Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA ƊAYA

Mece ce Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?

Mece ce Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah?
  • Allah ya damu da kai kuwa da gaske?

  • Yaya kamanin Allah? Yana da suna kuwa?

  • Shin yana yiwuwa a kusaci Allah kuwa?

1, 2. Me ya sa yake da kyau a yi tambayoyi?

KA TAƁA lura da yadda yara suke yin tambaya? Da yawa suna fara tambaya da zarar sun fara magana. Da idanunsu a buɗe su dube ka su yi tambaya kamar su: Me ya sa gajimare yake shuɗi? Da me aka yi taurari? Wa ya koya wa tsuntsaye kuka? Za ka yi ƙoƙari ƙwarai ka ba da amsa, amma ina, yana da wuya. Kyakkyawar amsa da za ka bayar, za ta sa su sake tambaya: Me ya sa?

2 Ba yara ba ne kawai suke yin tambayoyi. Sa’ad da muke girma, muna ci gaba da tambayoyi. Muna yin haka ne domin muna neman tafarkinmu, domin muna so mu fahimci haɗari da za mu guje wa, ko kuma domin mu gamsar da ƙwaƙwarmu. Amma mutane da yawa suna daina yin tambayoyi, musamman ma mafiya muhimmanci. Ko kuma su daina neman amsoshi.

3. Me ya sa mutane da yawa suke daina ƙoƙarin neman amsoshin tambayoyi da suka fi muhimmanci?

3 Ka yi tunanin tambaya da take bangon wannan littafin, da waɗanda suke shafin gabatarwa, ko kuwa waɗanda aka yi a farkon wannan babin. Waɗannan sune tambayoyi mafiya muhimmanci da za ka yi. Duk da haka, mutane da yawa sun ba da gari wajen neman amsoshin tambayoyin. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki zai iya ba da amsoshin kuwa? Wasu suna jin cewa za su yi wuyar fahimta. Wasu kuma sun damu cewa yin tambayoyi zai kai ga jin kunya. Wasu kuma sun ce irin waɗannan tambayoyi ya kamata a ƙyale su ga malaman addini da shugabanninsu. To me kake tsammani?

4, 5. Waɗanne tambayoyi ne suke da muhimmanci ƙwarai a rayuwa da za mu iya yi, me ya sa za mu nemi amsa?

4 Wataƙila, kana so ka sami amsoshi ga muhimman matsaloli na rayuwa? Babu shakka wani lokaci kana mamaki: ‘Menene manufar rayuwa? Wannan shi ne muhimmancin rayuwa? Yaya ainihi kamanin Allah?’ Yana da muhimmanci mu yi irin waɗannan tambayoyin, yana kuma da muhimmanci ka ci gaba da neman amsa har sai ka sami amsa ta gaskiya mai tabbaci. Babban malami Yesu Kristi ya ce: “Ku roƙa, za a ba ku; ku nema, za ku samu; ku ƙwanƙwasa, za a buɗe muku.”—Matta 7:7.

5 Idan ka ‘yi ta neman’ amsoshi ga waɗannan tambayoyi masu muhimmanci, za ka sami alheri. (Misalai 2:1-5) Ko menene mutane suka gaya maka, ana samun amsoshi, kuma kana iya samunsu—a cikin Littafi Mai Tsarki. Amsoshin ba su da wuyar fahimta. Mafi muhimmanci ma, suna ba da bege da farin ciki. Kuma za su iya taimakonka ka yi rayuwa mai gamsarwa a yanzu. Da farko, bari mu bincika tambaya da ta dami mutane da yawa.

SHIN ALLAH MARAR ƘAUNA NE MAI TAURIN ZUCIYA?

6. Me ya sa mutane da yawa suke tunanin cewa Allah bai damu da matsalolin mutane ba?

6 Mutane da yawa suna tsammanin amsar wannan tambayar e ce. Suna tunani ‘Idan Allah yana ƙaunar duniya, ba za ta kasance kyakkyawar wuri ba?’ Duniya wuri ce da take cike da yaƙe-yaƙe, ƙiyayya, da wasu matsaloli. Kuma dukanmu, muna yin rashin lafiya, muna wahala, muna rashin waɗanda muke ƙauna. Saboda haka, mutane da yawa sukan ce, ‘Idan Allah yana ƙaunarmu kuma ya damu da matsalolinmu, da ba zai hana waɗannan abubuwa faruwa ba?’

7. (a) Ta yaya malaman addini suka sa mutane da yawa suka yi tunanin cewa Allah mai taurin zuciya ne? (b) Menene ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da jarabta da muke fuskanta a yau?

7 Fiye ma da haka, malaman addini a wasu lokatai suna sa mutane su yi tunanin cewa Allah mai taurin zuciya ne. Ta yaya? Sa’ad da masifa ta faɗo, sai su ce nufin Allah ne. Wato, irin waɗannan malamai suna ɗora wa Allah alhakin munanan abubuwa da suke faruwa. Amma hakan gaskiya ne game da Allah? Menene ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa? Yaƙub 1:13 ta ba da amsa: “Kada kowa sa’anda ya jarabtu ya ce, Daga wurin Allah ne na jarabtu: gama Allah ba shi jarabtuwa da mugunta, shi kuwa da kansa ba shi jarabci kowa ba.” Saboda haka ba Allah ba ne sababin mugunta da kake gani a duniya. (Ayuba 34:10-12) Hakika, yana ƙyale miyagun abubuwa su faru. Amma da bambanci tsakanin ƙyale abu da kuma haddasa shi.

8, 9. (a) Ta yaya za ka kwatanta bambanci da ke tsakanin ƙyale mugunta ta wanzu da kuma haddasa ta? (b) Me ya sa bai dace ba mu ɗora wa Allah alhaki domin ya ƙyale ’yan Adam su bi mugun tafarki?

8 Alal misali, ka yi tunanin mutum mai hikima mai ƙauna da yaronsa ya girma amma suna tare a gida ɗaya. Sa’ad da yaron ya yi tawaye, ya nemi ya bar gidan, babansa zai hana shi ne?. Idan yaron ya shiga muguwar rayuwa ya faɗa cikin masifa. Babansa ne ya jawo masa masifar? A’a. (Luka 15:11-13) Hakazalika, Allah bai hana mutane ba sa’ad da suka zaɓi muguwar rayuwa, amma ba shi ne sababin matsalarsu ba. Hakika, ba zai dace ba a ɗora wa Allah alhakin matsalolin ’yan Adam.

9 Allah yana da kyakkyawan dalili na ƙyale mutane su bi mugun tafarki. Tun da Mahalicci ne mai hikima mai iko, ba dole ba ne ya yi mana bayanin dalilinsa na yin haka. Amma Allah ya yi haka ne domin ƙauna. Za ka fahimci waɗannan dalilai a Babi na 11. Amma ka tabbata cewa ba Allah yake da alhakin matsaloli da muke fuskanta ba. Maimakon haka, ya yi mana alkawarin magance su!—Ishaya 33:2.

10. Me ya sa za mu gaskata cewa Allah zai gyara dukan matsalar mugunta?

10 Bugu da ƙari, Allah mai tsarki ne. (Ishaya 6:3) Wannan yana nufin cewa marar aibi ne mai tsabta. Babu ko ɗigon mugunta a gare shi. Saboda haka za mu iya dogara sosai a gare shi. Ba za mu iya dogara ga mutane ba haka, domin wani lokaci suna lalacewa. Mutum mai gaskiya da yake sarauta sau da yawa ba shi da ikon gyara abin da miyagun mutane suka yi. Amma Allah yana da iko marar iyaka. Zai iya gyarawa kuma zai gyara dukan yadda mugunta ta shafi ’yan adam. Sa’ad da Allah ya yi haka, zai yi hakan ne a hanyar da za ta kawo ƙarshen mugunta har abada!—Zabura 37:9-11.

YAYA ALLAH YAKE JI GAME DA RASHIN GASKIYA DA MUKE FUSKANTA?

11. (a) Yaya Allah yake ji game da rashin adalci? (b) Yaya Allah yake ji game da wahalarka?

11 Yaya Allah yake ji a yanzu game da abin da yake faruwa a duniya da kuma a rayuwarka? Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah “yana son shari’a.” (Zabura 37:28) Saboda haka ya damu ƙwarai game da abin da ke mai kyau da abin da ke mugu. Yana ƙin dukan rashin adalci. Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da mugunta ta cika duniya a dā “abin ya ɓata masa [Allah] zuciya kuma.” (Farawa 6:5, 6) Allah bai sāke ba. (Malachi 3:6) Har yanzu yana ƙin irin wahala da yake gani a dukan duniya. Kuma Allah ba ya son ganin mutane suna wahala. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yana kula da ku.”—1 Bitrus 5:7.

Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Jehobah shi ne Mahalicci mai ƙauna na sararin samaniya

12, 13. (a) Me ya sa muke da halayen kirki irin su ƙauna, kuma ta yaya ƙauna take shafan ra’ayinmu game da duniya? (b) Me ya sa za ka tabbata cewa Allah zai yi wani abu game da matsaloli na duniya?

12 Ta yaya za mu tabbata cewa Allah ba ya son ganin muna wahala? Ga ƙarin tabbaci. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah ya halicci mutum a kamaninsa. (Farawa 1:26) Muna da halayen kirki domin Allah yana da halayen kirki. Alal misali, kana damuwa idan ka ga mutane marasa laifi suna wahala? Idan ka damu da irin wannan rashin adalci, ka tabbata cewa abin ya ma fi damun Allah.

13 Wani abin da ke mai kyau game da mutane shi ne cewa suna iya nuna ƙauna. Wannan yana nuna koyi da Allah. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Muna ƙauna domin Allah mai ƙauna ne. Ƙauna za ta iya motsa ka ka kawo ƙarshen rashin adalci da kake gani a wannan duniyar? Idan kana da ikon ka yi haka, ba za ka yi ba ne? Hakika, za ka yi hakan! Ka tabbata cewa Allah zai kawo ƙarshen wahala da rashin adalci. Alkawura da aka ambata a gabatarwa ta wannan littafin ba mafarki ba ne ko kuma bege marar tushe. Alkawuran Allah hakika za su kasance gaskiya! Domin ka ba da gaskiya ga irin waɗannan alkawura, kana bukatar ka fahimci Allahn da ya yi su.

ALLAH YANA SO KA SAN KO WANENE SHI

Idan kana so mutum ya san ka, ba sunanka za ka gaya masa ba? Allah ya sanar da mu sunansa cikin Littafi Mai Tsarki

14. Menene sunan Allah, kuma me ya sa za mu yi amfani da shi?

14 Idan kana so mutum ya san ka, menene za ka yi? Ba za ka gaya wa mutumin sunanka ba? Shin Allah yana da suna kuwa? Addinai da yawa za su amsa cewa sunansa “Allah” ne ko kuma “Ubangiji,” amma waɗannan ba sunaye ba ne. Sunayen sarauta ne kamar yadda “sarki” da “shugaban ƙasa” suke sunayen sarauta. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah yana da sunayen sarauta masu yawa. “Allah” da “Ubangiji” suna cikin waɗannan. Amma kuma, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Allah yana da suna: Jehobah. Zabura 83:18 ta ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Idan fassarar Littafin Mai Tsarki naka bai ƙunshi wannan sunan ba, kana iya tuntuɓar Rataye a shafuffuka na 195-197 na wannan littafin domin ka fahimci abin da ya sa. Gaskiya ita ce, sunan Allah ya bayyana sau dubbai a cikin Littafi Mai tsarki na dā. Saboda haka, Jehobah yana son ka san sunansa kuma ka kira shi da shi. Ana iya cewa, ya yi amfani ne da Littafi Mai Tsarki wajen gabatar maka da kansa.

15. Menene sunan nan Jehobah yake nufi?

15 Allah ya bai wa kansa suna da yake cike da ma’ana. Sunansa, Jehobah, yana nufin cewa Allah zai iya cika dukan wani alkawari da ya yi kuma zai yi dukan wani nufi da ke cikin zuciyarsa. * Sunan Allah ba na biyunsa. Shi kaɗai yake da wannan suna. Jehobah ya bambanta a hanyoyi masu yawa. Ta yaya?

16, 17. Menene za mu koya daga waɗannan sunayen sarauta na Jehobah: (a) “Maɗaukaki? (b) “Sarkin zamanai”? (c) “Mahalicci”?

16 Mun gani a Zabura 83:18 cewa Jehobah: ‘Kai kaɗai ne Maɗaukaki.’ Hakika, Jehobah ne kaɗai ake cewa “Maɗaukaki.” Ru’ya ta Yohanna 15:3 ta ce: “Ayyukanka masu-girma ne, masu-ban al’ajabi, ya Ubangiji Allah, Mai-iko duka; halullukanka kuma masu-adalci ne, masu-gaskiya kuma, ya Sarkin zamanai.” Sunan sarautan nan “Maɗaukaki” ya koya mana cewa Jehobah shi ne ya fi kowa iko. A iko ba wanda ya yi daidai da shi; shi ne mafifici. Sunan sarauta ‘Sarkin zamanai’ ya nuna mana cewa Jehobah ya bambanta a wata hanya kuma. Shi kaɗai ya wanzu a dukan lokaci. Zabura 90:2 ta ce: “Tun fil’azal kai ne Allah har abada.” Wannan batu ne mai ban tsoro, ko ba haka ba?

17 Jehobah ya kuma bambanta domin shi kaɗai ne Mahalicci. Ru’ya ta Yohanna 4:11 ta ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” Duk abin da ka yi tunaninsa, daga halittun ruhu marasa ganuwa zuwa taurari da ke sararin samaniya zuwa ’ya’yan itatuwa zuwa kifaye da suke iyo cikin teku da koguna dukansu sun wanzu ne domin Jehobah ya halicce su!

ZA KA IYA KUSANTAR JEHOBAH KUWA?

18. Me ya sa wasu mutane suke jin cewa ba za su taɓa kusantar Allah ba, amma menene Littafi Mai Tsarki ya koyar?

18 Karatu game da halaye masu ban tsoro na Jehobah ya sa wasu sun ɗan razana. Suna jin cewa Allah ya fiye fifita, saboda haka suna ganin ba za su taɓa kusantarsa ba, domin ba zai ɗauke su wani abu ba. Amma wannan ra’ayin gaskiya ne? Littafi Mai Tsarki bai koyar da haka ba. Ya ce game da Jehobah: “Ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.” (Ayukan Manzanni 17:27) Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku kusato ga Allah, shi kuwa za ya kusato gareku.”—Yaƙub 4:8.

19. (a) Ta yaya za mu fara kusantar Allah, kuma ta yaya za mu amfana? (b) Wane hali ne na Allah ya fi burge ka?

19 Ta yaya za ka kusaci Allah? Da farko, ka ci gaba da abin da kake yi a yanzu, koya game da Allah. Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa sanin Jehobah da kuma Yesu zai kai ga “rai madawwami”! Kamar yadda ka sani, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:16) Jehobah har ila yana da kyakkyawan halaye masu daɗaɗawa. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” (Fitowa 34:6) “Nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa.” (Zabura 86:5) Allah mai haƙuri ne. (2 Bitrus 3:9) Shi mai aminci ne. (Ru’ya ta Yohanna 15:4) Sa’ad da ka ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki, za ka ga yadda Jehobah ya nuna cewa yana da dukan waɗannan halaye da kuma wasu masu ban sha’awa.

20-22. (a) Domin ba ma ganin Allah wannan zai hana mu ne mu kusace shi? Ka yi bayani. (b) Menene wasu mutane masu nufin kirki za su ce ka yi, amma me ya kamata ka yi?

20 Hakika, ba za ka iya ganin Allah ba domin shi ruhu ne marar ganuwa. (Yohanna 1:18; 4:24; 1 Timothawus 1:17) Ta wajen koyo game da shi daga Littafi Mai Tsarki, za ka san shi ƙwarai. Kamar yadda mai zabura ya ce za ka “dubi jamalin [Jehobah].” (Zabura 27:4; Romawa 1:20) Da zarar ka koyi game da Jehobah, haka nan za ka fahimce shi kuma haka za ka ƙara ƙaunarsa kuma ka kusace shi.

Ƙauna da uba yake da ita ga yaransa tana kwatanta ƙauna mai yawa da Ubanmu na samaniya yake da ita a gare mu

21 A hankali za ka fahimci abin da ya sa Littafi Mai Tsarki ya koyar da mu mu ɗauki Jehobah a madadin Ubanmu. (Matta 6:9) Ba domin shi ya ba mu rai ba kawai amma kuma domin yana so mu sami rayuwa tagari, kamar yadda uba mai ƙauna zai so ga yaransa. (Zabura 36:9) Littafi Mai Tsarki kuma ya koyar da mu cewa mutane za su iya zama abokanan Jehobah. (Yaƙub 2:23) Kana iya zama abokin Mahaliccin dukan sararin samaniya—abin mamaki!

22 Sa’ad da ka ci gaba da koyo daga Littafi Mai Tsarki, za ka ga cewa wasu mutane masu nufin kirki za su ce maka ka daina nazarin. Za su damu cewa za ka sake abin da ka gaskata. Amma kada ka bar kowa ya hana ka ƙulla wannan abota mafi kyau da za ka iya ƙullawa.

23, 24. (a) Me ya sa ya kamata ka ci gaba da tambayoyi game da abin da kake koya? (b) Menene za a yi bayani a babi na gaba?

23 Hakika, da akwai abubuwa da ba za ka fahimta ba da farko. Neman taimako zai bukaci laushin hali a gare ka, amma kada ka ƙi yin haka domin kunya. Yesu ya ce yana da muhimmanci mu ƙasƙantar da kai, kamar ɗan yaro. (Matta 18:2-4) Yara kuma kamar yadda muka sani, suna da yawan tambaye-tambaye. Allah yana son ka sami amsoshi. Littafi Mai Tsarki ya yabi wasu da suka yi ɗokin su koyi game da Allah. Sun yi bincike cikin Nassosi a tsanake domin su tabbata ko abin da suke koya gaskiya ne.—Ayukan Manzanni 17:11.

24 Hanya mafi muhimmanci na koyo game da Jehobah ita ce bincika Littafi Mai Tsarki. Ya bambanta da dukan wani littafi. A wace hanya? Babi na gaba zai yi bayani a kan wannan batun.

^ sakin layi na 15 Domin ƙarin bayani game da ma’ana da kuma yadda za a furta sunan Allah dubi rataye a shafuffuka na 195-197.