Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a

Ka Kusaci Allah Cikin Addu’a
  • Me ya sa za mu yi addu’a ga Allah?

  • Menene dole ne mu yi domin Allah ya saurare mu?

  • Ta yaya Allah yake amsa addu’o’inmu?

“Wanda ya yi sama da duniya” yana shirye ya saurari addu’o’inmu

1, 2. Me ya sa za mu ɗauki addu’a cewa gata ce mai girma, kuma me ya sa muke bukatar mu san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da ita?

IDAN aka gwada da sararin samaniya, duniya ƙanƙanuwa ce. Hakika, ga Jehobah “wanda ya yi sama da duniya,” al’ummai kamar ɗigon ruwa suke daga guga. (Zabura 115:15; Ishaya 40:15) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: Jehobah “yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; za ya kuma ji kukarsu, ya cece su.” (Zabura 145:18, 19) Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi! Mahalicci mai iko duka yana kusa da mu kuma yana sauraronmu idan muka ‘kira shi da gaskiya.’ Gata ce mu je gaban Allah cikin addu’a!

2 Amma idan muna so Jehobah ya saurari addu’armu, dole ne mu yi addu’a a hanyar da ya amince da ita. Za mu iya yin haka ne idan muka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da addu’a. Yana da muhimmanci mu fahimci abin da Nassosi suka ce game da wannan batu, domin addu’a tana taimakonmu mu kusanci Jehobah.

ME YA SA ZA MU YI ADDU’A GA JEHOBAH?

3. Wane dalili ne mai muhimmanci ya sa za mu yi addu’a ga Jehobah?

3 Wani dalili ɗaya mai muhimmanci da ya sa za mu yi addu’a ga Jehobah shi ne cewa shi ya gayyace mu mu yi haka. Kalmarsa ta ƙarfafa mu: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Hakika kuwa ba za mu so mu yi banza da irin wannan tanadi da Mamallakin dukan sararin samaniya ya yi mana ba!

4. Ta yaya addu’a a kai a kai ga Jehobah yake ƙarfafa dangantakarmu da shi?

4 Wani dalili kuma na addu’a a kai a kai ga Jehobah shi ne cewa hanyar ƙarfafa dangantakarmu da shi ne. Abokanai na gaskiya ba sai sa’ad da suke bukatar wani abu suke magana da juna ba. Maimakon haka, abokanai nagari sukan ƙaunaci juna, kuma dangantakarsu tana ƙarfafa sa’ad da suka faɗi ra’ayinsu, damuwarsu, da kuma juyayinsu a sake. A wasu yanayi, haka dangantakarmu da Jehobah Allah take. Da taimakon wannan littafin, ka koyi abubuwa masu yawa game da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da Jehobah, mutuntakarsa, da kuma nufinsa. Ka fahimci cewa shi wani ne da gaske. Addu’a tana ba ka zarafi ka furta tunaninka da kuma motsin zuciyarka ga Ubanka na samaniya. Sa’ad da ka yi haka, za ka kusaci Jehobah.—Yaƙub 4:8.

WAƊANNE BUKATU NE DOLE MU CIKA?

5. Menene ya nuna cewa Jehobah ba ya sauraron dukan addu’o’i?

5 Shin Jehobah yana sauraron dukan addu’o’i ne? Ka yi la’akari da abin da ya gaya wa Isra’ilawa masu tawaye a zamanin annabi Ishaya: “Sa’anda ku ke yi mini yawan addu’oi, ba ni ji ba: hannuwanku cike su ke da jini.” (Ishaya 1:15) Saboda haka wasu ayyuka za su iya sa Allah ya ƙi sauraron addu’o’inmu. Domin Allah ya saurari addu’o’inmu da tagomashi, dole ne mu cika wasu bukatu.

6. Domin Allah ya saurari addu’o’inmu, mecece muhimmiyar bukata, kuma ta yaya za mu cika wannan?

6 Bukata mai muhimmanci, ita ce ba da gaskiya. (Markus 11:24) Manzo Bulus ya rubuta: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah sai shi bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6) Kasancewa da bangaskiya ta gaske ya fi kawai sanin cewa akwai Allah kuma cewa yana sauraro kuma yana amsa addu’o’i. Ta wajen ayyuka ake tabbatar da bangaskiya. Dole ne mu tabbatar da cewa muna da bangaskiya ta yadda muke rayuwa a kowace rana.—Yaƙub 2:26.

7. (a) Me ya sa ya kamata mu daraja Jehobah sa’ad da muke yin magana da shi? (b) Sa’ad da muke addu’a ga Allah, ta yaya za mu nuna tawali’u da kuma zuciya mai gaskiya?

7 Jehobah yana bukatar waɗanda suka je gare shi cikin addu’a su yi haka da tawali’u da kuma zuciya mai gaskiya. Muna bukatar mu kasance da tawali’u sa’ad da muke magana da Allah ko ba haka ba? Sa’ad da mutane suka sami damar magana da sarki ko kuma shugaban ƙasa, suna daraja shi, suna ɗaukaka matsayi mai girma na mai mulkin. Muna bukatar ba wa Jehobah daraja fiye da haka ma! (Zabura 138:6) Domin shi ne “Allah Alƙadiru.” (Farawa 17:1) Sa’ad da muka yi addu’a ga Allah, yadda muka yi haka ya kamata ya nuna cewa mun fahimci matsayinmu cikin tawali’u a gabansa. Irin wannan tawali’un zai kuma motsa mu mu yi addu’a daga zuciyarmu cikin gaskiya, za mu guje wa maimaita addu’a.—Matta 6:7, 8.

8. Ta yaya za mu yi aiki da ya yi daidai da addu’armu?

8 Wani abu kuma da zai sa Allah ya saurare mu shi ne yin ayyukan da suka jitu da addu’o’inmu. Jehobah yana so mu yi iya gwargwadon ƙarfinmu mu yi abin da muka yi addu’a dominsa. Alal misali, idan muka yi addu’a, “ka ba mu yau abincin yini,” dole ne mu yi aiki da ƙwazo a dukan aiki da za mu iya yi. (Matta 6:11; 2 Tassalunikawa 3:10) Idan muka yi addu’a domin mu magance wani rauni na jiki, dole ne mu mai da hankali mu guji dukan wani yanayi da zai iya kai mu cikin jaraba. (Kolossiyawa 3:5) Ƙari ga waɗannan bukatu masu muhimmanci, da wasu tambayoyi game da addu’a da za mu bukaci amsa.

AMSA WASU TAMBAYOYI GAME DA ADDU’A

9. Ga wa za mu yi addu’a, kuma ta wurin wa?

9 Ga waye ya kamata mu yi addu’a? Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a ga “Ubanmu wanda ke cikin sama.” (Matta 6:9) Saboda haka, addu’armu dole ne ta kasance ga Jehobah Allah shi kaɗai. Amma kuma, Jehobah ya bukaci mu fahimci matsayin Ɗansa makaɗaici, Yesu Kristi. Kamar yadda muka koya a Babi na 5, an aiko Yesu duniya domin ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa. (Yohanna 3:16; Romawa 5:12) Shi ne Babban Firist da kuma Alƙali da aka naɗa. (Yohanna 5:22; Ibraniyawa 6:20) Saboda haka, Nassosi suka umurce mu mu yi addu’o’inmu ta wurin Yesu. Shi kansa ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Domin a saurari addu’o’inmu, dole ne mu yi addu’a ga Jehobah ta wurin Ɗansa.

10. Me ya sa babu taƙaitaccen yanayi da ake bukata sa’ad da ake addu’a?

10 Dole ne mu kasance cikin wani yanayi sa’ad da muke addu’a? A’a. Jehobah bai bukaci kasancewa cikin wani yanayi ba, ko na hannu ko kuma na dukan jiki. Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa daidai ne a yi addu’a a cikin yanayi masu yawa. Wannan ya haɗa da yin addu’a a zaune, a durƙushe, a tsaye. (1 Labarbaru 17:16; Nehemiah 8:6; Daniel 6:10; Markus 11:25) Abin da ya fi muhimmanci shi ne zuciyar kirki, ba abin da wasu mutane za su gani ba. Hakika, sa’ad da muke ayyukanmu na yau da kullum ko kuma sa’ad da muka fuskanci yanayi na gaggawa, muna iya yin addu’a a zuciyarmu a dukan inda muke. Jehobah yana saurarar addu’a ma da wasu ba su lura da ita ba.—Nehemiah 2:1-6.

11. Waɗanne damuwa ne namu za su kasance batutuwa da suka dace na addu’a?

11 Menene za mu roƙa? Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Idan mun roƙi komi daidai da nufinsa, [Jehobah] yana jinmu.” (1 Yohanna 5:14) Saboda haka mu roƙi abubuwa da suke bisa ga nufin Allah. Nufinsa ne mu yi roƙo game da abubuwa da suka dame mu? Hakika kuwa! Addu’a ga Jehobah za ta iya kasance kamar magana ne da aboki na kud da kud. Za mu iya ‘zazzage zuciyarmu’ ga Allah. (Zabura 62:8) Daidai ne a gare mu mu yi roƙo domin ruhu mai tsarki, domin zai taimake mu mu yi abin da ke nagari. (Luka 11:13) Za mu iya kuma yin roƙo domin ja-gora sa’ad da muke so mu yanke shawara, da kuma jimiri sa’ad da muke fuskantar matsaloli. (Yaƙub 1:5) Sa’ad da muka yi zunubi, ya kamata mu roƙi gafara bisa ga hadayar Kristi. (Afisawa 1:3, 7) Hakika, ba al’amuran kanmu ba ne ya kamata su zama batutuwan addu’o’inmu. Mu yi wa wasu mutane addu’a—’yan iyalinmu da kuma ’yan’uwanmu masu bi.—Ayukan Manzanni 12:5; Kolossiyawa 4:12.

12. Ta yaya za mu ba wa batutuwa da suka shafi Ubanmu na sama wuri mai muhimmanci a addu’armu?

12 Batutuwa da suka shafi Jehobah Allah ya kamata mu sa su farko a addu’o’inmu. Dole ne mu furta yabo da godiya daga zukatanmu domin dukan alherinsa. (1 Labarbaru 29:10-13) Yesu ya koyar da addu’ar misali, da ke rubuce a Matta 6:9-13, a ciki ya koyar da mu mu yi addu’a cewa a tsarkake sunan Allah. Mulkin Allah ya zo kuma bayan wannan a yi nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a sama. Bayan ya gama da waɗannan batutuwa da suka shafi Jehobah ne Yesu ya mai da hankali ga damuwa na mutane. Sa’ad da muka ba wa Allah wuri mai muhimmanci a addu’armu, muna nuna cewa ba damuwarmu ba ce kawai ta dame mu.

13. Menene Nassosi suka nuna game da tsawon addu’a da za a karɓa?

13 Yaya ya kamata tsawon addu’armu ya kasance? Littafi Mai Tsarki bai kafa iyaka ga tsawon lokacin da ya kamata mu yi muna addu’a, na kanmu ko ga jama’a ba. Zai iya kasancewa daga gajeriyar addu’a kafin cin abinci zuwa doguwar addu’ar kanmu a nan muna iya buɗe cikinmu ga Jehobah. (1 Sama’ila 1:12, 15) Amma fa, Yesu ya la’anci mutanen da suke nuna cewa suna da adalci, masu addu’a don mutane su yabe su. (Luka 20:46, 47) Irin wannan addu’o’i ba sa burge Jehobah. Abin da yake da muhimmanci shi ne mu yi addu’a da ta fito daga zuciyarmu. Saboda haka, tsawon addu’a da za a karɓa zai bambanta bisa ga bukata da kuma yanayi.

Yana iya sauraron addu’armu a kowane lokaci

14. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ƙarfafa mu mu “yi addu’a,” a kai a kai kuma me ya sa wannan yake da ban ƙarfafa?

14 Sau nawa ya kamata mu yi addu’a? Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu “yi addu’a,” a kai a kai mu “lizima cikin addu’a,” kuma ya ce mu “yi addu’a ba fasawa.” (Matta 26:41; Romawa 12:12; 1 Tassalunikawa 5:17) Hakika, waɗannan furci ba sa nufin cewa dole ne mu riƙa addu’a ga Jehobah dare da rana ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki yana ariritarmu ne mu riƙa addu’a a kai a kai, mu riƙa yi wa Jehobah godiya domin alherinsa kuma mu riƙa zuba masa idanu domin ja-gora, ƙarfafa, da kuma ƙarfi. Ba abin farin ciki ba ne mu sani cewa Jehobah bai kafa iyaka ba ga tsawon lokaci da za mu yi muna addu’a ko kuma yawan lokaci da za mu yi masa addu’a ba? Idan muna ɗaukaka gatar yin addu’a, za mu nemi zarafin yin addu’a ga Ubanmu na sama.

15. Me ya sa za mu ce “Amin” a ƙarshen addu’armu ko kuma ga jama’a?

15 Me ya sa za mu ce “Amin” a ƙarshen addu’a? Kalmar nan “Amin” yana nufin “hakika,” ko kuma “hakan ya kasance.” Misalai na Nassosi sun nuna cewa daidai ne mu ce “Amin” a ƙarshen addu’ar kanmu ko kuma ga jama’a. (1 Labarbaru 16:36; Zabura 41:13) Ta wajen cewa “Amin” a ƙarshen addu’a, muna tabbatarwa ne cewa furcin da muka yi da gaske ne. Sa’ad da muka ce “Amin”—ko a hankali ko da babbar murya—a ƙarshen addu’ar wani, muna nuna cewa mun yarda da abin da ya ce.—1 Korinthiyawa 14:16.

YADDA ALLAH YAKE AMSA ADDU’O’INMU

16. Wane tabbaci ne za mu yi game da addu’a?

16 Da gaske ne Jehobah yana amsa addu’o’i? Hakika kuwa! Muna da dalilai masu ƙarfi na tabbata cewa mai “jin addu’a” ne, yana amsa addu’o’i da miliyoyin mutane suka yi da zuciya ɗaya. (Zabura 65:2) Amsar Jehobah ga addu’armu tana iya zuwa a hanyoyi dabam dabam.

17. Me ya sa za a iya cewa Allah yana amfani da mala’ikunsa da kuma bayinsa na duniya wajen amsa addu’o’inmu?

17 Jehobah yana amfani da mala’ikunsa da kuma bayinsa na duniya ya amsa addu’o’i. (Ibraniyawa 1:13, 14) Da labari masu yawa na mutane da suka yi addu’a ga Allah ya taimake su su fahimci Littafi Mai Tsarki ba da daɗewa ba bayan haka bayin Jehobah suka same su. Irin waɗannan labaran sun ba da tabbatacin ja-gorar mala’iku a aikin wa’azi na Mulki. (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Domin ya amsa addu’o’inmu da muka yi a lokacin da muke da bukata, Jehobah yana motsa wani Kirista ya taimake mu.—Misalai 12:25; Yaƙub 2:16.

Domin amsa addu’o’inmu, Jehobah yana iya motsa Kiristoci su taimake mu

18. Ta yaya Jehobah yake amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma Kalmarsa ya amsa addu’o’in bayinsa?

18 Jehobah Allah kuma yana amfani da ruhunsa mai tsarki da kuma Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya amsa addu’o’in bayinsa. Yana iya amsa addu’armu na taimako mu jimre wa gwaji ta wajen yi mana ja-gora da kuma ba mu ƙarfi ta wajen ruhunsa mai tsarki. (2 Korinthiyawa 4:7) Sau da yawa amsar addu’armu domin ja-gora daga Littafi Mai Tsarki take zuwa, a nan Jehobah yake yi mana taimako mu yanke shawara da ta dace. Ana iya samun Nassosi da za su yi taimako a lokacin nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu da kuma sa’ad da muka karanta littatafai na Kirista, kamar irin wannan littafin. Wani bayani da muke bukata ana iya tuna mana shi ta wajen abin da aka faɗa a taron Kirista ko kuma ta wajen kalamin dattijo a ikilisiya da ya damu da yanayinmu.—Galatiyawa 6:1.

19. Menene ya kamata mu tuna idan kamar ba a amsa addu’o’inmu ba?

19 Idan kamar Jehobah yana jinkirin amsa addu’o’inmu, wannan ba domin ba zai iya amsa su ba ne. Maimakon haka, dole mu tuna cewa Jehobah yana amsa addu’o’i ne bisa ga nufinsa kuma a lokacinsa. Ya san abin da muke bukata da kuma yadda za mu magance su fiye da yadda muka sani. Sau da yawa yana ƙyale mu mu ‘yi ta roƙo, mu yi ta nema, mu yi ta ƙwanƙwasawa.’ (Luka 11:5-10) Irin wannan naciya tana nuna wa Allah cewa muradinmu yana da ƙarfi kuma bangaskiyarmu ta gaskiya ce. Bugu da ƙari, Jehobah zai amsa addu’o’inmu a hanyar da ba za ta bayyana ƙiri ƙiri ba a gare mu. Alal misali, zai amsa addu’armu game da wani gwaji, ba ta wajen kawar da matsalar ba, amma ta wajen ba mu ƙarfi mu jimre.—Filibbiyawa 4:13.

20. Me ya sa za mu yi amfani da zarafin addu’a?

20 Ya kamata mu zama masu godiya domin Mahaliccin wannan sararin samaniya yana kusa da dukan waɗanda suke kiransa cikin addu’ar da ta dace. (Zabura 145:18) Ya kamata mu yi amfani da zarafin yin addu’a. Idan muka yi haka, za mu sami bege mai ban farin ciki na kusantar Jehobah, mai amsa addu’o’i.