Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah

Jibin Maraice na Ubangiji—Farilla da Ke Daraja Allah

AN UMURCI Kiristoci su kiyaye Farilla ta Tuna Mutuwar Kristi. Wannan farillar kuma ana kiranta “jibin Ubangiji.” (1 Korinthiyawa 11:20) Wane muhimmanci yake da shi? Yaushe kuma ta yaya za a kiyaye farillar?

Yesu Kristi ya kafa wannan farillar a daren bikin Ƙetarewa na Yahuduwa a shekara ta 33 A.Z. Ana bikin Ƙetarewa ne sau ɗaya a shekara a ranar 14 ga watan Nisan a kalandar Yahudawa. Domin su ƙirga kwanan watan wataƙila Yahudawa suna jira ne har sai farkon damina lokacin da rana da dare tsawonsu ɗaya. Wannan ita ce ranar da take da kusan awoyi 12 na dare da kuma awoyi 12 na rana. Fitowan sabon wata na kusa da wannan ranar shi ne farkon watan Nisan. Ana bikin Ƙetarewa a rana ta 14 bayan faɗuwar rana.

Yesu ya yi bikin Ƙetarewa tare da manzanninsa, ya sallami Yahuda Iskariyoti, sai kuma ya kafa farilla ta Jibin Maraice na Ubangiji. Wannan farillar ta canji bikin Ƙetarewa na Yahudawa saboda haka ya kamata a yi ta sau ɗaya a shekara.

Linjilar Matta ya ce: “Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya, ya karya; ya ba almajiran, ya ce, Ku karɓa, ku ci; wannan jikina ne. Kuma ya ɗauki ƙoƙo, ya yi godiya, ya ba su kuma, ya ce, Dukanku ku sha daga cikinsa; gama wannan jinina ne na alkawari, wanda an zubar domin mutane dayawa zuwa gafarar zunubai.”—Matta 26:26-28.

Wasu sun gaskata cewa Yesu ya juya burodin ya zama namansa, giyar kuma ta zama jininsa. Amma, jikin Yesu a cike yake sa’ad da ya ba da burodin. Da gaske ne cewa manzannin sun ci namansa a zahiri kuma sun sha jininsa? Da wannan zai taka dokar Allah. (Farawa 9:3, 4; Leviticus 17:10) In ji Luka 22:20, Yesu ya ce: “Wannan ƙoƙon sabon alkawari ne cikin jinina, wanda an zubar dominku.” Ƙoƙon ya juya ne ya zama “ sabon alkawari” a zahiri? Hakan ba zai yiwu ba, tun da alkawari yarjejeniya ne ba abin da za a iya riƙewa da hannu ba ne.

Saboda haka, burodin da giyar alamu ne kawai. Burodin alamar jikin Kristi ne marar zunubi. Yesu ya yi amfani da raguwar burodi na bikin Ƙetarewa. An yi burodin ba tare da yisti ba. (Fitowa 12:8) A Littafi Mai Tsarki yisti alamar zunubi ne. Saboda haka, burodin alamar kamiltaccen jiki da Yesu ya ba da hadaya ne. Ba shi da zunubi.—Matta 16:11, 12; 1 Korinthiyawa 5:6, 7; 1 Bitrus 2:22; 1 Yohanna 2:1, 2.

Jar giya alama ce ta jinin Yesu. Wannan jinin ta kafa sabon alkawari. Yesu ya ce an zubar da jininsa domin “gafarar zunubai.” Saboda haka mutane suna iya zama masu tsabta a gaban Allah kuma za su iya shiga sabon alkawari da Jehobah. (Ibraniyawa 9:14; 10:16, 17) Wannan alkawari ya sa ya yiwu Kiristoci masu aminci 144,000 su tafi sama. A nan za su zama sarakuna da firistoci domin albarkar dukan ’yan adam.—Farawa 22:18; Irmiya 31:31-33; 1 Bitrus 2:9; Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 14:1-3.

Waye zai ci wannan alamu na tuna Mutuwar Yesu? Waɗanda kawai suke cikin sabon alkawarin ne—wato, waɗanda suke da begen zuwa sama—su ne kawai ya kamata su ci burodin kuma su sha giyar. Ruhun Allah yake tabbatar wa waɗannan cewa an zaɓe su su zama sarakuna a samaniya. (Romawa 8:16) Kuma suna cikin alkawarin Mulki da Yesu.—Luka 22:29.

Waɗanda suke da begen rayuwa har abada a Aljanna a duniya fa? Suna yin biyayya ga umurnin Yesu kuma suna halartar bikin Jibin Maraice na Ubangiji, suna zuwa ne domin su lura, ba don su ci ko su sha ba. Sau ɗaya a shekara bayan faɗuwar rana, a ranar 14 ga watan Nisan, Shaidun Jehobah suna kiyaye farilla ta Jibin Maraice na Ubangiji. Ko da yake dubbai kalilan ne kawai suke da’awar zuwa sama, wannan farilla tana da muhimmanci ga dukan Kiristoci. Lokaci ne na yin bimbini bisa ƙauna ta Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi.—Yohanna 3:16.