Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu

Halittun Ruhu—Yadda Suke Shafanmu
  • Shin mala’iku suna taimakon mutane ne?

  • Ta yaya miyagun ruhohi suka rinjayi mutane?

  • Muna bukatar mu ji tsoron miyagun ruhohi ne?

1. Me ya sa za mu so mu koyi game da mala’iku?

SANIN mutum ya ƙunshi sanin wani abu game da iyalinsa. Hakazalika, sanin Jehobah Allah ya ƙunshi sanin iyalinsa na mala’iku. Littafi Mai Tsarki ya kira mala’iku “ ’ya’yan Allah.” (Ayuba 38:7) To, menene matsayinsu a nufin Allah? Suna da wani matsayi a tarihin mutane kuwa? Shin mala’iku suna shafan rayuwarka kuwa? Idan haka ne, ta yaya?

2. Daga ina mala’iku suka fito, kuma su nawa ne?

2 Littafi Mai Tsarki ya yi maganar mala’iku sau ɗarurruwa. Bari mu bincika kaɗan daga cikin waɗannan domin mu ƙara fahimtar mala’iku. Daga ina mala’iku suka fito? Kolossiyawa 1:16 ta ce: “A cikinsa [Yesu Kristi] aka halitta dukan abu, cikin sammai da bisa duniya kuma.” Saboda haka, dukan halittu na ruhu da ake kira mala’iku, Jehobah Allah ne ya halicci kowannensu ta wajen Ɗan farinsa. Mala’ikun su nawa ne? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an halicci mala’iku miliyoyi barkatai, kuma dukansu suna da iko.—Zabura 103:20. *

3. Menene Ayuba 38:4-7 suka gaya mana game da mala’iku?

3 Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ta gaya mana cewa, sa’ad da aka kafa duniya, “dukan ’ya’yan Allah kuwa suka yi sowa don farinciki.” (Ayuba 38:4-7) Saboda haka mala’iku sun wanzu da daɗewa kafin ma a halicci mutum, kai kafin ma a halicci duniya. Wannan saƙo na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’iku suna da motsin zuciya, domin ya ce ‘suka yi sowa don farin ciki.’ Ka lura cewa ‘dukan ’ya’yan Allahu’ suka yi murna tare. A wannan lokacin dukan mala’iku suna cikin iyali guda mai haɗin kai mai bauta wa Jehobah Allah.

TAIMAKO DA KĀRIYA DAGA MALA’IKU

4. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mala’iku masu aminci suna da marmari a ayyukan mutane?

4 Tun da suka ga halittar mutane na fari, halittun ruhu masu aminci suna nuna ƙauna ga iyalin ’yan adam da take ƙaruwa da kuma cika nufin Allah. (Misalai 8:30, 31; 1 Bitrus 1:11, 12) Amma, da shigewar lokaci, mala’iku suka lura cewa yawancin ’yan adam sun juya daga bautar Mahaliccinsu mai ƙauna. Babu shakka cewa wannan ya sa mala’ikun masu aminci baƙin ciki. Amma kuma, sa’ad da mutum ya koma ga Jehobah, “akwai murna a wurin mala’ikun.” (Luka 15:10) Tun da mala’iku sun damu haka da mutane da suke bauta wa Allah, ba abin mamaki ba ne cewa Jehobah ya yi ta amfani da mala’ikun wajen ƙarfafa bayinsa masu aminci a duniya da kuma kāre su. (Ibraniyawa 1:7, 14) Ga wasu misalai.

“Allahna ya aiko mala’ikansa, ya rufe bakin zakuna.”—Daniel 6:22

5. Waɗanne misalai muke da su a Littafi Mai Tsarki na taimako daga mala’iku?

5 Mala’iku biyu suka taimaki mutumin nan mai aminci Lutu da ’ya’yansa mata biyu su tsira daga halakar mugayen biranan nan Saduma da Gwamrata ta wajen fitar da su daga wannan wuri. (Farawa 19:15, 16) Ƙarnuka bayan haka, aka jefa Daniel cikin kogon zakoki, amma ya kuɓuta daga bakinsu ya ce: “Allahna ya aiko mala’ikansa ya rufe bakin zakuna.” (Daniel 6:22) A ƙarni na farko A.Z., mala’ika ya cece manzo Bitrus daga kurkuku. (Ayukan Manzanni 12:6-11) Bugu da ƙari, mala’iku suka ƙarfafa Yesu a farkon hidimarsa a duniya. (Markus 1:13) Kuma sa’ad da Yesu yake dab da mutuwa, mala’ika ya bayyana masa kuma ya “ƙarfafa shi.” (Luka 22:43) Lalle wannan ya ƙarfafa Yesu a wannan lokaci mai muhimmanci a rayuwarsa!

6. (a) Ta yaya mala’iku suke ceton mutanen Allah a yau? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

6 A yau, mala’iku ba sa bayyana wa mutanen Allah a duniya. Ko da yake ba sa ganuwa ga idanun mutane, mala’ikun Allah har ila suna kāre mutanensa, musamman ma daga dukan wani abin da yake da haɗari a ruhaniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” (Zabura 34:7) Me ya sa waɗannan kalmomi ya kamata su zama abin ƙarfafa a gare mu? Domin da miyagun halittun ruhu da suke so su halaka mu! Su wanene su? Daga ina suka fito? Ta yaya suke so su yi mana lahani? Domin mu sami amsa, bari mu bincika a taƙaice abin da ya faru a farkon tarihin mutane.

HALITTU NA RUHU DA ABOKAN GABANMU NE

7. Har yaya Shaiɗan ya yi nasara wajen juya mutane daga Allah?

7 Kamar yadda muka koya daga Babi na 3 na wannan littafin, ɗaya daga cikin mala’ikun ya yi muradin sarauta bisa mutane saboda haka ya juya wa Allah baya. Daga baya aka san wannan mala’ikan da suna Shaiɗan Iblis. (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Bayan ya yaudari Hauwa’u, Shaiɗan ya yi nasara wajen juya yawancin mutane daga Allah a ƙarni na 16, ’yan kaɗan kawai suka kasance da aminci, kamar su Habila, Annuhu, da kuma Nuhu.—Ibraniyawa 11:4, 5, 7.

8. (a) Ta yaya wasu mala’iku suka zama aljanu? (b) Domin su tsira daga ambaliya ta zamanin Nuhu, menene aljanun suka yi?

8 A zamanin Nuhu, wasu mala’iku suka yi wa Jehobah tawaye. Suka ƙyale matsayinsu daga iyalin Allah na samaniya, suka sauƙo duniya, suka ɗauki jiki irin na mutane. Me ya sa? Mun karanta a Farawa 6:2: “Sai ’ya’yan Allah suka ga ’yan mata na mutane kyawawa ne; suka ɗauko wa kansu mata dukan waɗanda suka zaɓa.” Amma Jehobah Allah bai ƙyale irin wannan aiki na waɗannan mala’iku da kuma sakamakonsa na lalata mutane ya ci gaba ba. Ya kawo ambaliya a duniya da ta share dukan miyagun mutane kuma ya kāre bayinsa masu aminci ne kawai. (Farawa 7:17, 23) Saboda haka, mala’ikun da suka yi tawaye, ko kuma aljanu, aka tilasta musu barin jiki irin na mutane suka koma sama a halittar su ta ruhu. Suka goyi bayan Iblis, wanda ya zama “sarkin aljanu.”—Matta 9:34.

9. (a) Menene ya faru da aljanun sa’ad da suka koma sama? (b) Menene za mu bincika game da aljanun?

9 Sa’ad da mala’iku marasa biyayya suka koma sama, an mai da su bare kamar sarkinsu, Shaiɗan. (2 Bitrus 2:4) Ko da yake ba sa iya ɗaukan jikin mutane, har yanzu suna da mummunar rinjaya bisa mutane. Da taimakon waɗannan aljanu, Shaiɗan yana yaudarar “dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9; 1 Yohanna 5:19) Ta yaya? Ainihi, aljanun suna amfani da hanyoyin da suka tsara domin yaudarar mutane. (2 Korinthiyawa 2:11) Bari mu bincika wasu cikin waɗannan hanyoyi.

YADDA ALJANU SUKE YAUDARA

10. Menene sihiri?

10 Domin su yaudari mutane, aljanu suna amfani da sihiri. Yin sihiri ƙulla dangantaka ne da aljanu, ko kai tsaye ko kuma ta hannun mutane. Littafi Mai Tsarki ya la’anci sihiri kuma ya yi mana gargaɗi mu guji dukan wani abin da yake da alaƙa da shi. (Galatiyawa 5:19-21) Sihiri yana yi wa aljanu abin da ƙugiya take yi wa masūnci. Masūnci yana amfani da abubuwa da yawa a ƙugiya domin ya kama kifaye iri dabam dabam. Hakazalika, miyagun ruhohi suna amfani da sihiri iri dabam dabam domin su rinjayi dukan ire-iren mutane.

11. Menene duba, kuma me ya sa ya kamata mu guje shi?

11 Wata irin ƙugiya da aljanu suke amfani da ita ita ce duba. Mecece duba? Ƙoƙari ne a san abin da zai faru a nan gaba ko kuma wani abin sirri. Wasu ire-iren duba sun haɗa da hisabi, katin tarot, zuba wuri, duba da tafin hannu, ko kuma neman alama cikin mafarki. Ko da yake mutane da yawa suna tsammanin duba ba wani abu ba ne mai lahani, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa duba da miyagun ruhohi suna aiki tare. Alal misali, Ayukan Manzanni 16:16-18 sun ambaci “ruhu na duba” da ya sa yarinya take “duba.” Amma ta kasa duba sa’ad da aljanin ya fice daga gareta.

Aljanu suna amfani da hanyoyi da yawa su yaudari mutane

12. Me ya sa yake da haɗari a yi ƙoƙarin magana da matattu?

12 Wata hanya kuma da aljanu suke yaudarar mutane ita ce ta wajen ƙarfafa su su nemi taimakon matattu. Mutane da suke baƙin cikin rashin wanda suke ƙauna sau da yawa ana ruɗin su da mugun ra’ayi game da waɗanda suka mutu. Boka zai ba da bayani na musamman ko kuma ya yi magana da muryar da ta yi kama da ta mutumin da ya mutu. Saboda haka, mutane da yawa suka gaskata cewa matattu suna da rai da gaske, da cewa idan aka je gare su za su taimaki rayayyu su jimre baƙin cikinsu. Amma irin wannan “ta’aziyya” ƙarya ce kuma tana da haɗari. Me ya sa? Domin aljanu za su iya kwaikwayon muryar mamacin kuma su ba boka bayani game da mamacin. (1 Sama’ila 28:3-19) Bugu da ƙari, kamar yadda muka gani a Babi na 6, matacce ba ya rayuwa kuma. (Zabura 115:17) Saboda haka dukan wanda ya yi “sha’ani da matattu” miyagun ruhohi sun ruɗe shi kuma yana yin abin da ya saɓa wa nufin Allah. (Kubawar Shari’a 18:10, 11; Ishaya 8:19) Saboda haka, ka mai da hankali ka guji wannan mugun tarkon da aljanu suke amfani da shi.

13. Menene mutane da yawa da dā suke tsoron aljanu suka yi?

13 Miyagun ruhohi suna tsorata mutane ƙari ga yaudara. A yau, Shaiɗan da aljannunsa sun sani cewa ‘sauran zarafinsu kaɗan ne’ kafin a halakar su, kuma yanzu fajircinsu ya fi na dā. (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Duk da haka, dubban mutane da a dā suke rayuwa cikin tsoron irin waɗannan miyagun ruhohi sun ’yantu. Ta yaya suka sami ’yantuwa? Menene mutum zai iya yi idan ma yana sihiri?

YADDA ZA KA TSAYAYYA WA MIYAGUN RUHOHI

14. Kamar Kiristoci na ƙarni na farko a Afisas, ta yaya za mu ’yantu daga miyagun ruhohi?

14 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda za mu tsayayya wa miyagun ruhohi da kuma yadda za mu ’yantu daga gare su. Ka yi la’akari da misalin Kiristoci na ƙarni na farko a birnin Afisas. Wasunsu masu sihiri ne kafin su zama Kiristoci. Sa’ad da suka yanke shawarar cewa suna so su ’yantu daga sihiri, menene suka yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Waɗansu kuwa ba kaɗan ba daga masu-yin sihiri suka tattara littattafansu, suka ƙone su a gaban dukan mutane.” (Ayukan Manzanni 19:19) Ta wajen ƙona littattafansu na sihiri, waɗannan sababbin Kiristoci sun kafa misali ga dukan waɗanda suke so su yi tsayayya ga miyagun ruhohi a yau. Mutane da suke so su bauta wa Jehobah suna bukatar su kawar da dukan wani abin da yake da alaƙa da sihiri. Waɗannan za su haɗa da littattafai, mujallu, wasanni, kati, da kuma waƙoƙi da suke ƙarfafa ayyukan sihiri kuma suke masa ado. Sun haɗa har ila da layu da wasu abubuwa da ake saka wa domin kāriya daga aljannu.—1 Korinthiyawa 10:21.

15. Domin mu tsayayya wa miyagun ruhohi, menene muke bukatar mu yi?

15 Bayan wasu shekaru da Kiristoci a Afisas suka halaka littattafansu na sihiri, manzo Bulus ya rubuta musu: ‘kokuwarmu . . . da mugayen ruhohi ne.’ (Afisawa 6:12) Aljanun ba su kasala ba. Sun yi ƙoƙari su yi nasara. To, menene waɗannan Kiristoci suke bukatar su yi? Bulus ya ce: “Musamman kuma, ku ɗauki garkuwa ta bangaskiya, wadda za ku iya ɓice dukan jefejefe masu-wuta na Mugun [Shaiɗan] da ita.” (Afisawa 6:16) Iyaka girman garkuwarmu na ban gaskiya, haka iyaka tsayayyarmu ga miyagun ruhohi zai kasance.—Matta 17:20.

16. Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

16 Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu? Ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ƙarfin garu ya dangana ne a kan harsashinsa. Haka yake da bangaskiyarmu, ƙarfin bangaskiyarmu ya dangana ne sosai a kan ƙarfin tushensa, wato cikakken sani na Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Idan muna karatu kuma muna nazarin Littafi Mai Tsarki kullum, bangaskiyarmu za ta yi ƙarfi. Kamar garu mai ƙarfi, haka wannan bangaskiyar za ta kāre mu daga rinjayar miyagun ruhohi.—1 Yohanna 5:5.

17. Wane mataki yake da muhimmanci idan za mu tsayayya wa miyagun ruhohi?

17 Waɗanne matakai ne kuma waɗannan Kiristoci na Afisas suke bukatar su ɗauka? Suna bukatar ƙarin kāriya domin suna zaune a birni da yake cike da shaiɗanci. Saboda haka Bulus ya gaya musu: “Kuna addu’a kowane loto cikin Ruhu da kowace irin addua da roƙo.” (Afisawa 6:18) Tun da mu ma muna rayuwa a duniya da ta cika da shaiɗanci, roƙon Jehobah domin taimako yana da muhimmanci ƙwarai wajen tsayayya wa miyagun ruhohi. Hakika, muna bukatar mu kira sunan Jehobah a cikin addu’armu. (Misalai 18:10) Saboda haka, mu ci gaba da addu’a ga Allah ya “cece mu daga Mugun,” Shaiɗan Iblis. (Matta 6:13) Jehobah zai amsa irin wannan addu’ar.—Zabura 145:19.

18, 19. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa za mu yi nasara a kokawarmu da miyagun ruhohi? (b) Wace tambaya ce za a amsa a babi na gaba?

18 Miyagun ruhohi suna da haɗari, amma ba ma bukatar mu ji tsoronsu, idan muka tsayayya wa Iblis kuma muka kusaci Allah ta wajen yin nufinsa. (Yaƙub 4:7, 8) Ikon aljanun yana da iyaka. An yi musu horo a zamanin Nuhu, kuma za su fuskanci hukuncinsu na ƙarshe a nan gaba. (Yahuda 6) Ka tuna kuma cewa muna da kāriyar mala’iku masu iko na Jehobah. (2 Sarakuna 6:15-17) Waɗannan mala’iku suna ƙaunar su ga mun yi nasara wajen tsayayya wa miyagun ruhohi. Kamar a ce mala’iku masu adalci suna yaba mana ne. Saboda haka mu kasance kusa da Jehobah da kuma iyalinsa na halittun ruhu masu aminci. Mu kuma guji dukan wani irin sihiri kuma a kullum mu bi gargaɗin Kalmar Allah. (1 Bitrus 5:6, 7; 2 Bitrus 2:9) Sa’an nan za mu yi nasara a kokawarmu da miyagun ruhohi.

19 Amma me ya sa Allah ya ƙyale miyagun ruhohi da kuma mugunta da ya jawo wa mutane wahala ƙwarai? Za a amsa wannan tambayar a babi na gaba.

^ sakin layi na 2 Game da mala’iku masu adalci, Ru’ya ta Yohanna 5:11 ta ce: “Yawansu fa zambar goma ajiye zambar goma ne, da kuma dubban dubbai.” Saboda haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an halicci miliyoyin mala’iku.