Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 33

Yesu Zai Iya Kāre Mu

Yesu Zai Iya Kāre Mu

Yaya kake ɗaukan Yesu—kamar sarki mai iko ko kuma kamar jariri?

SA’AD da Yesu ya yi girma kuma ya san yadda aka kāre shi sa’ad da yake ƙarami, kana tsammanin ya yi addu’a ga Jehovah ya yi masa godiya?— Menene kake tsammanin Yesu ya gaya wa Yusufu da Maryamu sa’ad da ya san cewa sun kāre ransa ta wajen tafiya da shi ƙasar Masar?—

Hakika, Yesu ba jariri ba ne yanzu. Ba ya ma duniya kamar yadda ya taɓa zama. Amma ka lura cewa wasu mutane kamar suna tunanin Yesu jariri ne a sakarkari?— Haka yake a lokacin Kirsimati, a wurare dabam dabam ana ganin hotunan Yesu yana jariri.

Ko da yake Yesu ba ya duniya yanzu, ka yarda yana da rai?— Hakika, an ta da shi daga matattu, kuma yanzu shi Sarki ne mai iko a sama. Me kake tsammani zai yi domin ya kāre waɗanda suke masa hidima?— Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna yadda zai kāre waɗanda suke ƙaunar shi. Bari mu ga yadda ya yi haka wata rana da yake cikin kwalekwale da almajiransa.

Da yamma ne. Yesu ya yi ta koyarwa a bakin Tekun Galili, wanda yake da tsawon mil 13 da faɗin mil bakwai da rabi. Ya ce wa almajiransa: “Mu tafi wancan ƙetaren teku.” Sai suka fara tafiya su ƙetare tekun. Yesu ya gaji tilis, sai ya je bayan kwalekwale ya kwanta a kan matashin kai. Ba da daɗewa ba ya fara share barci.

Menene Yesu yake gaya wa iska da taguwar ruwa?

Almajiransa suka kasance a faɗake su ci gaba da tuka jirgin. Kome ya tafi daidai na ɗan lokaci, amma sai iska mai ƙarfi ta fara busawa. Ta yi ta busawa da ƙarfi sosai, taguwar kuma ta yi girma. Taguwar ta fara shiga cikin jirgin, jirgin kuma ya fara cika da ruwa.

Almajiran suka tsorata domin za su nitse. Amma Yesu bai ji tsoro ba. Yana barci a bayan jirgin. A ƙarshe, almajiran suka tashe shi, suka ce: ‘Malam, Malam, ka cece mu; za mu mutu a wannan hadarin.’ Sai Yesu ya tashi ya yi wa iskar da taguwar magana. “Ka natsu, yi shiru”! in ji shi.

A take iska ta daina busawa, kuma kogin ya yi shuru. Almajiran suka yi mamaki. Ba su taɓa ganin irin wannan ba a dā. Suka fara ce wa juna: “Wannan fa wanene, har da iska da ruwa yana umurninsu, suna kuwa ji?”—Luka 8:22-25; Markus 4:35-41.

Ka san ko wanene Yesu?— Ka san inda ya sami ikonsa mai yawa?— Bai kamata almajiran su ji tsoro ba sa’ad da Yesu yana tare da su, domin Yesu ba mutum ba ne kawai. Zai iya yin abubuwa masu ban mamaki da babu mutumin da zai iya yi. Bari in gaya maka kuma abin da ya taɓa yi a teku mai hadari.

Daga baya ne, wata rana. Sa’ad da yamma ta yi, Yesu ya gaya wa almajiransa su shiga jirgin ruwa su tafi wajen ƙetaren teku zai bi su. Sai Yesu ya tafi shi kaɗai cikin duwatsu. Wajen babu kowa, inda zai iya yi wa Ubansa, Jehovah Allah, addu’a.

Almajiran suka shiga cikin jirgi suka fara tafiya zuwa ƙetaren tekun. Ba da daɗewa ba iska ta fara busawa. Ta yi ta busawa da ƙarfi. Ga dare ya yi. Sai mutanen suka kwance zanen jirgin suka fara tuƙawa da filafilai. Amma ba sa sauri domin iskar mai ƙarfi tana busa su. Jirgin yana gaba yana baya a tsakiyar taguwar ruwan, kuma ruwa yana shiga cikin jirgin. Mutanen suka yi ƙoƙarin su isa bakin tekun amma sun kasa.

Yesu har yanzu shi kaɗai ne a cikin dutsen. Ya daɗe a wurin. Amma yanzu ya ga cewa almajiransa suna cikin haɗari a taguwa. Saboda haka, ya bar cikin dutsen ya je bakin tekun. Yesu yana so ya taimaki almajiransa, saboda haka ya fara tafiya zuwa wurinsu a kan tekun mai hadari!

Menene zai faru idan ka yi ƙoƙarin ka yi tafiya a kan ruwa?— Za ka nitse, ƙila ka sha ruwa. Amma Yesu dabam yake. Shi yana da iko na musamman. Yesu ya yi tafiya mai nisa domin ya isa wurin jirgin. Asuba ta yi kusa da almajiran suka ga Yesu yana zuwa wurinsu a kan ruwa. Ba su yarda da abin da suka gani ba. Sun tsorata sosai, suka yi kuka. Sai Yesu ya yi musu magana: “Hankalinku shi kwanta; ni ne; kada ku ji tsoro.”

Me ya sa Yesu ya yi abin ban al’ajabi?

Da Yesu ya shiga cikin jirgin sai aka daina iska. Almajiran suka ƙara mamaki. Suka faɗi gaban Yesu suka ce: “Hakika kai Ɗan Allah ne.”—Matta 14:22-33; Yohanna 6:16-21.

Da kana nan a lokacin da Yesu yake yin irin waɗannan abubuwa da ba za ka ji daɗi ba?— Ka san abin da ya sa Yesu ya yi waɗannan abubuwan ban al’ajabi?— Ya yi su ne domin yana ƙaunar almajiransa kuma yana so ya taimake su. Amma kuma ya yi waɗannan abubuwa domin ya nuna iko mai yawa da yake da shi da zai yi amfani da shi a nan gaba sa’ad da ya zama Sarkin Mulkin Allah.

Ta yaya Yesu yake kāre bayinsa a yau?

Har a yau Yesu sau da yawa yana amfani da ikonsa ya kāre mabiyansa daga ƙoƙarin da Shaiɗan yake yi ya hana su gaya wa wasu game da Mulkin Allah. Amma Yesu ba ya amfani da ikonsa ya kāre almajiransa daga yin rashin lafiya ko kuma ya warkar da su sa’ad da ba su da lafiya. Dukan manzannin Yesu ma sun mutu daga baya. An kashe Yaƙub ɗan’uwan Yohanna, Yohanna kuma aka saka shi a kurkuku.—Ayukan Manzanni 12:2; Ru’ya ta Yohanna 1:9.

Haka yake a yau. Ko mutane suna bauta wa Jehovah ko ba sa bauta masa, suna yin rashin lafiya kuma su mutu. Amma ba da daɗewa ba, a lokacin sarautar Yesu Sarkin gwamnatin Allah, abubuwa za su canja. Babu wanda a lokacin zai ji tsoro domin Yesu zai yi amfani da ikonsa ya albarkaci dukan waɗanda suka yi masa biyayya.—Ishaya 9:6, 7.

Wasu ayoyi da suka nuna iko mai yawa na Yesu cewa shi ne wanda Allah ya naɗa Sarki a Mulkin Allah su ne Daniel 7:13, 14; Matta 28:18; da kuma Afisawa 1:20-22.