Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 6

Babban Malami Ya Yi wa Wasu Hidima

Babban Malami Ya Yi wa Wasu Hidima

KANA son wani ya yi maka wani abin kirki?— Hakika, mutane suna so wani ya yi musu wani abu mai kyau. Dukanmu muna so. Babban Malami ya san da haka, ko da yaushe yana yin abubuwa ga mutane. Ya ce: ‘Na zo ne ba don a yi mini hidima ba, amma domin ni in yi hidima.’—Matta 20:28.

Menene mabiyan Yesu suke gardama a kai?

Saboda haka, idan muna so mu zama kamar Babban Malami, menene dole ne mu yi?— Dole ne mu yi wa wasu hidima. Dole ne mu yi musu abin da yake da kyau. Gaskiya ne cewa mutane da yawa ba sa yin haka. Hakika, mutane da yawa ko da yaushe suna son mutane su yi musu hidima. Akwai lokacin da har mabiyan Yesu ma suka ji haka. Kowanne yana so ya zama babba ko kuma mafi muhimmanci.

Wata rana Yesu yana tafiya da almajiransa, waɗanda suke mabiyansa. Bayan sun shiga cikin birnin Kafarnahum, kusa da Kogin Galili, duka suka shiga cikin wani gida. Yesu ya tambaye su: “Gardamar me ku ke yi a kan hanya?” Suka yi tsit, domin a kan hanya sun yi gardama tsakaninsu game da wanda ya fi girma.—Markus 9:33, 34.

Yesu ya sani cewa ba daidai ba ne ga kowanne cikin almajiransa ya yi tunanin cewa shi ya fi girma. Saboda haka, kamar yadda muka koya a babi na farko na wannan littafi, ya tsayar da yaro ƙarami a tsakaninsu ya gaya musu su zama masu tawali’u kamar wannan yaron. Amma duk da haka ba su koya ba. Kusan ya mutu, Yesu ya koya musu darasi da ba za su taɓa mantawa ba. Menene ya yi?—

Sa’ad da suke cin abinci tare, Yesu ya tashi daga kan teburin kuma ya tuɓe rigarsa ya bar ’yar ciki. Ya ɗauki tawul ya ɗaure a kwankwasonsa. Sai ya ɗauki tasa ya zuba ruwa a ciki. Wataƙila mabiyansa suna mamakin abin da zai yi.

Sa’ad da almajiran suna kallonsa, Yesu ya zagaya dukansu, ya sunkuya ya wanke ƙafafuwansu. Sai ya bushar da su da tawul. Ka yi tunanin haka! Menene za ka yi idan kana wurin? Yaya za ka ji?—

Wane darasi Yesu ya koya wa mabiyansa?

Mabiyansa ba su ga ya dace ba Babban Malami ya yi musu hidima a wannan hanyar. Sun ji kunya. Bitrus bai yarda Yesu ya yi masa irin wannan hidima ba. Amma Yesu ya ce wannan yana da muhimmanci ya yi ta.

A yau ba ma wanke ƙafafun mutane. Amma wannan ana yi sa’ad da Yesu yake duniya. Ka san abin da ya sa?— A ƙasar da Yesu da mabiyansa suke zama, mutane sukan sa takalma a ƙafafunsu. Saboda haka sa’ad da suka yi tafiya a hanya mai ƙura, sai ƙafafunsu su yi datti. Kirki ne a wanke ƙafafun baƙon da ya shigo cikin gida.

Amma a wannan lokaci babu ko ɗaya cikin bayin Yesu da ya yarda ya wanke ƙafafun wasu. Saboda haka Yesu ya yi shi da kansa. Da ya yi wannan, Yesu ya koya wa mabiyansa muhimmiyar darasi. Suna bukatar su koyi wannan darasin. Kuma darasi ne da mu ma a yau muke bukatar mu koya.

Ka san menene darasin?— Bayan Yesu ya saka rigarsa kuma ya koma ya zauna, ya yi bayani: “Kun san abin da na yi muku? Kuna ce da ni Malami, da Ubangiji: kuna faɗi daidai kuma; gama haka ni ke. Idan fa ni, Ubangiji da Malami, na wanki sawayenku, ya kamata ku kuma ku wanki na juna.”—Yohanna 13:2-14.

Me za ka yi ka taimake wasu?

A nan Babban Malami ya nuna cewa yana son mabiyansa su yi wa wasu hidima. Ba ya so su yi tunani game da kansu kawai. Ba ya so su yi tunani cewa suna da muhimmanci ƙwarai, wasu ne ya kamata su yi musu hidima. Yana so su kasance a shirye su yi wa wasu hidima.

Wannan ba darasi ba ne mai kyau?— Za ka zama kamar Babban Malami ka yi wa wasu hidima?— Dukanmu za mu iya yin abubuwa ga wasu. Wannan zai faranta musu rai. Amma mafi kyau, zai sa Yesu da Ubansa farin ciki.

Ba shi da wuya mu yi wa wasu hidima. Idan ka lura za ka ga abubuwa da yawa da za ka iya yi wa wasu. Ka yi tunani yanzu: Da akwai wani abin da za ka iya yi ka taimaki mamarka? Ka san cewa tana yi maka abubuwa da yawa da kuma iyalinku. Za ka iya taimakonta?— Me ya sa ba za ka tambaye ta ba?

Wataƙila za ka shirya wajen da iyalinku za su ci abinci. Ko kuma ka tara kwanuka bayan iyalinku ta ci abinci. Wasu yara suna zuwa zubar da datti kowacce rana. Ko menene za ka iya yi kana yi wa wasu ne hidima, kamar yadda Yesu ya yi.

Kana da ƙanne maza da mata da za ka yi wa hidima? Ka tuna, Yesu Babban Malami ya yi wa har mabiyansa hidima. Ta wajen yi wa ƙannenka hidima kana yin koyi da Yesu ne. Menene za ka yi musu?— Wataƙila za ka koya musu su kwashe kayan wasansu bayan sun gama wasa. Ko kuma ka taimake su saka tufafinsu. Ko kuma wataƙila ka taimake su su je su yi barci. Za ka iya tunanin wani abin da za ka yi dominsu?— Za su yi ƙaunarka domin waɗannan abubuwa, kamar yadda mabiyan Yesu suka ƙaunace shi.

A makaranta ma za ka iya yi wa wasu hidima. Zai iya kasancewa ɗan ajinku ne ko kuma malaminku. Idan takardar wani ta fāɗi, zai kasance kirki a gare ka ka taimake shi ka ɗauka masa. Za ka so ka goge allo ko kuma ka yi wani abu ga malaminku. Buɗe ƙofa ma ga wasu hidima ce mai kyau.

A wani lokaci, za mu ga cewa mutane ba za su yi godiya ba ga hidimar da muka yi musu. Kana tsammanin wannan ya kamata ya hana ka yin nagarta?— A’a! Mutane da yawa ba su gode wa Yesu ba domin ayyuka masu kyau da ya yi. Amma wannan bai hana shi yin nagarta ba.

Saboda haka kada ka daina yin hidima ga wasu. Bari mu tuna da Babban Malami, Yesu, kuma koyaushe mu yi ƙoƙari mu bi misalinsa.

Domin ƙarin nassosi game da taimakon wasu mutane, ka karanta Misalai 3:27, 28; Romawa 15:1, 2; da kuma Galatiyawa 6:2.