Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?

Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?

HALITTAR ruhu da ake kira Mika’ilu ba a ambace shi sau da yawa ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, dukan lokacin da aka yi maganarsa yana yin wani abu. A cikin Littafin Daniel, Mika’ilu yana yaƙan miyagun ruhohi; a cikin wasiƙar Yahuda, yana jayayya da Shaiɗan; a Ru’ya ta Yohanna kuma, yana yaƙi da Iblis da kuma aljanunsa. Ta wajen kāre sarautar Jehobah da kuma yaƙan abokan gaban Allah, Mika’ilu ya ci sunansa wanda yake nufin—“Waye kamar Allah?” Amma wanene Mika’ilu?

Wasu mutane suna da suna fiye da ɗaya. Alal misali, an san Yaƙub da Isra’ila, manzo Bitrus kuma, Siman. (Farawa 49:1, 2; Matta 10:2) Haka nan kuma, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Mika’ilu wani suna ne na Yesu Kristi, kafin ya rayu a duniya da kuma bayan ya rayu a duniya. Bari mu bincika wasu dalilai na Nassi da ya sa muka ce haka.

Babban Mala’ika. Kalmar Allah ta kira Mika’ilu “shugaban Mala’ika.” (Yahuda 9) Ka lura cewa an kira Mika’ilu shugaban mala’iku. Wannan ya nuna cewa mala’ikan guda ɗaya ne. Hakika, furcin nan “shugaban mala’ika” ya bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki a kaɗaici ne ba a jam’i ba. Bugu da ƙari, Yesu yana da alaƙa da ofishin shugaban mala’iku. Game da Ubangiji Yesu Kristi da aka ta da daga matattu, 1 Tassalunikawa 4:16 ta ce: “Ubangiji da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-ƙarfi, da muryar sarkin mala’iku.” Saboda haka an kwatanta muryar Yesu da ta sarkin mala’iku. Domin haka, wannan nassin yana nunawa ne cewa Yesu shi ne Mika’ilu shugaban mala’iku.

Shugaban Dakaru. Littafi Mai Tsarki ya ce “Mika’ilu da nasa mala’iku suna fita su yi gāba da dragon; . . . kuma ya yi gāba tare da nasa mala’iku.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7) Saboda haka, Mika’ilu shugaba ne na dakarun mala’iku masu aminci. Ru’ya ta Yohanna kuma ya kwatanta Yesu da Shugaban dakaru na mala’iku masu aminci. (Ru’ya ta Yohanna 19:14-16) Kuma manzo Bulus ya faɗa takamaimai cewa “Ubangiji Yesu” da “mala’iku na ikonsa.” (2 Tassalunikawa 1:7; Matta 16:27; 24:31; 1 Bitrus 3:22) Littafi Mai Tsarki ya yi maganar Mika’ilu da “mala’ikunsa” da kuma Yesu da “mala’ikunsa.” (Matta 13:41) Tun da babu inda Kalmar Allah ta nuna cewa da akwai dakaru biyu na mala’iku masu aminci a sama—ɗaya Mika’ilu yake ja-gora, ɗaya kuma Yesu—daidai ne a kammala da cewa Mika’ilu Yesu Kristi ne a ofishinsa na sama. *

^ sakin layi na 1 Da ƙarin bayani da ya nuna cewa Mika’ilu yana nufin Ɗan Allah a Littafi na 2, shafuffuka na 393-394, na Insight on the Scriptures, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.