Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 41

Yara da Suka Faranta wa Allah Rai

Yara da Suka Faranta wa Allah Rai

WANE yaro ne a duniya kake tsammani ya faranta wa Jehovah rai ƙwarai da gaske?— Ɗansa ne Yesu. Bari mu yi magana a kan abubuwa da Yesu ya yi da ya faranta wa Ubansa rai.

Iyalin Yesu suna da zama a wurin da yake da nisan tafiyar kwana uku daga Urushalima, inda haikali mai kyau na Jehovah yake. Yesu ya kira haikalin “gidan Ubana.” Shi da iyalinsa suna zuwa can kowacce shekara su halarci bikin Ƙetarewa.

Wata shekara, sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, iyalinsa suka fara komawa gida bayan an ƙare bikin Ƙetarewar. Har sai da suka tsaya daddare suka gano cewa Yesu ba ya tsakanin danginsu da abokanansu. Nan da nan Maryamu da Yusufu suka koma Urushalima su nemi Yesu. A ina kake tsammanin yake?—

Sun sami Yesu a cikin haikali. Yana sauraran malamai, kuma yana yin tambayoyi. Kuma idan suka yi masa tambaya, sai ya ba su amsa. Sun yi mamakin amsoshi da ya bayar. Ka ga abin da ya sa Allah ya yi farin ciki da Ɗansa?—

Hakika, sa’ad da Yusufu da Maryamu suka sami Yesu daga baya sun yi farin ciki. Amma Yesu bai damu ba. Ya sani cewa haikalin wuri ne mai kyau. Saboda haka, ya yi tambaya: “Ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin [gidan] Ubana?” Ya sani cewa haikali gidan Allah ne, kuma yana so ya kasance a can.

Daga baya, Maryamu da Yusufu suka koma da Yesu zuwa Nazarat. Wane hali kake tsammanin Yesu ya nuna wa iyayensa?— Littafi Mai Tsarki ya ce yana “biyayya da su.” Me kake tsammanin wannan yake nufi?— Yana nufin cewa yana yin abin da suka ce. Hakika, ya yi abin da iyayensa suka ce ya yi, kamarsu jawo ruwa daga rijiya.—Luka 2:41-52.

Ta yaya Yesu ya faranta wa Allah rai sa’ad da yake yaro?

Saboda haka, ka yi tunani game da wannan: Ko da yake Yesu kamili ne, ya yi wa iyayensa ajizai biyayya. Wannan ya faranta wa Allah rai kuwa?— Hakika ya faranta masa rai, domin Kalmar Allah ta gaya wa yara: ‘Ku yi biyayya da iyayenku.’ (Afisawa 6:1) Kai ma za ka faranta wa Allah rai idan ka yi wa iyayenka biyayya kamar yadda Yesu ya yi.

Wata hanya kuma da za ka faranta wa Allah rai ita ce gaya wa wasu mutane game da shi. Amma wasu mutane za su ce maka wannan ba aikin yara ƙanana ba ne. Sa’ad da mutane suka yi ƙoƙari su hana yara daga yin haka, Yesu ya ce: “Ba ku taɓa karantawa ba, Daga cikin bakin jarirai da masu-shan mama ka cika yabo?” (Matta 21:16) Saboda haka, dukanmu za mu iya gaya wa wasu game da Jehovah da kuma game da yadda yake da kirki, idan muna so. Kuma idan muka yi haka za mu faranta wa Allah rai.

Daga ina muke koyon abubuwa game da Allah da za mu iya gaya wa wasu game da shi?— Daga nazarinmu na Littafi Mai Tsarki a gida. Amma muna koyo kuma daga wurin da mutanen Allah suke taruwa su yi nazari. Ta yaya za mu iya sanin ko su waye waɗannan?—

Menene mutanen suke yi a wurin taronsu? Suna koyar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne da gaske? Suna karatunsa ne kuma su tattauna shi? Ta haka ne muke koyo game da Allah, ko ba haka ba?— A taron Kiristoci kuma za mu yi tsammanin mu ji abin da Allah ya ce, ko ba haka ba?— Amma me zai faru idan mutane suka ce ba dole ba ne ka yi rayuwa irin wadda Littafi Mai Tsarki ya ce? Za ka ce su mutanen Allah ne?—

Ga wani abu kuma da ya kamata mu yi tunani a kai. Littafi Mai Tsarki ya ce mutanen Allah za su kasance mutane ne “domin sunansa.” (Ayukan Manzanni 15:14) Tun da sunan Allah Jehovah ne, za mu iya tambayar mutane ko Jehovah ne Allahnsu. Idan suka ce a’a, to mun san cewa su ba mutanensa ba ne. Mutanen Allah kuma za su riƙa gaya wa wasu mutane game da Mulkin Allah. Kuma za su nuna ƙaunarsu ga Allah ta wajen kiyaye dokokinsa.—1 Yohanna 5:3.

Idan ka san mutanen da suke yin dukan waɗannan abubuwa, ya kamata ka haɗu da su domin bauta. Ya kamata ka mai da hankali ka saurara da kyau a waɗannan taron sai kuma ka amsa tambayoyi sa’ad da aka yi su. Abin da Yesu ya yi ke nan sa’ad da yake gidan Allah. Kuma idan ka yi waɗannan abubuwa, za ka faranta wa Allah rai, kamar yadda Yesu ya yi.

Za ka iya tuna wasu yara da aka yi maganarsu a cikin Littafi Mai Tsarki da suka faranta wa Allah rai?— Timothawus misali ne mai kyau. Babansa bai yi imani da Jehovah ba. Amma mamarsa Afiniki da kakarsa Lois sun ba da gaskiya ga Jehovah. Timothawus ya saurare su ya koyi game da Jehovah.

Ko da yake babansa ba mai bi ba ne, me ya sa Timothawus yake so ya bauta wa Allah?

Sa’ad da Timothawus ya yi girma manzo Bulus ya ziyarci garin da yake da zama. Ya lura da yadda Timothawus yake so ya bauta wa Jehovah. Saboda haka, ya gayyaci Timothawus ya bi shi ya bauta wa Allah sosai. Dukan inda suka je, suna gaya wa mutane game da Mulkin Allah da kuma game da Yesu.—Ayukan Manzanni 16:1-5; 2 Timothawus 1:5; 3:14, 15.

Amma misalan yara maza ne kawai suke cikin Littafi Mai Tsarki na waɗanda suka faranta wa Allah rai?— A’a. Ka yi la’akari da yarinya ƙarama Ba’isra’iliya da ta faranta wa Allah rai. Sa’ad da take raye, al’ummar Suriya da al’ummar Isra’ila abokanan gaba ne. Wata rana Suriyawan suka yi yaƙi da Isra’ila suka kama yarinyar. Suka kai ta gidan babban soja da ake kira Na’aman. A nan ta zama baiwar matar Na’aman.

Na’aman yana da cuta da ake kira kuturta. Babu likita da ya iya yi masa magani. Amma yarinya ƙaramar daga Isra’ila ta yi imani cewa bawan Allah na musamman zai taimaki Na’aman. Hakika, Na’aman da matarsa ba sa bauta wa Jehovah. Ya kamata ne yarinyar ta gaya musu abin da ta sani? Da kai ne me za ka yi?—

Ta yaya yarinya Ba’isra’iliya ta faranta wa Allah rai?

Ƙaramar yarinyar ta ce: ‘Idan Na’aman zai je wurin annabin Jehovah a Isra’ila, za a warkar da Na’aman daga kuturtarsa.’ Na’aman ya saurari yarinyar ya tafi wurin annabin. Sa’ad da ya yi abin da annabin ya ce masa ya yi, ya warke. Wannan ya sa Na’aman ya zama mai bauta wa Allah na gaskiya.—2 Sarakuna 5:1-15.

Za ka so ka taimaki wani ya koyi game da Jehovah da kuma abubuwa da zai yi, kamar yadda wannan ƙaramar yarinyar ta yi?— Waye kake tsammanin za ka iya taimakonsa?— Hakika, da farko ba za su yarda ba cewa suna bukatar taimako. Amma za ka iya gaya musu game da abubuwa masu kyau da Jehovah yake yi. Kuma za su saurare ka. Kuma ka tabbata cewa wannan zai faranta wa Allah rai.

Za a samu ƙarin ƙarfafawa ga yara su yi farin ciki wajen bauta wa Allah cikin Zabura 122:1 (121:1, “Dy”); 148:12, 13; Mai-Wa’azi 12:1; 1 Timothawus 4:12; da kuma Ibraniyawa 10:23-25.