Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 6

Yadda Za a Zabi Nishadi Mai Kyau

Yadda Za a Zabi Nishadi Mai Kyau

“A yi duka [abubuwa] domin a girmama Allah.”—1 KORINTIYAWA 10:31.

1, 2. Wane zaɓi ne muke bukatar mu yi game da nishaɗi?

A CE kana so ka sha mangwaro mai zaƙi amma sai ka lura cewa gefe ɗaya ya ruɓe. Me za ka yi? To, kana iya shanye dukan mangwaron, har da gefen da ya ruɓe; kana iya jefar da dukan mangwaron, har da gefen da ya ruɓe; ko kuma kana iya yanke gefen da ya ruɓe ka jefar don ka sha mangwaron. Wannene za ka zaɓa?

2 To, nishaɗi yana kama da wannan mangwaron. A wani lokaci kana so ka ɗan wartsake, amma sai ka fahimci cewa dukan hanyoyin nishaɗin da ake da su a yau ba su da kyau ga ɗabi’a, ruɓaɓɓu ne. Saboda haka, me za ka yi? Wasu ba su damu da abin da yake da kyau ba suna more dukan irin nishaɗi da wannan duniya take bayarwa. Wasu suna gudun dukan wani nishaɗi domin kada su ga abin da ba shi da kyau. Amma wasu suna mai da hankali su guji nishaɗi marar kyau amma a wani lokaci sukan more nishaɗin da yake da ɗan kyau. Wane zaɓi ne za ka yi domin ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah?

3. Menene za mu tattauna a yanzu?

3 Yawancinmu za mu zaɓi na ukun. Mun fahimci cewa muna bukatar wartsakewa amma muna son nishaɗinmu ya zama mai kyau. Saboda haka, muna bukatar mu tattauna nishaɗin da yake da kyau da marar kyau. Amma da farko, bari mu tattauna yadda irin nishaɗi da muka zaɓa zai shafi bautar mu ga Jehobah.

‘A YI DUKA ABUBUWA DOMIN A GIRMAMA ALLAH’

4. Ta yaya keɓe kanmu zai shafi nishaɗinmu?

4 Wani Mashaidi da ya tsufa, da ya yi baftisma a shekara ta 1946 ya ce: “Na tabbata cewa zan halarci dukan jawabin baftisma kuma in saurara da kyau kamar ni ne zan yi baftisma.” Me ya sa? Ya yi bayani, “Tuna keɓe kai da na yi ya kasance mataki ne mai muhimmanci wajen kasancewa da aminci.” Babu shakka za ka yarda da abin da ya ce. Tuna wa kanka cewa ka yi wa Jehobah alkawarin za ka yi amfani da rayuwarka ka bauta masa zai motsa ka ka jimre. (Karanta Mai-Wa’azi 5:4) Hakika, bimbini bisa keɓe kanka zai shafi ra’ayinka game da hidimar Kirista da kuma wasu ɓangarorin rayuwa, wannan ya haɗa da nishaɗi. Manzo Bulus ya nanata wannan gaskiyar sa’ad da ya rubuta wa Kiristocin zamaninsa: ‘Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.’—1 Korintiyawa 10:31.

5. Ta yaya Leviticus 22:18-20 suka taimake mu ga bi gargaɗin da ke Romawa 12:1?

5 Dukan abin da muke yi a rayuwa tana da dangantaka da bautar mu ga Jehobah. A wasiƙarsa zuwa ga Romawa, Bulus ya yi amfani da kalma mai ƙarfi don ya nanata wannan gaskiya ga ’yan’uwa masu bi. Ya aririce su: “Ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” (Romawa 12:1) Jikinka ya haɗa da tunaninka, zuciyarka, da kuma ƙarfinka na zahiri. Kana amfani da dukan wannan wajen bauta wa Allah. (Markus 12:30) Bulus ya yi maganar irin wannan hidima ta sadaukarwa cewa hadaya ce. Wannan furci ya ƙunshi gargaɗi. A Dokar Musa, Allah ba ya karɓan hadaya da take da aibi. (Leviticus 22:18-20) Haka kuma, idan hadayar ruhaniya ta Kirista tana da aibi a wata hanya, Allah ba zai karɓa ba. Ta yaya irin wannan zai faru?

6, 7. Ta yaya Kirista zai sa jikinsa ya kasance da aibi, kuma menene sakamakon haka?

6 Bulus ya gargaɗi Kiristoci da suke Roma: “Kada zunubi fa ya yi mulki cikin jikinku.” Bulus kuma ya gaya masu su kashe ‘ayyukan jiki.’ (Romawa 6:12-14; 8:13) Da farko a cikin wasiƙarsa, ya ba da misalin irin waɗannan ‘ayyukan jiki.’ Game da ’yan adam masu zunubi, mun karanta: ‘Bakinsu cike ya ke da zagi.’ ‘Ƙafafunsu masu garaje ne garin zubda jini.’ ‘Babu tsoron Allah a gaban idanunsu.’ (Romawa 3:13-18) Jikin Kirista zai kasance da aibi idan ya yi amfani da shi domin irin waɗannan ayyuka. Alal misali, idan da gangan ne Kirista yake kallon hotunan batsa ko kuma mugunta, yana ‘bada [idanunsa] ga zunubi’ kuma saboda haka ya kasance da aibi a dukan jikinsa. Dukan wata hadayar da ya bayar ta kasance marar tsarki ke nan kuma Allah ba zai karɓa ba. (Kubawar Shari’a 15:21; 1 Bitrus 1:14-16; 2 Bitrus 3:11) Lalle wannan sakamako ne mai tsanani don zaɓan nishaɗi marar kyau!

7 A bayyane yake cewa nishaɗin da Kirista ya zaɓa yana da sakamako mai tsanani. Babu shakka, za mu so mu zaɓi nishaɗi da zai kyautata ba wanda zai ɓata hadayarmu ga Allah ba. Bari yanzu mu tattauna yadda za mu san nishaɗi mai kyau da marar kyau.

“KU YI ƘYAMAR ABIN DA KE MUGU”

8, 9. (a) Za a iya raba nishaɗi zuwa kashi nawa ne? (b) Waɗanne irin nishaɗi ne muke ƙi, kuma me ya sa?

8 Hakika, za a iya raba nishaɗi gida biyu. Ɗaya ya ƙunshi nishaɗi da Kiristoci suke guje wa; ɗayan kuma ya ƙunshi nishaɗi da Kiristoci za su iya so ko kuma ba za su so ba. Bari mu fara da na farkon, nishaɗi da Kiristoci suke guje wa.

9 Kamar yadda aka gani a Babi na 1, wasu irin nishaɗi suna ɗaukaka abubuwa da aka hana a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ka yi tunanin Dandali a Intane, fim, ko shiri a talabijin ko kuma waƙa da suka ƙunshi ayyukan aljannu ko kuma hotunan batsa ko kuma waɗanda suke lalata ɗabi’a. Tun da irin waɗannan abubuwa suna nuna ayyuka da ke ƙeta mizanai ko kuma dokokin Littafi Mai Tsarki cewa suna da kyau, ya kamata Kiristoci na gaskiya su guje su. (Ayukan Manzanni 15:28, 29; 1 Korintiyawa 6:9, 10; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Ta wajen ƙin irin wannan nishaɗi marar kyau, kana nuna cewa da gaske kana “ƙyamar abin da ke mugu” kuma ka “rabu da mugunta.” Ta haka za ka kasance da “bangaskiya marar-riya.”—Romawa 12:9; Zabura 34:14; 1 Timothawus 1:5.

10. Wane irin tunani ne game da nishaɗi da yake da haɗari kuma me ya sa?

10 Amma wasu suna gani kamar yin nishaɗi da ke nuna lalata ba shi da wani ila. Suna tunani, ‘Zan iya kallonsa a fim, ko kuma a talabijin, amma ba zan taɓa yin haka da kaina ba.’ Irin wannan tunanin na yaudara ne kuma yana da haɗari. (Karanta Irmiya 17:9) Idan muna farin cikin kallon abin da Jehobah ya hana, muna “ƙyamar abin da ke mugu” kuwa da gaske? Idan muna kallon irin wannan mugun hali a kai a kai zai shafi halinmu. (Zabura 119:70; 1 Timothawus 4:1, 2) Irin wannan halin zai shafi abin da muke yi ko kuma yadda muke ɗaukan zunubin wasu.

11. Ta yaya Galatiyawa 6:7 ta kasance gaskiya a batun nishaɗi?

11 Wannan ya faru da gaske. Wasu Kiristoci sun yi lalata domin abin da suke yawan kallo ya rinjaye su. Ta abin da ya faru musu sun koya cewa “abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.” (Galatiyawa 6:7) Amma ana iya guje wa irin wannan sakamako marar kyau. Idan ka mai da hankali ka shuka abu mai kyau a rayuwarka, da farin ciki za ka girbe abu mai kyau.—Dubi akwatin nan “ Wane Irin Nishaɗi Ne Zan Zaɓa?” da ke shafi na 67.

SHAWAWARI BISA MIZANAN LITTAFI MAI TSARKI

12. Ta yaya Galatiyawa 6:5 ya shafi nishaɗi, kuma wane ja-gora muke da shi wajen yanke shawara?

12 Bari yanzu mu tattauna ɓangare na biyu, wato, nishaɗin da ke nuna abubuwa da ba a haramta ko kuma halalta su ba kai tsaye a cikin Kalmar Allah. Sa’ad da ake zaɓa daga wannan nishaɗi, kowane Kirista yana bukatar ya yanke shawarar kansa game da abin da yake da kyau a gare shi. (Karanta Galatiyawa 6:5) Duk da haka, sa’ad da muka fuskanci wannan zaɓi, muna da makama. Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi mizanai ko kuma gaskiya, da za su taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake tunani. Ta wajen mai da wa waɗannan mizanai hankali, za mu iya fahimtar “nufin Ubangiji” game da dukan abu, har da irin nishaɗi da za mu zaɓa.—Afisawa 5:17.

13. Menene zai motsa mu mu guji nishaɗi da zai baƙanta wa Jehobah rai?

13 Hakika dukan Kiristoci ba daidai suke ba wajen fahimi. (Filibbiyawa 1:9) Ƙari ga haka, Kiristoci sun fahimci cewa ra’ayi ya bambanta wajen nishaɗi. Saboda haka, kada a yi tsammanin cewa dukan Kiristoci za su zaɓi irin nishaɗi ɗaya. Har a wannan ma, idan muka ƙyale mizanan Allah su rinjayi tunaninmu da kuma zuciyarmu, hakan zai sa mu ƙudurta guje wa dukan wani nishaɗi da zai baƙanta wa Jehobah rai.—Zabura 119:11, 129; 1 Bitrus 2:16.

14. (a) Wane abu za mu yi la’akari da shi sa’ad da muke zaɓan nishaɗi? (b) Ta yaya za mu saka al’amuran Mulki farko a rayuwarmu?

14 Sa’ad da muke zaɓan nishaɗi, da akwai wani abu mai muhimmanci da za mu yi la’akari da shi: wato, lokacinmu. Irin abin da nishaɗinmu ya ƙunsa zai nuna irin abin da muke so, lokaci da muke ɓata wa a kai zai nuna abin da ya fi muhimmanci a gare mu. Hakika, ga Kiristoci, abubuwa na ruhaniya sun fi muhimmanci. (Karanta Matta 6:33) To, menene za ka yi domin ka tabbata cewa al’amuran Mulki sune farko a rayuwarka? Manzo Bulus ya ce: “Ku duba fa a hankali yadda ku ke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi.” (Afisawa 5:15, 16) Hakika, yin nishaɗi a lokacin da ya kamata zai taimaka wajen keɓe lokacin da ake bukata domin “mafifitan al’amura” wato, ayyukan da suke ƙara ƙarfafa ruhaniyarka.—Filibbiyawa 1:10.

15. Me ya sa yake da kyau mu kula da lafiyarmu sa’ad da muke zaɓan nishaɗi?

15 Yana da kyau mu kula da lafiyarmu sa’ad da muke zaɓan nishaɗi. Menene wannan yake nufi? Ka sake yin la’akari da misalin mangwaro da aka bayar. Domin kada ka ci inda ya ruɓe, za ka yanka wurin da ya ruɓa da kuma wuraren da suke kusa da shi. Hakazalika, za ka mai da hankali sa’ad da kake zaɓan nishaɗi. Kirista mai hikima ba zai guji nishaɗi kawai da ya ƙunshi abubuwa da suka ƙeta mizanan Littafi Mai Tsarki ba amma zai guji waɗanda kamar sun ƙunshi abubuwa da suke da la’ani a ruhaniya. (Misalai 4:25-27) Manne wa Kalmar Allah zai taimake ka ka yi haka.

“IYAKAR ABIN DA KE MAI-TSABTA”

Bin mizanan Allah wajen zaɓan nishaɗi yana kāre mu daga haɗari na ruhaniya

16. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna da ra’ayin Jehobah game da ɗabi’a? (b) Ta yaya amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki zai zama hanyar rayuwarmu?

16 Idan ya zo ga zaɓan nishaɗi, Kiristoci na gaskiya da farko suna yin la’akari da ra’ayin Jehobah. Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda Jehobah yake ji da kuma mizaninsa. Alal misali, Sarki Sulemanu ya faɗi abubuwa da yawa da Jehobah ba ya so, kamar su “harshe mai-ƙarya, hannuwa masu-zubda jinin mara-laifi: Zuciya mai-tsiro da miyagun tunani, ƙafafu masu-saurin gudu gari yin ƙeta.” (Misalai 6:16-19) Ta yaya ra’ayin Jehobah zai shafi naka? “Ya ku masu-ƙaunar Ubangiji,” in ji mai Zabura, “sai ku ƙi mugunta.” (Zabura 97:10) Irin zaɓinka na nishaɗi ya kamata ya nuna cewa da gaske kana ƙin mugunta. (Galatiyawa 5:19-21) Ka kuma tuna cewa, abin da kake yi a ɓoye, fiye da wanda kake yi a cikin jama’a, ya nuna ainihi irin mutumin da kake. (Zabura 11:4; 16:8) Saboda haka, idan kana da muradin ka nuna a dukan ɓangarorin rayuwarka yadda Jehobah yake ji game da abubuwa, za ka zaɓi abubuwa da suka jitu da mizanan Littafi Mai Tsarki a koyaushe. Yin haka zai zama hanyar rayuwarka.—2 Korintiyawa 3:18.

17. Kafin ka zaɓi nishaɗi, wace tambaya za ka yi?

17 Menene kuma za ka iya yi domin ka tabbata cewa dukan ayyukanka sun jitu da yadda Jehobah yake tunani sa’ad da kake zaɓan nishaɗi? Ka yi tunani a kan wannan tambayar, ‘Ta yaya wannan zai shafe ni da kuma dangantakata da Allah?’ Alal misali, kafin ka yanke shawarar ko za ka kalli wani fim, ka tambayi kanka, ‘Ta yaya abin da wannan fim ɗin ya ƙunsa zai shafi lamiri na?’ Bari mu ga mizani da ya shafi wannan batun.

18, 19. (a) Ta yaya mizani da ke cikin Filibbiyawa 4:8 zai taimake mu mu sani ko nishaɗinmu mai kyau ne? (b) Waɗanne mizanai ne kuma zai iya taimakonka ka zaɓi nishaɗi mai kyau? (Dubi hasiya.)

18 Wani mizani mai muhimmanci yana cikin Filibbiyawa 4:8, wanda ya ce: ‘Iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan.’ Hakika, ba nishaɗi Bulus yake magana a kai ba, amma yin bimbini, da ya kamata ya kasance a abubuwan da za su faranta wa Allah rai. (Zabura 19:14) Duk da haka, ana iya amfani da kalaman Bulus ga nishaɗi. Ta yaya?

19 Ka tambayi kanka, ‘Shin irin fim da nake zaɓa, wasannin bidiyo, waƙa, ko kuma wasu irin nishaɗi suna cika zuciyata ne da “iyakar abin da ke mai-tsabta”?’ Alal misali, bayan ka kalli fim, wane abu kake tunaninsa? Idan abubuwa ne masu kyau masu wartsakewa, to ka san cewa nishaɗinka mai kyau ne. Amma kuma, idan fim ɗin da ka kalla ya sa kana tunanin abin da ba shi da kyau, to ka sani cewa nishaɗinka ba shi da kyau, yana iya kasancewa mai haɗari ma. (Matta 12:33; Markus 7:20-23) Me ya sa? Domin tunanin abubuwa marar kyau za su ta da maka hankali, su sa taɓo ga lamirinka da Littafi Mai Tsarki ya koyar, kuma zai lalata dangantakarka da Allah. (Afisawa 5:5; 1 Timothawus 1:5, 19) Tun da irin wannan nishaɗi yana shafan mutumtakarmu a hanya marar kyau, ka ƙuduri aniyar guje masa. * (Romawa 12:2) Ka zama kamar mai zabura da ya yi wa Jehobah addu’a: “Ka kawasda idanuna ga barin duban abin banza.”—Zabura 119:37.

BIƊI ABIN DA ZAI AMFANI WANI

20, 21. Ta yaya 1 Korintiyawa 10:23, 24 suka shafi zaɓen nishaɗi mai kyau?

20 Bulus ya faɗi wani mizani mai muhimmanci da ake bukata a yi la’akari da shi sa’ad da ake nema a yanke shawara game da wani abu. Ya ce: “Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ya dace ba. Abu duka halal ne; amma ba dukan abu ne ya ke gini ba. Kada kowa shi biɗa ma kansa, amma abin da za ya amfana maƙwabcinsa.” (1 Korintiyawa 10:23, 24) Ta yaya wannan mizani ya shafi nishaɗi mai kyau? Kana bukatar ka tambayi kanka, ‘Ta yaya nishaɗi da na zaɓa zai shafi wasu?’

21 Lamirinka zai iya ƙyale ka ka more wani irin nishaɗi da a wurin ka ba shi da ‘laifi.’ Amma, idan ka lura cewa lamirin wasu masu bi bai yarda da shi ba, za ka zaɓi ka bari. Me ya sa? Domin ba ka so ‘ka yi wa ’yan’uwanka zunubi’ ko kuma ‘ka yi wa Kristi zunubi,’ kamar yadda Bulus ya ce, ta wajen sa ya kasance da wuya ’yan’uwa masu bi su kasance da aminci ga Allah. Ka tuna da gargaɗin nan: “Kada ku bada sanadin tuntuɓe.” (1 Korintiyawa 8:12; 10:32) Kiristoci na gaskiya a yau suna bin gargaɗin Bulus ta wajen guje wa nishaɗi da ba ‘laifi’ ba ne amma ba mai ‘ginawa ba.’—Romawa 14:1; 15:1.

22. Me ya sa Kiristoci ba su damu da bambancin ra’ayi game da wasu batutuwa ba?

22 Da akwai kuma wani ɓangare na wannan batun biɗan abin da zai amfani wasu. Kada Kirista da lamirinsa ya hana shi yin wani abu ya nace cewa sai dukan waɗanda suke cikin ikilisiya sun bi ra’ayinsa game da irin nishaɗi da yake gani ya dace. Idan ya yi haka, zai kasance kamar wani direba ne a kan babbar hanya da ya nace cewa dukan direbobi da suke bin wannan hanyar dole ne su yi gudu daidai da yadda shi yake so. Irin wannan ra’ayin bai dace ba. Domin ƙauna ta Kirista, wani da yake da lamiri mai ka’ida yana bukata ya daraja wasu ’yan’uwa masu bi waɗanda ra’ayinsu game da nishaɗi ya bambanta da na shi amma kuma suna cikin iyakan mizanan Littafi Mai Tsarki. A wannan hanyar zai sa sanin ya kamata da yake da shi “ta sanu ga dukan mutane.”—Filibbiyawa 4:5; Mai-Wa’azi 7:16.

23. Ta yaya za ka tabbata cewa ka zaɓi nishaɗi mai kyau?

23 A taƙaice, ta yaya za ka tabbata cewa ka zaɓi nishaɗin da ya dace? Ka ƙi dukan wani nishaɗi da yake nuna ayyukan lalata da Allah ya hana a cikin Kalmarsa. Ka bi mizanan Littafi Mai Tsarki da za a iya amfani da su ga nishaɗi dabam dabam da ba a ambata cikin Littafi Mai Tsarki ba. Ka guji nishaɗi da zai yi wa lamirinka rauni, kuma da son rai ka ƙyale ire-iren nishaɗi da zai raunana lamirin wasu, musamman ma na ’yan’uwa masu bi. Bari shawararka ta ɗaukaka Allah kuma ta tsare ka da iyalinka cikin ƙaunar Allah.

^ sakin layi na 19 Za a sami wasu ƙarin mizanai da suka shafi nishaɗi a Misalai 3:31; 13:20; Afisawa 5:3, 4; da kuma Kolossiyawa 3:5, 8, 20.