba. Ya ce Allah ne ya halicci dukan abubuwa.—Farawa 1:26-31.

Tun da wani ne ya yi gida, waye ya yi fure, itatuwa, da kuma dabbobi?

Amma wani zai ce maka bai gaskata da Allah ba. To, me za ka ce?— Me ya sa ba za ka nuna wani gida ba? Ka tambayi mutumin: “Waye ya gina wannan gidan?” Kowa ya sani cewa wani ne ya gina gidan. Hakika gidan bai gina kansa ba!—Ibraniyawa 3:4.

Sai ka kai mutumin lambu ka nuna masa fure. Ka tambaye shi: “Waye ya yi wannan?” Ba mutum ba ne ya yi. Kuma kamar yadda gida bai yi kansa ba haka wannan furen bai yi kansa ba. Wani ne ya yi shi. Allah ne ya yi su.

Ka ce wa mutumin ya tsaya ya saurari kukan tsuntsu. Sai ka tambaye shi: “Waye ya yi tsuntsun kuma ya koya masa yin kuka?” Allah ne ya yi hakan. Allah ne ya yi sama da ƙasa da kuma dukan abubuwa da rayayyu ne! Shi ne Wanda yake ba da rai.

Duk da haka, wani zai ce shi ya gaskata ne da abin da yake gani kawai. Zai iya cewa: ‘Idan ban gan shi ba, ba zan gaskata da shi ba.’ Wasu mutane sun ce ba su gaskata da Allah ba domin ba sa iya ganinsa.

Gaskiya ne ba za mu iya ganin Allah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Babu mutumin da zai iya ganin Allah.’ Babu namiji, tamace, ko yaro a duniya da zai iya ganin Allah. Saboda haka, kada kowa ya yi ƙoƙarin zana hoto ko siffar Allah. Allah kansa ya ce kada mu yi siffarsa. Saboda haka, Allah ba zai yi farin ciki ba idan muna da irin waɗannan abubuwan a gidanmu.—Fitowa 20:4, 5; 33:20; Yohanna 1:18.

Amma idan ba za ka iya ganin Allah ba, ta yaya ka sani da gaske cewa akwai Allah? Ka yi tunanin wannan. Za ka iya ganin iska?— A’a. Babu mutumin da zai iya ganin iska. Amma kana iya ganin abin da iska take yi. Kana ganin ganye suna motsi sa’ad da iska ta busa reshen itace. Saboda haka ka gaskata cewa da akwai iska.

Ta yaya ka sani cewa da akwai iska?

Kana iya ganin abin da Allah ya yi. Sa’ad da ka ga fure mai rai da kuma tsuntsu, ka ga abin da Allah ya yi. Saboda haka ka gaskata da gaske cewa da akwai Allah.

Wani zai iya tambayarka, ‘Waye ya yi rana da kuma duniya?’ Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ya halitta sama da ƙasa.” (Farawa 1:1) Hakika, Allah ya yi dukan abubuwa masu ban mamaki! Yaya kake ji game da wannan?—

Ba shi da kyau ne mu kasance a raye? Za mu iya jin kuka mai daɗi na tsuntsaye. Za mu iya ganin furanni da kuma wasu abubuwa da Allah ya halitta. Kuma za mu iya cin abinci da Allah ya ba mu.

Domin dukan waɗannan abubuwa, ya kamata mu yi wa Allah godiya. Fiye da haka ma, ya kamata mu yi masa godiya domin ya ba mu rai. Idan muna godiya ga Allah da gaske, za mu yi wani abu. Menene wannan?— Za mu saurari Allah, kuma za mu yi abin da ya gaya mana a cikin Littafi Mai Tsarki. Ta wannan hanyar za mu nuna cewa da gaske muna ƙaunar Wanda ya yi dukan abubuwa.

Ya kamata mu yi wa Allah godiya domin dukan abin da ya yi. Ta yaya? Ka karanta abin da yake rubuce cikin Zabura 139:14; Yohanna 4:23, 24; 1 Yohanna 5:21; da kuma Ru’ya ta Yohanna 4:11.