Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi

Ma’anar Sunan Allah da Yadda Ake Amfani da Shi

A NAKA Littafi Mai Tsarki, yaya aka fassara Zabura 83:18? New World Translation of the Holy Scriptures ya fassara shi haka: “Domin mutane su sani, kai wanda sunanka ne Jehobah, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan Duniya.” Wasu fassara na Littafi Mai Tsarki ma sun fassara shi kusan haka. Duk da haka, fassara masu yawa sun cire sunan Jehobah, sun sauya shi da laƙabi irin su “Ubangiji” ko kuma “Madawwami.” Me ya kamata ya kasance a wannan ayar? Laƙabi ko kuma sunan Jehobah?

Sunan Allah da bakaken Ibrananci

Wannan ayar ta yi magana game da sunan. A Ibrananci na asali da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da shi, suna marar na biyunsa ya bayyana a nan. An rubuta shi haka יהוה (YHWH) da baƙaƙen Ibrananci. A Hausa, ana kiran sunan “Jehobah” ne. Wannan sunan ya bayyana ne kawai a aya ɗaya ta Littafi Mai Tsarki? A’a. Ya bayyana a rubutun ainihi na Ibrananci sau 7,000!

Yaya muhimmancin sunan Allah? Ka yi la’akari da addu’ar alama da Yesu Kristi ya koya mana. Ya fara ta da cewa: “Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Daga baya, Yesu ya yi addu’a: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Allah ya amsa daga sama, yana cewa: “Na rigaya na ɗaukaka shi, kuma ni sake ɗaukaka shi.” (Yohanna 12:28) Babu shakka, sunan Allah yana da muhimmanci ƙwarai. To, me ya sa, wasu masu fassara suka sake sunan da laƙabi a Littafi Mai Tsarki da suka fassara?

Kamar dai dalilan biyu ne. Na farko, wasu suna da’awar cewa bai kamata a yi amfani da sunan ba tun da ba a san yadda ake furta shi ba a yau. Ba a rubuta Ibrananci na dā da wasula. Saboda haka, a yau babu wanda ya tabbata yadda mutanen zamanin Littafi Mai Tsarki suka furta YHWH. Amma, ya kamata ne wannan ya hana mu amfani da sunan Allah? A zamanin Littafi Mai Tsarki, sunan nan Yesu wataƙila ana furta shi ne Yeshua ko kuma Yehoshua—babu wanda zai iya tabbatawa. Duk da haka, mutane a dukan duniya suna amfani da suna Yesu yadda aka fi sabawa da shi a yarensu. Ba sa yin jinkirin amfani da sunan domin ba su san yadda ake furta shi ba a ƙarni na farko. Hakazalika, idan ka tafi wata ƙasa, za ka ga cewa yadda suke furta sunanka zai bambanta. Saboda haka, rashin tabbacin yadda ake furta sunan Allah a dā ba dalili ba ne na ƙin amfani da shi.

Wani dalili kuma da ake bayarwa na cire sunan Allah daga Littafi Mai Tsarki shi ne tsohuwar al’adar Yahudawa. Yawancinsu sun yi imani cewa bai kamata a furta sunan Allah ba. Wannan imani a bayyane yake cewa ya samo asalinsa ne daga rashin fahimtar doka ta Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ba za ka kama sunan Ubangiji Allahnka banza ba; gama Ubangiji ba za ya kuɓutadda wanda yana kama sunansa banza ba.”—Fitowa 20:7.

Wannan dokar ta hana kama sunan Allah a banza. Amma ta hana kama sunan Allah ne da daraja? Ko kaɗan. Marubutan Littafin Mai Tsarki na Ibrananci (“Tsohon Alkawari”) dukan su mutane ne masu aminci waɗanda suka kiyaye Dokar da Allah ya bai wa Isra’ila ta dā. Duk da haka, suna kama sunan Allah sau da yawa. Alal misali, sun saka shi cikin zabura da jama’a masu yawa suke rerawa lokacin bauta. Jehobah Allah ya umurci masu bauta masa su kira sunansa, kuma masu aminci sun yi biyayya da hakan. (Joel 2:32; Ayukan Manzanni 2:21) Saboda haka, Kiristoci a yau ba sa ƙin kama sunan Allah da daraja, kamar yadda Yesu ya yi.—Yohanna 17:26.

Masu fassarar Littafi Mai Tsarki sun yi kuskure mai tsanani wajen sauya sunan Allah da laƙabi. Sun sa Allah ya kasance yana da nesa kuma ba zai yiwu a ƙulla dangantaka da shi ba, alhali kuma Littafi Mai Tsarki ya aririci mutane su yi ƙoƙari ‘Allah ya amince da su.’ (Zabura 25:14 Littafi Mai Tsarki) Ka yi tunanin wani amininka. Ta yaya za ku zama aminai idan ba ka san sunan abokinka ba? Hakazalika, sa’ad da aka bar mutane cikin duhu game da sunan Allah, Jehobah, ta yaya za su kusaci Allah? Bugu da ƙari, sa’ad da mutane ba sa kama sunan Allah, jahilai ne ga ma’anarsa mai ban mamaki. Menene ma’anar sunan Allah?

Allah da kansa ya yi bayani game da ma’anar sunansa ga bawansa mai aminci Musa. Sa’ad da Musa ya yi tambaya game da sunan Allah, Jehobah ya amsa yana cewa: “Zan Kasance yadda na ga dama.” (Fitowa 3:14; Rotherham) Saboda haka, Jehobah zai kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa.

Da a ce kana iya kasancewa dukan abin da ka ga dama, me za ka yi? Me za ka yi wa abokananka? Idan ɗaya daga cikinsu ya faɗa rashin lafiya, za ka zama likita domin ka yi masa magani. Idan wani kuma ya yi hasarar dukiyarsa, za ka zama mai arziki domin ka taimake shi. Gaskiya ita ce, ba za ka iya yin haka ba. Hakika dukanmu. Sa’ad da ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki za ka yi mamakin ganin yadda Jehobah ya kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika alkawuransa. Kuma yana faranta masa rai ya yi amfani da ikonsa ya amfani waɗanda suke ƙaunarsa. (2 Labarbaru 16:9) Waɗanda ba su san sunansa ba sun yi hasarar wannan ɓangaren na mutuntakar Jehobah.

A bayyane yake cewa ya kamata a yi amfani da sunan Jehobah a cikin Littafi Mai Tsarki. Sanin ma’anarsa da kuma yin amfani da shi wajen bauta suna taimakawa ƙwarai wajen kusantar Ubanmu na sama, Jehobah. *

^ sakin layi na 3 Domin ƙarin bayani game da sunan Allah, ma’anarsa, da kuma dalilin da ya sa ya kamata a yi amfani da shi wajen bauta, dubi mujallar nan The Divine Name That Will Endure Forever, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.