Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA UKU

Ra’ayin Allah Game da Rai

Ra’ayin Allah Game da Rai
  • Menene Ra’ayin Allah Game da rai?

  • Menene Ra’ayin Allah Game da zubar da ciki?

  • Ta yaya za mu nuna muna daraja rai?

1. Wanene ya halicci dukan abubuwa masu rai?

“UBANGIJI shi ne Allah mai-gaskiya,” in ji annabi Irmiya. “Allah mai-rai ne.” (Irmiya 10:10) Bugu da ƙari, Jehobah Allah shi ne Mahaliccin dukan wani abu mai rai. Mala’iku suka ce masa: “Kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) A cikin waƙar yabo ga Allah, Sarki Dauda ya ce: “A wurinka maɓulɓular rai ta ke.” (Zabura 36:9) Saboda haka, rai kyauta ne daga Allah.

2. Menene Jehobah ya yi domin ya raya mu?

2 Jehobah ne yake raya mu. (Ayukan Manzanni 17:28) Shi yake ba mu abincin da muke ci, da ruwan da muke sha, da kuma iskar da muke sheƙa, da kuma ƙasar da muke zama a kanta. (Ayukan Manzanni 14:15-17) Jehobah ya yi wannan a hanyar da ta sa rayuwa ta kasance mai armashi. Amma saboda mu more rayuwa da kyau, muna bukatar mu koyi dokokin Allah kuma mu yi musu biyayya.—Ishaya 48:17, 18.

KA DARAJA RAI

3. Yaya Allah ya ɗauki kashe Habila?

3 Allah yana so mu daraja rai—ranmu da kuma rayukan wasu. Alal misali, a zamanin Adamu da Hauwa’u, ɗansu Kayinu ya yi fushi matuƙa da ƙaninsa Habila. Jehobah ya yi wa Kayinu gargaɗi cewa fushinsa zai sa ya yi zunubi mai tsanani. Kayinu ya yi banza da gargaɗin. Ya “tasa ma Habila ƙanensa, ya kashe shi.” (Farawa 4:3-8) Jehobah ya yi wa Kayinu horo domin ya kashe ɗan’uwansa.—Farawa 4:9-11.

4. A Dokar Musa, ta yaya Allah ya nanata yadda ya kamata a ɗauki rai?

4 Bayan shekaru dubbai, Jehobah ya bai wa ’ya’yan Isra’ila dokoki domin su taimaka musu su bauta masa yadda zai amince. Domin waɗannan dokoki an ba da su ta hannun annabi Musa, wani lokaci ana kiransu Dokar Musa. Dokar Musa ɗin ta ce: “Ba za ka yi kisankai ba.” (Kubawar Shari’a 5:17) Wannan ya nuna wa Isra’ilawa cewa Allah yana daraja ran mutane kuma dole ne mutane su daraja rayukan wasu.

5. Yaya ya kamata mu ɗauki zubar da ciki?

5 To, ran wanda ba a haifa ba fa? In ji Dokar Musa, haddasa mutuwar jariri a cikin uwarsa ba daidai ba ne. Hakika, har irin wannan ran yana da muhimmanci ga Jehobah. (Fitowa 21:22, 23; Zabura 127:3) Wannan ya nuna cewa zubar da ciki ba shi da kyau.

6. Me ya sa bai kamata mu ƙi wani ba?

6 Daraja rai ya ƙunshi ɗaukan mutane yadda ya kamata. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan wanda ya ƙi ɗan’uwansa mai-kisankai ne: kun sani babu mai-kisankai wanda shi ke da rai na har abada cikinsa zaune.” (1 Yohanna 3:15) Idan muna son rai madawwami, muna bukatar mu cire dukan wata ƙiyayyar wani da ke cikin zuciyarmu, domin ƙiyayya ita ce tushen yawancin mugunta. (1 Yohanna 3:11, 12) Yana da muhimmanci mu koyi mu yi ƙaunar juna.

7. Waɗanne irin halaye ne ba sa daraja rai?

7 To, yaya batun daraja namu ran? Galibi, mutane ba sa so su mutu, amma wasu suna ɗaukar kasada domin nishaɗi. Alal misali, mutane da yawa suna shan taba, ko su tauna ta, ko kuma su sha miyagun ƙwayoyi domin annashuwa. Irin wannan abubuwa suna iya yi wa jiki lahani kuma sau da yawa suna kashe masu shansu. Mutumin da yake jarabar shan irin waɗannan abubuwa bai ɗauki rai da tsarki ba. Waɗannan halaye ba su da tsabta a gaban Allah. (Romawa 6:19; 12:1; 2 Korinthiyawa 7:1) Domin mu bauta wa Allah yadda zai amince, dole ne mu bar irin waɗannan halaye. Ko da yake yin haka zai yi wuya, Jehobah zai yi mana taimako da muke bukata. Kuma yana yabon ƙoƙarin da muke yi mu daraja ranmu domin kyauta ne mai muhimmanci daga wurinsa.

8. Me ya sa za mu riƙa tuna cewa ya kamata mu mai da hankali?

8 Idan muna daraja rai, za mu riƙa tuna cewa ya kamata mu mai da hankali. Ba za mu riƙa rayuwa ta ko oho ba kuma ba za mu ɗauki kasada ba domin nishaɗi ko annashuwa. Za mu guji mugun tuƙi da kuma miyagun wasanni. (Zabura 11:5) Dokar Allah ga Isra’ila ta dā ta ce: “Sa’anda ka gina sabon gida, sai ka ja dangarma bisa beni, domin kada ka ja ma gidanka alhakin jini, idan wani ya faɗo daga can.” (Kubawar Shari’a 22:8) Cikin jituwa da mizanin da aka bayar a wannan dokar, ka tabbata cewa matakala na gidanka na sama suna gyare domin kada santsi ya kwashi wani ya faɗi ya ji rauni. Idan kana da mota, ka tabbata cewa tuƙa ta ba shi da haɗari. Kada ka ƙyale gidanka ko kuma motarka ta kasance haɗari ga kanka da kuma wasu.

9. Idan muna daraja rai, yaya za mu yi da dabbobi?

9 To, ran dabba fa? Wannan ma yana da daraja a wajen Mahaliccinsa. Allah ya ƙyale kashe dabbobi domin abinci da kuma tufafi ko kuma domin a kāre mutane daga haɗari. (Farawa 3:21; 9:3; Fitowa 21:28) Amma, yi wa dabbobi mugunta ko kuma kashe su kawai domin wasa ba daidai ba ne kuma yana nuna matuƙar rashin daraja tsarkakar rai.—Misalai 12:10.

KA DARAJA JINI

10. Ta yaya Allah ya nuna cewa da nasaba tsakanin rai da jini?

10 Bayan Kayinu ya kashe ɗan’uwansa Habila, Jehobah ya gaya masa: “Muryar jinin ƙaninka ta yi ƙara a wurina daga ƙasa.” (Farawa 4:10) Sa’ad da Allah ya yi magana game da jinin Habila, yana magana ne game da ran Habila. Kayinu ya ɗauki ran Habila, yanzu za a hori Kayinu. Jinin Habila, ko kuma ransa yana kuka ne ga Jehobah ya yi hukunci. An sake nuna nasaba da take tsakanin jini da rai bayan Ambaliya ta zamanin Nuhu. Ƙafin Ambaliyar, mutane suna cin ’ya’yan itatuwa, da ganyaye. Bayan Ambaliyar, Jehobah ya gaya wa Nuhu da kuma ’ya’yansa: “Kowane abu mai-motsi wanda ya ke da rai, za ya zama abincinku; kamar ganye duk na ba ku su.” Amma, Allah ya yi wannan hanin: “Sai dai nama tare da ransa, watau jininsa ke nan, wannan ba za ku ci ba.” (Farawa 1:29; 9:3, 4) A bayyane yake, Jehobah ya nuna nasaba da ke tsakanin rai da jinin halitta.

11. Menene Jehobah ya hana a yi da jini tun daga zamanin Nuhu?

11 Muna daraja jini ta wajen ƙin cinsa. A cikin Dokar da Jehobah ya ba wa Isra’ilawa, ya ba da wannan umurni: “Kuma kowane mutum . . . wanda yana farauta ya kama kowane nama, ko tsuntsu, halal ga ci; sai shi zubarda jininsa, shi rufe da ƙura. . . . Domin wannan na ce ma ’ya’yan Isra’ila, Ba za ku ci jini na kowane irin nama” ba. (Leviticus 17:13, 14) Allah ya ba Nuhu umurnin kada a ci jini, shekaru 800 da farko, har yanzu ya kamata mu bi umurnin. Yadda Jehobah ya ɗauki wannan a bayyane yake sarai: Bayinsa za su iya cin naman dabba amma ba jininsa ba. Za su zub da jinin a ƙasa—wato, suna mai da ran halittar ga Allah.

12. Wace doka game da jini ruhu mai tsarki ya bayar a ƙarni na farko kuma yake ci gaba har zuwa yau?

12 Umurni makamancin wannan yana kan Kiristoci. Manzanni da kuma dattawa da suke ja-gora a tsakanin mabiyan Yesu a ƙarni na farko suka taru suka yanke shawarar doka da dukan ikilisiyar Kirista za ta bi. Ga abin da suka ce: “Ya yi kyau ga Ruhu Mai-tsarki, da mu kuma, kada mu nawaita muku wani abu gaba da waɗannan wajibai; ku hanu daga abin aka miƙa ma gumaka, da jini kuma, da abin da aka maƙare [barin jini cikin nama], da fasikanci.” (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Saboda haka dole ne mu guji ‘jini.’ A idanun Allah, yin haka muhimmancinsa ɗaya ne da guje wa bautar gunki da kuma lalata.

Idan likitan ka ya ce kada ka sha giya, za ka yarda a saka ne a jikin ka ta jijiyoyinka?

13. Ka ba da misalin abin da ya sa guje wa jini ya haɗa da guje wa ƙarin jini.

13 Shin umurnin mu guji jini ya haɗa ne da karɓar ƙarin jini? E. Alal misali, a ce Likita ya hana ka shan giya. Wannan yana nufin kada ka sha amma kana iya saka ta a jikinka ta jijiyoyinka ne? A’a! Hakazalika, guje wa jini yana nufin kada mu saka shi a jikinmu sam. Saboda haka umurnin mu guje wa jini yana nufin cewa kada mu ƙyale kowa ya saka mana jini ta cikin jijiyoyinmu.

14, 15. Idan likitoci suka ce za su ƙara wa Kirista jini, me ya kamata ya yi kuma me ya sa?

14 Idan Kirista ya ji mugun rauni ko kuma yana bukatar fiɗa fa? A ce likitoci sun ce dole ne a ƙara masa jini idan ba haka ba zai mutu. Hakika, Kirista ba zai so ya mutu ba. Domin ƙoƙarinsa ya kāre kyauta mai muhimmanci ta rai daga Allah, zai yarda da wasu fannonin magani da ba su ƙunshi jini ba. Saboda haka, zai iya neman irin wannan magani idan wannan yana samuwa kuma zai yarda da wasu hanyoyin magani da ba su ƙunshi jini ba.

15 Ya kamata ne Kirista ya taka dokar Allah domin ya ɗan ƙara tsawon rayuwarsa a wannan zamanin? Yesu ya ce: “Dukan wanda ya ke nufi shi ceci ransa, ɓadda ransa shi ya ke yi: kuma dukan wanda ya ke ɓadda ransa sabili da ni, samunsa ya ke yi.” (Matta 16:25) Ba ma so mu mutu. Amma idan muna so mu yi tattalin ranmu ta wajen taka dokar Allah, za mu shiga haɗarin rasa rai madawwami. Muna masu hikima, mu dogara ga adalcin dokar Allah, da cikakken tabbacin cewa idan muka mutu domin wani abu, Wanda Ya Ba Mu Rai zai tuna da mu a lokacin tashin matattu kuma ya sake ba mu kyauta mai tamani na rai.—Yohanna 5:28, 29; Ibraniyawa 11:6.

16. Menene bayin Allah suke da niyyar yi game da jini?

16 A yau, bayin Allah masu aminci suna da niyyar bin umurninsa game da jini. Ba za su ci jini ba ta kowace hanya. Kuma ba za su karɓi jini ba domin magani. * Sun tabbata cewa Mahaliccin jini ya san abin da ya fi kyau a gare su. Ka gaskata haka?

HANYAR DA TA DACE KAWAI NA AMFANI DA JINI

17. A Isra’ila ta dā, wace hanyar amfani da jini Jehobah Allah ya amince da ita?

17 Dokar Musa ta nanata hanyar da ta dace na amfani da Jini. Game da bauta da ake bukata daga Isra’ilawa na dā Jehobah ya ba da umurni: “Ran nama yana cikin jini: na kuwa ba ku shi bisa bagadi domin a yi kafarar rayukanku: gama jini ne ke yin kafara saboda rai.” (Leviticus 17:11) Sa’ad da Isra’ilawa suka yi zunubi, za su sami gafara ta wajen miƙa dabba kuma a zuba kaɗan cikin jininsa a kan bagade a mazauni ko kuma daga baya a haikalin Allah. Hanyar da ta dace na amfani da jini ita ce irin waɗannan hadayun.

18. Wane amfani da albarka za mu iya samu daga jinin Yesu da aka zubar?

18 Kiristoci na gaskiya ba sa ƙarƙashin Dokar Musa kuma saboda haka ba sa ba da hadaya ta dabbobi su zuba jinin dabba a kan bagadi. (Ibraniyawa 10:1) Amma, amfani da jini a kan bagadi a zamanin Isra’ila ta dā yana nuni da hadaya na ƙarshe mafi tamani—na Ɗan Allah, Yesu Kristi. Kamar yadda muka koya a Babi na 5 na wannan littafi, Yesu ya ba da ransa na mutum ya ƙyale a zubar da jininsa wajen hadaya. Sa’ad da ya haura zuwa sama kuma sau ɗaya tak ba ƙari ya miƙa tamanin jininsa da aka zubar ga Allah. (Ibraniyawa 9:11, 12) Wannan ya ba da dalilin gafarta zunubai kuma ya buɗe mana hanyar samun rai madawwami. (Matta 20:28; Yohanna 3:16) Wannan amfani da jini ya kasance mai matuƙar muhimmanci! (1 Bitrus 1:18, 19) Sai ta wajen bangaskiya ga jinin Yesu da ya zubar za mu sami tsira.

Ta yaya za ka daraja rai da kuma jini?

19. Dole ne mu yi menene domin mu ‘kuɓuta daga jinin dukan mutane’?

19 Ya kamata mu yi wa Jehobah Allah godiya domin ya yi mana tanadin rai cikin ƙauna! Kuma hakan bai kamata ba ne ya motsa mu mu gaya wa mutane game da zarafin samun rai madawwami daga bangaskiya ga hadaya ta Yesu? Damuwa ta ibada na rayukan ’yan’uwa mutane za ta motsa mu mu yi haka da ƙwazo da kuma himma. (Ezekiel 3:17-21) Idan muka sauƙe wannan hakkin yadda ya dace, za mu iya cewa kamar yadda manzo Bulus ya ce: “Ni kuɓutace ne daga jinin dukan mutane. Gama ban ji nauyin bayyana muku dukan shawarar Allah.” (Ayukan Manzanni 20:26, 27) Gaya wa mutane game da Allah da kuma nufinsa ita ce hanya mafi kyau da ya nuna cewa muna daraja rai da jini ƙwarai da gaske.

^ sakin layi na 16 Domin ƙarin bayani game da wasu hanyoyin magani maimakon ƙarin jini, ka dubi shafuffuka 13-17 na mujallar nan How Can Blood Save Your Life? (Ta Yaya Jini Zai Ceci Ranka?) da Shaidun Jehobah suka wallafa.