Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Yadda Annabcin Daniel ya Bayyana Zuwan Almasihu

Yadda Annabcin Daniel ya Bayyana Zuwan Almasihu

ANNABI Daniel ya rayu shekaru 500 kafin a haifi Yesu. Duk da haka, Jehobah ya nuna wa Daniel bayani da ya taimaka wajen nuna lokaci da za a shafa Yesu, ko kuma a naɗa shi ya zama Almasihu, ko kuma Kristi. An gaya wa Daniel: “Ka sani fa, ka fahimta kuma, tun daga loton fitowar doka a maida Urushalima, a gine ta kuma, har zuwan loton Masiya sarki, za a yi bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu.”—Daniel 9:25.

Domin mu fahimci lokacin da Almasihun zai zo, kana bukatar ka sani da farko lokacin da zai kai ga zuwan Almasihu. Annabcin ya ce, “daga loton fitowar doka a maida Urushalima.” Yaushe ne aka ba da wannan “doka”? In ji Marubucin Littafi Mai Tsarki Nehemiya, an ba da dokar a sake gina ganuwa a kewaye Urushalima “cikin shekara ta ashirin ta Artaxerxes sarki.” (Nehemiah 2:1, 5-8) ’Yan tarihi sun tabbatar da cewa shekara ta 474 K.Z., ita ce cikakkiyar shekara ta farko ta Artaxerxes a gadon sarauta. Saboda haka, shekararsa ta ashirin a sarauta ita ce shekara ta 455 K.Z. A yanzu mun fahimci farkon lokacin Annabcin Daniel na Almasihu, shekara ta 455 K.Z.

Daniel ya nuna tsawon lokacin da zai ɗauka kafin “Masiya sarki” ya zo. Annabcin ya ce “za a yi bakwai bakwai: cikin bakwai sattin da biyu”—gaba ɗaya sun zama bakwai 69. Yaya tsawon wannan lokaci yake? Yawancin fassarar Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa waɗannan ba bakwai na kwana bakwai ba ne, amma bakwai ne na shekaru. Wato, kowane bakwai yana nufin shekara bakwai. Yahudawa dā suna sane da wannan yanayin na bakwai na shekaru. Alal misali, suna kiyaye Asabarci na shekara bayan kowace shekara bakwai. (Fitowa 23:10, 11) Saboda haka, bakwai 69 na annabci shekaru 7 ne sau 69, ko kuma shekaru 483.

Yanzu abin da za mu yi shi ne mu lissafa. Idan muka ƙirga shekaru 483 daga shekara ta 455 K.Z., zai kai mu ga shekara ta 29 A.Z. Wannan shi ne daidai lokaci da Yesu ya yi baftisma ya zama Almasihu! * (Luka 3:1, 2, 21, 22) Wannan ba cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ba ne mai ban mamaki?

^ sakin layi na 2 Daga shekara ta 455 K.Z., zuwa shekara ta 1 K.Z., shekaru 454 ne. Daga shekara ta 1 K.Z., zuwa shekara ta 1 A.Z., shekara ɗaya ce (babu shekara ta sifili). Kuma daga shekara ta 1 A.Z., zuwa shekara ta 29, shekaru 28 ne. Idan muka haɗa waɗannan adadi uku wuri ɗaya za mu sami shekaru 483. An ‘datse’ Yesu a shekara ta 33 A.Z., a cikin bakwai na 70. (Daniel 9:24, 26) Dubi littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy! babi na 11, da kuma Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafuffuka na 899-901. Shaidun Jehobah ne suka wallafa su.