Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 4

Allah Yana da Suna

Allah Yana da Suna

MENENE sau da yawa kake tambayar wani sa’ad da ka sadu da shi da farko?— Sunansa kake tambaya. Dukanmu muna da suna. Allah ya ba wa mutum na farko a duniya suna. Ya kira shi Adamu. Matar Adamu an kira ta Hauwa’u.

Ba mutane ba ne kawai suke da sunaye. Ka yi tunanin wasu abubuwa da ke da sunaye. Sa’ad da wani ya ba ka kare, za ka ba shi suna, ko ba haka ba?— Hakika, suna yana da muhimmanci.

Ka ɗaga ido ka ga taurari masu dumbin yawa daddare. Kana tsammanin suna da suna?— E, Allah ya ba kowanne tauraro suna. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Yana ƙididigan yawan taurari; dukansu yana ba su sunayensu.”—Zabura 147:4.

Ka san cewa dukan taurari suna da sunansu?

Waye za ka ce ya fi kowa a dukan sararin samaniya?— Hakika, Allah ne. Kana tsammanin yana da suna?— Yesu ya ce Yana da shi. Yesu ya taɓa ce wa Allah cikin addu’a: ‘Na sanar da sunanka zuwa ga mabiyana.’ (Yohanna 17:26) Ka san sunan Allah?— Allah da kansa ya gaya mana sunansa. Ya ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne.” Saboda haka, sunan Allah JEHOVAH ne.—Zabura 83:18.

Yaya kake ji idan wasu suka tuna da sunanka?— Kana farin ciki, ko ba haka ba?— Jehovah ma yana son mutane su san sunansa. Saboda haka mu yi amfani da sunan nan Jehovah sa’ad da muke magana game da Allah. Babban Malami ya yi amfani da sunan Allah, Jehovah, sa’ad da yake magana da mutane. Wata rana Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar [Jehovah] Allahnka da dukan zuciyarka.”—Markus 12:30.

Yesu ya sani cewa “Jehovah” suna ne mai muhimmanci ƙwarai. Saboda haka ya koyar da mabiyansa su yi amfani da sunan Allah. Har ya koyar da su su kira sunan Allah a cikin addu’o’insu. Yesu ya san cewa Allah yana son dukan mutane su san Sunansa, Jehovah.

A dā can Allah ya nuna muhimmancin sunansa ga Musa, wanda yana ɗaya daga cikin ’ya’yan Isra’ila. ’Ya’yan Isra’ila da ake kiransu Isra’ilawa, sun zauna a ƙasar da ake kiranta Masar. Mutanen wannan ƙasar ana kiransu Masarawa. Sun mai da Isra’ilawan bayi kuma suna cin zalinsu. Sa’ad da Musa ya yi girma, ya yi ƙoƙari ya taimaki wani ɗan’uwansa. Wannan ya ba Fir’auna, sarkin ƙasar Masar, haushi. Yana so ya kashe Musa! Saboda haka Musa ya gudu daga ƙasar Masar.

Musa ya je wata ƙasa. Ƙasar Midiya. A wajen Musa ya yi aure kuma ya fara haifan ’ya’ya. Kuma ya yi aikin kiwo, yana kiwon tumaki. Wata rana Musa yana kiwon tumaki a kusa da dutse sai ya ga abin mamaki. Kurmi yana cin wuta, amma ba ya ƙonewa! Musa ya ratsa domin ya gani da kyau.

Ka san abin da ya faru?— Musa ya ji murya daga tsakiyar kurmin. Muryar ta yi kira, “Musa! Musa!” Wa yake wannan kira?— Allah ne yake magana! Allah yana da ayyuka da yawa da Musa zai yi. Allah ya ce: ‘Zo in aike ka ga Fir’auna, sarkin Masar, ka fito da mutanena, ’ya’yan Isra’ila, daga ƙasar Masar.’ Allah ya yi alkawari zai taimaki Musa ya yi hakan.

Wane abu ne mai muhimmanci Musa ya koya daga kurmi da wuta ke ci?

Amma Musa ya gaya wa Allah: ‘Sa’anda na zo wurin ’ya’yan Isra’ila a ƙasar Masar na ce musu Allah ya aiko ni. In sun tambaye ni, ‘Menene sunansa?’ Me zan ce?’ Allah ya gaya wa Musa ya ce wa ’ya’yan Isra’ila: ‘Jehovah ya aiko ni wajenku, kuma ya ce Jehovah shi ne sunansa har abada.’ (Fitowa 3:1-15) Wannan ya nuna cewa Allah zai kasance da sunan nan Jehovah. Ba zai taɓa canja shi ba. Allah yana so a san shi da sunan nan Jehovah har abada.

Ta yaya Allah ya sanar da sunansa a Jar Teku?

Sa’ad da Musa ya koma ƙasar Masar, Masarawan suna tsammanin cewa Jehovah wani ɗan ƙaramin allah ne na Isra’ila. Ba su yi tunanin cewa shi ne Allahn dukan duniya ba. Saboda haka Jehovah ya gaya wa sarkin Masar: ‘Zan sanar da sunana kuma a cikin dukan duniya.’ (Fitowa 9:16) Hakika Jehovah ya sanar da sunansa. Ka san yadda ya yi haka?—

Ya sa Musa ya fito da mutanen Isra’ila daga ƙasar Masar. Sa’ad da suka isa Jar Teku, Jehovah ya yi musu busashiyar hanya ta cikin ruwan. Isra’ilawa suka bi kan busashiyar hanyar suka fita lafiya lau. Amma bayan da Fir’auna da dukan sojojinsa suka shiga cikin daben tekun, ruwa da aka tare a ɓangarori biyun suka rushe a kan Masarawa, kuma dukansu suka mutu.

Ba da daɗewa ba mutane a dukan duniya suka fara jin abin da Jehovah ya yi a Jar Teku. Ta yaya muka sani cewa sun ji?— Bayan shekara 40, Isra’ilawa suka isa ƙasar Kan’ana, ƙasar da Jehovah ya yi alkawari zai ba su. Rahab ta gaya wa Isra’ilawa maza guda biyu: “Mun ji yadda Ubangiji ya shanyadda ruwan Jan Teku a gabanku, lokacinda kuka fito Masar.”—Joshua 2:10.

A yau mutane da yawa kamar waɗannan Masarawan suke. Su ma ba su yarda da cewa Jehovah shi ne Allah na dukan duniya ba. Saboda haka Jehovah yana son mutanensa su gaya wa wasu game da shi. Wannan shi ne abin da Yesu ya yi. A lokacin da rayuwarsa ta kusan ƙarewa a duniya, ya gaya wa Jehovah cikin addu’a: “Na kuma sanar musu da sunanka.”—Yohanna 17:26.

Yesu ya sanar da sunan Allah. Za ka iya nuna inda sunan Allah yake a cikin Littafi Mai Tsarki?

Kana so ka zama kamar Yesu? To, ka gaya wa wasu cewa sunan Allah Jehovah ne. Za ka gani cewa mutane da yawa ba su san da haka ba. Wataƙila ka nuna nassi da ke cikin Littafi Mai Tsarki a Zabura 83:18. Bari mu ɗauki Littafi Mai Tsarki yanzu mu bincika nassin tare. Ya ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”

To, menene muka koya daga karanta wannan?— Mun koyi cewa Jehovah shi ne suna mafi muhimmanci. Sunan Allah Mai Iko Duka, Uban Yesu Wanda ya yi dukan abu. Kuma ka tuna cewa Yesu ya ce ya kamata mu yi ƙaunar Jehovah Allah da zuciya ɗaya. Kana ƙaunar Jehovah?—

Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Jehovah?— Hanya ɗaya ita ce ta wajen sanin cewa Aboki ne. Wata hanya kuma ta wajen gaya wa wasu sunansa ne. Za mu nuna musu a cikin Littafi Mai Tsarki cewa sunansa Jehovah ne. Za mu iya faɗan abubuwa na ban mamaki da Jehovah ya yi da kuma abubuwan kirki da ya yi. Wannan yana faranta wa Jehovah rai sosai domin yana so mutane su san shi. Za mu iya sa hannu a yin wannan, ko ba za mu iya ba ne?—

Ba kowa ba ne zai so ya saurara sa’ad da muke magana game da Jehovah. Mutane da yawa ba su saurara ba har sa’ad da Yesu, Babban Malami, yake magana game da Shi. Amma wannan bai hana Yesu magana game da Jehovah ba.

Saboda haka, bari mu zama kamar Yesu. Mu ci gaba da magana game da Jehovah. Idan muka yi, Jehovah zai yi farin ciki da mu, domin muna ƙaunar sunansa.

Yanzu ka karanta daga cikin Littafi Mai Tsarki wasu ayoyi da suka nuna muhimmancin sunan Allah: Ishaya 12:2, 4, 5; Ishaya 26:4; Matta 6:9; Yohanna 17:6; da kuma Romawa 10:13.