Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 31

Inda Za Ka Sami Ta’aziyya

Inda Za Ka Sami Ta’aziyya

KA TAƁA kaɗaita kuma kana baƙin ciki?— Ka taɓa yin mamaki ko akwai wanda yake ƙaunarka?— Wasu yara suna jin haka. Amma Allah ya yi alkawari: ‘Ni ba ni manta da kai ba.’ (Ishaya 49:15) Wannan ba abin farin ciki ba ne a yi tunani a kansa?— Hakika, Jehovah Allah yana ƙaunarmu da gaske!

Yaya kake tsammanin wannan ɗan rago da ya ɓata yake ji?

Wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama ubana da uwata sun yashe ni. Amma Ubangiji za ya ɗauke ni.” (Zabura 27:10) Sanin wannan zai iya kasancewa ta’aziyya a gare mu, ko ba haka ba ne?— Jehovah ya gaya mana: ‘Kada ku ji tsoro; gama ina tare da ku . . . na taimake ku.’Ishaya 41:10.

Amma fa wani lokaci Jehovah yana ƙyale Shaiɗan ya ba mu wahala. Jehovah yana ƙyale Shaiɗan ya gwada bayinsa. Iblis ya taɓa wahalar da Yesu ƙwarai har Yesu ya yi wa Jehovah kuka: ‘Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?’ (Matta 27:46) Ko da yake Yesu yana wahala ya sani cewa Jehovah yana ƙaunarsa. (Yohanna 10:17) Amma Yesu ya sani cewa Allah yana ƙyale Shaiɗan ya gwada bayinsa kuma yana ƙyale Shaiɗan ya sa su wahala. A wani babi za mu ba da bayanin abin da ya sa Allah yake ƙyale Shaiɗan ya yi haka.

Sa’ad da muke ƙanana, bai da wuya mu ji tsoro. Alal misali, ka taɓa ɓata hanya?— Ka tsorata?— Yara da yawa za su tsorata. Babban Malami ya taɓa ba da labari game da wani da ya ɓata. Amma ba yaro ba ne ya ɓata. Ɗan rago ne ya ɓata.

A wasu hanyoyi, kana kama da ɗan rago. Me ya sa za a faɗi haka? Abin da ya sa shi ne, ’yan tumaki ba su da girma kuma ba su da ƙarfi. Saboda haka, suna bukatar wani ya kula da su kuma ya kāre su. Mutumin da yake kiwon tumaki ana kiransa makiyayi.

A cikin labarin Yesu ya faɗi game da makiyayi da yake da tumaki ɗari. Amma sai ɗaya ya ɓata. Wataƙila yana so ya ga abin da yake wancan gefe na tudu. Bai daɗe ba, ɗan ragon ya yi nisa da sauran. Za ka iya tunanin yadda ya ji sa’ad da ya duba ya ga shi kaɗai ne?—

Menene makiyayin zai yi sa’ad da ya ga cewa rago ɗaya ya ɓata? Zai ce ne ai wannan laifin ragon ne, saboda haka, ba zai damu ba? Ko kuma zai bar tumaki 99 ɗin ne ya je neman ɗayan? Ya dace ne ya wahala haka a kan rago ɗaya?— Idan kai ne wannan ragon da ya ɓata, za ka so makiyayin ya neme ka?—

Wanene ya yi kama da makiyayin da ya ceci ragonsa?

Makiyayin yana ƙaunar tumakinsa ƙwarai, har da wanda ya ɓata ma. Saboda haka, ya je neman wanda ya ɓata. Ka yi tunanin yadda ragon da ya ɓata zai yi farin ciki sa’ad da ya ga makiyayin yana zuwa! Kuma Yesu ya ce makiyayin ya yi farin ciki domin ya sami ragon da ya ɓata. Ya yi farin ciki a kansa fiye da tumaki 99 da ba su ɓata ba. To, waye ne ya yi daidai da wannan makiyayi na labarin da Yesu ya bayar? Waye ne yake kula da mu sosai kamar yadda wannan makiyayin yake kula da tumakinsa?— Yesu ya ce Ubansa a samaniya yana yin haka. Kuma Ubansa Jehovah ne.

Jehovah Allah shi ne Babban Makiyayi na mutanensa. Yana ƙaunar dukan waɗanda suke bauta masa, har da yara ƙanana kamar ka. Ba ya son kowannenmu ya raunana ko kuma ya halaka. Babu shakka ta’aziyya ce mu sani cewa Allah yana ƙaunarmu sosai haka!—Matta 18:12-14.

Jehovah ya kasance da gaske a gare ka kamar yadda babanka ko kuma wasu mutane suke a gare ka?

Ka gaskata da Jehovah Allah da gaske?— Wani ne ainihi a gare ka?— Gaskiya ne cewa ba za mu iya ganin Jehovah ba. Domin shi ruhu ne. Yana da jiki da idanunmu ba sa iya gani ba. Amma shi wani ne ainihi, kuma yana iya ganinmu. Ya san lokacin da muke bukatar taimako. Kuma za mu iya yi masa magana cikin addu’a, kamar yadda muke yi wa mutane magana a nan duniyar. Jehovah yana so mu yi haka.

Saboda haka, idan ka kaɗaita ko kuma kana baƙin ciki, me ya kamata ka yi?— Ka yi wa Jehovah magana. Ka matsa kusa da shi kuma zai yi maka ta’aziyya ya taimake ka kuma. Ka tuna cewa Jehovah yana ƙaunarka, idan ma kana jin kowa ya ƙi ka. Bari mu ɗauki Littafi Mai Tsarki namu. A Zabura sura 23 an gaya mana, daga aya ta 1: “Ubangiji makiyayina ne; ba zan rasa kome ba. Yana sanya ni in kwanta a cikin makiyaya mai-ɗanya: yana bishe ni a gefen ruwaye na hutawa.”

Ka lura da abin da marubucin ya daɗa a aya ta 4: “Hakika, ko tafiya ni ke yi ta tsakiyar ƙwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron kowace masifa ba, gama kana tare da ni: Sandarka da kerenka suna yi mini ta’aziyya.” Haka mutane suke ji idan Jehovah ne Allahnsu. Suna samun ta’aziyya yayin da suke cikin damuwa. Haka kake ji?—

Kamar yadda makiyayi mai ƙauna yake kula da garkensa, haka Jehovah yake kula da mutanensa da kyau. Yana nuna musu hanya mai kyau da za su bi, kuma suna bi da farin ciki. Ko da masifa ta kewaye su, ba sa bukatar su tsorata. Makiyayi yana amfani da sandarsa ko kuma kerensa ya kāre tumakinsa daga dabbobin da za su yi musu ɓarna. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da yadda saurayi makiyayi Dauda ya kāre tumakinsa daga zaki da kuma karen daji. (1 Samu’ila 17:34-36) Mutanen Allah ma sun sani cewa Jehovah zai kāre su. Suna iya samun kwanciyar hankali domin sun sani Allah yana tare da su.

Kamar makiyayi da yake kāre tumakinsa, waye zai taimake mu sa’ad da muke cikin wahala?

Jehovah yana ƙaunar tumakinsa ƙwarai, kuma yana kula da su da kyau. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa.’—Ishaya 40:11.

Bai sa ka farin ciki ba ka sani cewa Jehovah haka yake?— Ba ka so ka zama ɗaya cikin tumakinsa?— Tumaki suna saurarar muryar makiyayinsu. Suna kasancewa kusa da shi. Kana saurarawa ga Jehovah?— Kana kasancewa kusa da shi?— To, ba ka bukatar jin tsoro. Jehovah zai kasance tare da kai.

Jehovah yana kula cikin ƙauna da waɗanda suke bauta masa. Bari mu karanta tare abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da wannan, a Zabura 37:25 (36:25, “Dy”); 55:22 (54:23, “Dy”); da kuma Luka 12:29-31.