Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 27

Waye ne Allahnka?

Waye ne Allahnka?

ME YA sa wannan tambayar, Waye ne Allahnka? take da muhimmanci?— Domin mutane suna bauta wa alloli da yawa. (1 Korinthiyawa 8:5) Sa’ad da manzo Bulus ya sami iko daga wurin Jehovah ya warkar da wani mutum da bai taɓa tafiya ba, mutane suka yi kuwwa, suka ce: “Allohi sun sauko a wurinmu da kamanin mutane.” Mutanen suna so su bauta wa Bulus da abokinsa Barnaba. Suka kira Bulus Hamasa, Barnaba kuma suka kira shi Zafsa, waɗannan sunayen allolin ƙarya ne.

Amma Bulus da Barnaba ba su ƙyale mutanen sun bauta musu ba. Suka ruga cikin taron suka ce: “Ku juyo daga waɗannan al’amura marasa-amfani zuwa Allah mai-rai.” (Ayukan Manzanni 14:8-15) Waye ne “Allah mai-rai,” wanda ya halicci dukan abu?— Hakika, Jehovah ne “Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Yesu ya kira Jehovah “Allah makaɗaici mai-gaskiya.” Saboda haka, waye ya cancanci a bauta masa?— Jehovah ne kawai!—Zabura 83:18; Yohanna 17:3; Ru’ya ta Yohanna 4:11.

Me ya sa Bulus da Barnaba ba su ƙyale mutane su bauta musu ba?

Mutane da yawa suna bauta wa wasu alloli ban da “Allah makaɗaici mai-gaskiya.” Sau da yawa suna bauta wa abubuwa da suka yi da itace, dutse, ko kuma ƙarfe. (Fitowa 32:4-7; Leviticus 26:1; Ishaya 44:14-17) Har mutane ma da suka shahara wani lokaci ana kiransu alloli, taurari, ko kuma gumaka. Daidai ne mu ba su ɗaukaka?—

Bayan Bulus ya zama manzo, ya rubuta: “Allah na wannan zamani ya makantarda hankulan marasa-bada gaskiya.” (2 Korinthiyawa 4:4) Wanene wannan allah?— Hakika, Shaiɗan Iblis ne! Shaiɗan ya sa mutane suna bauta wa mutane da kuma abubuwa da yawa.

Sa’ad da Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya sa Yesu ya yi masa sujjada, menene Yesu ya gaya wa Shaiɗan?— “Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Matta 4:10.) Yesu ya bayyana sarai cewa bauta ta Jehovah ce. Bari mu karanta game da wasu samari da suka san da haka. Sunayensu Shadrach, Meshach, da Abednego.

Waɗannan samari Yahudawa, ɓangare ne na al’ummar Allah Isra’ila kuma an kama su kamammun yaƙi zuwa ƙasar Babila. A can wani sarki mai suna Nebuchadnezzar ya gina wani babban gunki na zinariya. Wata rana ya ba da doka cewa idan aka yi kiɗa, kowa ya yi sujjada ga gunkin. ‘Dukan wanda bai yi sujjada ba, za a jefa shi cikin tanderu mai wuta,’ ya ƙone. Da me za ka yi?—

Me ya sa waɗannan mutane ba su bauta wa gunki ba?

Shadrach, Meshach, da Abednego suna yin dukan abin da sarkin ya umurta. Amma sun ƙi su yi wannan. Ka san abin da ya sa?— Domin dokar Allah ta ce: ‘Kada ka yi wani allah a bayana. Kada ka yi wa kanka gunki don ka bauta masa.’ (Fitowa 20:3-5) Saboda haka, Shadrach, Meshach, da Abednego suka bi dokar Jehovah maimakon umurnin sarki.

Sarkin ya yi fushi, babu ɓata lokaci ya sa aka kawo masa samari Yahudawan nan uku. Ya yi tambaya: ‘Gaskiya ne cewa ba ku a bauta wa allolina? Zan sake ba ku zarafi. Idan kuka ji kiɗa, ku durƙusa ku bauta wa gunkin da na yi. Idan ba ku yi ba, za a jefa ku cikin tanderu mai ƙuna. Kuma wanene wannan Allahn da zai cece ku daga hannuna?’

To, menene waɗannan samarin za su yi yanzu? Da menene za ka yi?— Suka ce wa sarkin: ‘Allahnmu wanda muke bauta wa zai iya ya cece mu. Amma ko idan bai cece mu ba, allolinka ba waɗanda za mu bauta wa ba ne. Ba za mu bauta wa gunkinka na zinariya ba.’

Sarkin ya fusata. Ya ba da umurni: ‘Ku ƙara wuta ya fi dā zafi sau bakwai!’ Sai ya umurci dakarunsa su ɗaure Shadrach, Meshach, da Abednego su jefa su cikin tanderun! Tanderun ya yi zafi sosai da dakarun sarkin suka mutu domin wutar! To Yahudawa ukun kuma fa?

Shadrach, Meshach, da Abednego suka faɗa tsakiyar wutar. Amma suka tashi suka tsaya! Ba su ƙone ba. Kuma ba a ɗaure suke ba. Ta yaya wannan zai yiwu?— Sarkin ya leƙa cikin tanderun, abin da ya gani ya tsorata shi. ‘Ba mutane uku muka jefa cikin wuta ba?’ ya yi tambaya. Bayinsa suka amsa: “Hakika, ya sarki.”

Ta yaya Jehovah ya ceci bayinsa daga tanderu mai wuta?

Sai sarkin ya ce: ‘Duba! Ina ganin mutane huɗu suna tafiya a ciki, kuma wutar ba ta ƙone su ba.’ Ka san ko wanene mutum na huɗun?— Mala’ikan Allah ne. Ya kāre Yahudawa ukun daga ƙuna.

Da ya ga wannan, sarkin ya zo ƙofar tanderun ya yi kira: “Shadrach, da Meshach, da Abednego, ku bayin Allah maɗaukaki, ku fito, ku zo nan.” Da suka fito, kowa ya ga cewa ba su ƙone ba. Ba sa ma warin hayaƙi. Sai sarkin ya ce: ‘Mai albarka ne Allah na Shedrach, da na Meshach, da Abednego, wanda ya aiko mala’ikansa, ya ceci bayinsa domin ba za su bauta wa wani allah ba sai Allahnsu.’—Daniel, sura 3.

Waɗanne gumaka mutane suke bauta wa a yau?

Za mu koyi darasi daga abin da ya faru a lokacin. Har wa yau mutane suna kafa gumaka domin bauta. The Encyclopedia Americana ya ce: “Tuta, kamar gicciya, tana da tsarki.” Za a iya yin gunki da itace, dutse, ƙarfe, ko yadi. Almajiran Yesu na farko ba su bauta wa daular Romawa ba, da wanda ɗan tarihi Daniel P. Mannix ya ce ya yi daidai da “ƙin ya sara wa tuta ko kuma rantsuwa.”

Kana tsammanin da wani bambanci ne a wurin Allah idan gunkin addini an yi shi da yadi, ko da itace, ko da dutse, ko kuma da ƙarfe?— Zai dace bawan Jehovah ya yi sujjada ga wannan gunkin?— Shadrach, Meshach, da Abednego ba su yi haka ba, kuma Jehovah ya yi farin ciki da su. Ta yaya za ka bi misalinsu?—

Waɗanda suke bauta wa Jehovah ba za su bauta wa wani mutum ba ko kuma wani abu. Ka karanta abin da aka ce a Joshua 24:14, 15, 19-22; Ishaya 42:8; 1 Yohanna 5:21; da kuma Ru’ya ta Yohanna 19:10.