Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 14

Ka Kasance Mai Gaskiya Cikin Dukan Abu

Ka Kasance Mai Gaskiya Cikin Dukan Abu

“Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”—IBRANIYAWA 13:18.

1, 2. Me ya sa Jehobah yake farin ciki sa’ad da ya ga ƙoƙarce-ƙoƙarcen da muke yi don kasancewa masu gaskiya? Ka kwatanta.

WATA uwa da yaronta ɗan ƙarami sun fita daga wani shago tare. Nan da nan, sai yaron ya tsaya, fuskarsa cike da tsoro. Yana riƙe da ɗan ƙaramin abin wasa na yara da ya ɗauka a cikin shagon. Ya mance bai mai da shi ba, kuma bai tambayi mamarsa ba ko za ta saya. Cike da baƙin ciki, ya nemi ta taimake shi. Ta kwantar da hankalinsa kuma ta mai da shi cikin shagon don ya mai da abin da ya ɗauka kuma ya ba su haƙuri. Yayin da yake yin hakan, zuciyar mamar ta cika da farin ciki da alfahari. Me ya sa?

2 Iyaye suna farin ciki sosai idan suka ga cewa yaransu suna koyan muhimmancin kasancewa masu gaskiya. Haka ma Ubanmu na samaniya, “Allah na gaskiya.” (Zabura 31:5) Sa’ad da muke girma a ruhaniya, yana farin cikin ganin ƙoƙarin da muke yi na kasancewa masu gaskiya. Domin muna son mu faranta masa rai kuma mu tsare kanmu a cikin ƙaunarsa, muna yin abin da manzo Bulus ya faɗa a kalamansa: “Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibraniyawa 13:18) Bari mu mai da hankali a kan hanyoyi huɗu na rayuwa waɗanda a wasu lokatai yana iya yi mana wuya mu kasance masu gaskiya. Bayan haka, za mu tattauna wasu albarka da ake samu a sakamakon hakan.

MU GAYA WA KANMU GASKIYA

3-5. (a) Ta yaya ne Kalmar Allah ta gargaɗe mu game da haɗarurrukan ruɗin kai? (b) Menene zai taimaka mana mu gaya wa kanmu gaskiya?

3 Ƙalubale na farko shi ne koyan yadda za mu gaya wa kanmu gaskiya. Yana da sauƙi mu mutane ajizai mu ruɗi kanmu. Alal misali, Yesu ya gaya wa Kiristocin da ke Lawudikiya cewa sun ruɗi kansu ta wajen yin tunanin cewa suna da arziki, amma gaskiyar ita ce su ‘matalauta ne, makafi, tsiraru,’ suna cikin yanayi mai ban tausayi. (Ru’ya ta Yohanna 3:17) Ruɗin kansu da suke yi ne ya sa su cikin mugun haɗari.

4 Kana iya tuna gargaɗin da manzo Yaƙub ya yi: “Idan kowane mutum yana aza kansa mai-addini ne, shi kuwa ba ya kame harshensa ba amma yana yaudara zuciyatasa, addinin wannan banza ne.” (Yaƙub 1:26) Idan mun yi amfani da harshenmu a hanyar da bai dace ba, ba za mu bauta wa Jehobah yadda yake so ba. Bautarmu ga Jehobah za ta zama na banza, marar amfani. Menene zai taimaka mana mu guje wa irin wannan mugun tafarkin?

5 A cikin waɗannan ayoyin, Yaƙub ya kwatanta gaskiyar kalmar Allah da madubi. Ya shawarce mu mu lizima cikin kamiltacciyar dokar Allah kuma mu yi gyare-gyaren da ya kamata. (Karanta Yaƙub 1:23-25) Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu gaya wa kanmu gaskiya kuma mu ga abin da muke bukatar mu yi don mu ƙara kyautata rayuwarmu sosai. (Makoki 3:40; Haggai 1:5) Muna kuma iya yin addu’a ga Jehobah kuma mu roƙe shi ya bincika mu, ya taimaka mana mu ga kasawarmu kuma mu yi gyara. (Zabura 139:23, 24) Rashin gaskiya kasawa ce da ke tasowa cikin dabara, kuma muna bukatar mu ɗauke ta yadda Ubanmu na samaniya ya ɗauke ta. Misalai 3:32 ta ce: “Mashiririci abin ƙyama ne ga Ubangiji: Amma asirinsa yana tare da masu-adalci.” Jehobah yana iya taimaka mana mu kasance da irin ra’ayinsa kuma mu ɗauki kanmu yadda ya ɗauke mu. Ka tuna abin da Bulus ya ce: ‘Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.’ Ko da yake mu ba kamiltattu ba ne ba a yanzu, muna da cikakken muradin son kasancewa masu gaskiya a kowane lokaci.

FAƊIN GASKIYA A CIKIN IYALI

Kasancewa masu gaskiya yana taimaka mana mu guji halin da za mu so mu ɓoye

6. Me ya sa ya kamata abokan aure su gaya wa juna gaskiya, kuma waɗanne haɗarurruka ne suke bukatar su guje wa?

6 Ya kamata gaskiya ta yi fice a cikin iyalin Kirista. Saboda haka, ya kamata mata da miji su riƙa gaya wa juna gaskiya. A cikin auren Kirista, ba a amince da mugayen ayyuka marar tsabta kamar su yin soyayya da wani ko wata da ba aboki ko abokiyar aure ba, yin dangantaka a ɓoye ta hanyar Intane, ko kuwa yin amfani da hotunan batsa ko ta wace hanya. Wasu Kiristoci ma’aurata sun yi irin wannan mugun zunubin kuma sun ɓoye shi ga miji ko matarsu. Yin hakan rashin gaskiya ne. Ka lura da kalaman Sarki Dauda mai aminci: “Ban tara zama da mutanen banza ba; ba kuwa zan shiga tare da masu-makirci ba.” (Zabura 26:4) Idan kai ma’auraci ne, kada ka taɓa yin abin da zai sa ka ɓoye ainihin halinka ga abokiyar aurenka!

7, 8. Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki ne za su iya taimaka wa yara su koyi muhimmancin gaskiya?

7 Sa’ad da iyaye suke koya wa yaransu muhimmancin faɗin gaskiya, zai dace su yi amfani da misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Akwai labarin Achan, wanda ya yi sata kuma ya nemi ya ɓoye satar da ya yi; da na Gehazi, wanda ya yi ƙarya don ya sami abin duniya; da Yahuda, wanda ya yi sata kuma ya yi mugun ƙarya don ya yi wa Yesu illa.—Joshua 6:17-19; 7:11-25; 2 Sarakuna 5:14-16, 20-27; Matta 26:14, 15; Yohanna 12:6.

8 Idan ya zo ga misalai masu kyau, akwai labarai irin na Yakubu, wanda ya umurci yaransa su mai da kuɗaɗen da suka gani a cikin jakunkunarsu domin yana ganin cewa an yi kuskure ne aka saka su ciki; ga kuma Jephthah da ɗiyarsa, wadda ta amince da alkawarin da babanta ya ɗauka kuma ta yi sadaukarwa; ga kuma misalin Yesu, wanda ya gabatar da kansa babu tsoro a gaban mugun taro don ya cika annabci kuma ya kāre abokansa. (Farawa 43:12; Alƙalawa 11:30-40; Yohanna 18:3-11) Waɗannan ’yan misalan za su iya taimaka wa iyaye su ga cewa, akwai bayanai masu tamani a cikin Kalmar Allah da za su iya taimaka musu su koya wa yaransu su ƙaunaci gaskiya kuma su ɗauke ta da tamani.

9. Menene iyaye za su guje wa idan suna son su kafa wa yaransu misali na faɗin gaskiya, kuma me ya sa irin wannan misalin yake da muhimmanci?

9 Irin waɗannan koyarwar sun ɗora wa iyaye hakki mai muhimmanci. Manzo Bulus ya yi wannan tambayar: “Kai fa mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba? kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata?” (Romawa 2:21) Wasu iyaye suna rikita yaransu, su ce ku faɗi gaskiya su kuma iyayen ba sa faɗin gaskiya. Suna iya ba da hujjar yin sata da kuma yin ƙarya ta wajen cewa “Ai dama suna son mutane su ɗauki waɗannan abubuwan ne” ko kuwa “Wannan ƙaramar ƙarya ce.” Sata, sata ce, ko menene ƙanƙantar abin da aka sata, ƙarya, ƙarya ce, ko da menene aka ƙanƙantar abin da aka faɗa. * (Karanta Luka 16:10) Yara suna gane munafunci da wuri kuma hakan yana iya yi musu lahani sosai. (Afisawa 6:4) Amma, sa’ad da suka koyi faɗin gaskiya daga misalan iyayensu, za su iya girma su ɗaukaka Jehobah a wannan duniyar ta rashin gaskiya.—Misalai 22:6.

FAƊIN GASKIYA A CIKIN IKILISIYA

10. Game da tattaunawa da juna yadda ya kamata a tsakanin ’yan’uwa masu bi, waɗanne gargaɗi ne ya kamata mu riƙa tunawa?

10 Yin tarayya da ’yan’uwanmu Kiristoci yana ba mu dama mai yawa na kasancewa masu gaskiya. Kamar yadda muka koya a Babi na 12, muna bukatar mu mai da hankali sosai ga furcinmu, musamman a tsakanin ’yan’uwanmu na ruhaniya maza da mata. Tattaunawa ta yau da kullum tana iya komawa muguwar gulma, ko tsegumi! Idan muka maimaita wani labarin da bai da tushe, muna taimakawa ne wajen yaɗa ƙarya, saboda haka, ya kamata mu kula da abubuwan da ke fita daga bakinmu. (Misalai 10:19) A wani ɓangaren kuma, muna iya sanin cewa wani abu gaskiya ne, amma hakan ba ya nufin cewa sai mun faɗe shi. Alal misali, wataƙila batun bai shafe mu ba, ko kuwa ba zai dace mu tattauna game da shi ba. (1 Tassalunikawa 4:11) Wasu sukan nuna rashin ɗa’a kuma su ce gaskiya ce, amma ya kamata kalamanmu a kowane lokaci su zama masu daɗin ji kuma masu kyau.—Karanta Kolossiyawa 4:6.

11, 12. (a) A waɗanne hanyoyi ne wasu da suka yi mugun zunubi suke daɗa matsalarsu? (b) Waɗanne ƙarairayi ne Shaiɗan yake ɗaukakawa game da mugayen zunubai, kuma ta yaya za mu iya tsayayya da su? (c) Ta yaya za mu iya nuna cewa mu masu gaskiya ne ga ƙungiyar Jehobah?

11 Yana da muhimmanci sosai mu kasance masu gaya wa waɗanda suke shugabanci a cikin ikilisiya gaskiya. Wasu da suka yi mugun zunubi sukan daɗa matsalar ta wajen ɓoye zunubinsu da kuma yi wa dattawan ikilisiya ƙarya idan aka tambaye su game da batun. Irin su suna yin zunubi ne a ɓoye, yayin da suke nunawa a fili cewa suna bauta wa Jehobah amma tafarkin mugun zunubi ne suke bi. A sakamakon haka, irin wannan tafarkin yana mai da rayuwar mutumin gabaki ɗaya ta zama ta ƙarya. (Zabura 12:2) Wasu suna gaya wa dattawa kaɗan daga cikin gaskiyar kuma su ɓoye muhimman bayanan. (Ayukan Manzanni 5:1-11) Irin wannan rashin gaskiyar ta samo asali ne daga gaskata ƙarairayin da Shaiɗan yake ɗaukakawa.—Duba akwatin nan “ Ƙarairayin Shaiɗan Game da Mugayen Zunubai,” a shafi na 164-165.

12 Yana kuma da muhimmanci mu gaya wa ƙungiyar Jehobah gaskiya sa’ad da muke amsa tambayoyi a rubuce. Alal misali, sa’ad da muke ba da rahoton ayyukan da muka yi a hidima, mu mai da hankali kada mu rubuta abubuwan da ba gaskiya ba ne. Hakazalika, sa’ad da muke cika fam na gatan hidima, kada mu rubuta ƙarya game da yanayin lafiyarmu ko kuwa duk wani abu game da kanmu.—Karanta Misalai 6:16-19.

13. Ta yaya za mu iya kasancewa masu gaskiya a kasuwancin da muke yi da mai bi?

13 Faɗin gaskiya ga ’yan’uwanmu masu bi ya shafi batutuwan kasuwanci. A wasu lokatai, Kiristoci maza da mata suna iya yin kasuwanci tare. Suna bukatar su keɓe waɗannan batutuwan daga bautar da suke yi tare a Majami’ar Mulki ko kuwa a hidima. Dangantaka ta kasuwanci tana iya kasancewa ta shugaban aiki da ma’aikaci. Idan muka ɗauki ’yan’uwanmu maza ko mata aiki, muna bukatar mu yi sha’ani cikin gaskiya, mu biya su ainihin kuɗin da muka yi yarjejeniya da su a lokacin da ya kamata, da kuma abubuwan da doka ta ce a ba su. (1 Timothawus 5:18; Yaƙub 5:1-4) Hakazalika, idan ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ɗauke mu aiki, muna bukatar mu yi aikin kuɗin da ake biyanmu. (2 Tassalunikawa 3:10) Ba za mu sa rai cewa za a fifita mu fiye da wasu domin dangantakarmu ta ruhaniya ba, kamar dai dole ne shugaban aikinmu ya ba mu hutu, ko kuwa wasu abubuwa masu kyau da ba za a ba sauran ma’aikatan ba.—Afisawa 6:5-8.

14. Sa’ad da Kiristoci suka haɗa hannu a kasuwanci, wane mataki ya kamata su ɗauka, me ya sa?

14 Idan kasuwancin da muke yi na haɗa hannu ne da ke tattare da haɗari, wataƙila mun saka kuɗi ko kuma mun ranci kuɗi fa? Littafi Mai Tsarki ya ba mu mizani mai amfani: Ku rubuta komi da komi! Alal misali, sa’ad da Irmiya ya sayi fegin ƙasa, ya sa an rubuta takardu biyu, kuma shaidu sun sa hannu, an kuma adana takardun sosai don nan gaba. (Irmiya 32:9-12; kuma ka duba Farawa 23:16-20.) Sa’ad da ake kasuwanci da ’yan’uwa masu bi, rubuta dukan bayanan da kuma saka hannu tare da shaidu ba ya nufin rashin yarda. Maimakon haka, hakan yana kawar da rashin fahimta, da na sani, da kuma rigimar da za ta iya jawo rabuwa. Dukan Kiristocin da suke kasuwanci tare su tuna cewa, babu kasuwancin da ya cancanci saka haɗin kai da salamar ikilisiya cikin haɗari. *1 Korintiyawa 6:1-8.

FAƊIN GASKIYA A DUNIYA

15. Yaya Jehobah yake ji game da rashin gaskiya a kasuwanci, kuma menene Kiristoci za su yi game da irin wannan halin?

15 Ba a cikin ikilisiya ba ce kawai Kirista zai kasance mai faɗin gaskiya ba. Bulus ya ce: ‘Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.’ (Ibraniyawa 13:18) Sa’ad da muke kasuwanci da mutanen duniya, Mahaliccinmu yana son mu kasance masu gaskiya. A cikin littafin Misalai kaɗai, an ambata muhimmancin yin amfani da ma’auni na gaskiya sau huɗu. (Misalai 11:1; 16:11; 20:10, 23) A zamanin dā, ana yawan amfani da ma’auni a kasuwa don a auna nauyin kayan da aka saya da kuma kuɗin da aka biya. ’Yan kasuwa macuta suna amfani da ma’auni iri biyu waɗanda ba daidai ba ne ba don su ruɗi kuma su cuci masu sayayya a hannunsu. * Jehobah ya ƙi jinin irin waɗannan halayen! Idan muna son mu tsare kanmu a cikin ƙaunarsa, dole ne mu guje wa dukan wani irin rashin gaskiya a kasuwanci.

16, 17. Waɗanne ire-iren rashin gaskiya ne suka zama ruwan dare a duniya a yau, kuma menene Kiristoci na gaskiya suka ƙudurta za su yi?

16 Domin Shaiɗan ne ke mulkin wannan duniyar, ba ma mamakin ganin rashin gaskiya a ko’ina. A kullum muna fuskantar jarrabawa ta nuna rashin gaskiya. Sa’ad da mutane suka rubuta takardar neman aiki, suna yawan yin ƙarya da ƙara gishiri, sukan rubuta sakamakon da suka ƙera da kansu da kuma fahimin da ba su da shi. Sa’ad da mutane suke cika fam na shiga da fita ƙasa, haraji, inshora, da makamancin haka, sukan rubuta amsoshin ƙarya don su sami abin da suke so. Yawancin ɗalibai suna satar amsa a ranar jarabawa, ko kuwa sa’ad da suke rubuta labarai da rahotanni wa makaranta, suna iya zuwa cikin Intane su rubuta abin da suka gani, kuma su gabatar da aikin da wani ya yi a matsayin na su. Sa’ad da mutane suka yi sha’ani da shugabanni masu rashawa, a yawancin lokaci sukan ba da cin hanci don su sami abin da suke so. Wannan ba abin mamaki ba ne a gare mu a duniyar da yawancin ‘mutane suke son kansu, son kuɗi, . . . marasa-son nagarta.’—2 Timothawus 3:1-5.

17 Kiristoci na gaskiya sun ƙudurta cewa ba za su saka hannu a irin waɗannan ayyukan ba. Abin da ke sa faɗin gaskiya ya zama ƙalubale a wasu lokatai shi ne, waɗanda suke saka hannu a irin waɗannan hanyoyin na rashin gaskiya suna yin nasara kuma suna samun ci gaba a wannan duniyar. (Zabura 73:1-8) Su kuwa Kiristoci suna iya shan wahala na tattalin arziki domin suna son su kasance masu gaskiya ‘cikin dukan abu.’ Wannan sadaukarwar tana da amfani kuwa? Ƙwarai da gaske! Me ya sa? Waɗanne albarka ne ake samu daga kasancewa mai gaskiya?

ALBARKAR KASANCEWA MAI GASKIYA

18. Me ya sa yin suna wajen faɗin gaskiya yake da tamani sosai?

18 Abubuwa kaɗan ne kawai a rayuwa suke da tamani fiye da yin suna wajen faɗin gaskiya. (Duba akwatin nan “ Ina Faɗin Gaskiya Kuwa?” a shafi na 167.) Wani abu da ya kamata ka sani shi ne, kowanne mutum yana iya samun irin wannan sunan! Hakan bai dangana ba a kan iyawarka, dukiyarka, kamaninka, inda aka haife ka, ko kuma duk wani abin da ya fi ƙarfinka. Duk da haka, yawancin mutane sun kasa yin suna mai kyau. Masu suna mai kyau suna da wuyan samu. (Mikah 7:2) Wasu suna iya yi maka dariya domin kana faɗin gaskiya, amma wasu za su nuna godiya domin kai mai gaskiya ne kuma za su amince da kai su kuma daraja ka. Yawancin Shaidun Jehobah sun ga cewa gaskiyarsu ta taimaka musu wajen samun kuɗi. Sun riƙe aikinsu yayin da aka kori ma’aikata marar gaskiya, ko kuwa sun sami aiki a wuraren da ake mugun bukatar ma’aikata masu gaskiya.

19. Ta yaya ne faɗin gaskiya zai shafi lamirinmu da kuma dangantakarmu da Jehobah?

19 Ko da ka shaida hakan ko a’a, za ka ga cewa faɗin gaskiya yana kawo albarka mai girma. Za ka kasance da lamiri mai tsabta. Bulus ya rubuta: “Mun kawarda shakka muna da kyakkyawan lamiri.” (Ibraniyawa 13:18) Bugu da ƙari, Ubanmu na samaniya mai ƙauna yana kallon ka, kuma yana ƙaunar mutane masu gaskiya. (Karanta Zabura 15:1, 2; Misalai 22:1) Hakika, kasancewa mai faɗin gaskiya zai taimaka maka ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah, kuma babu wani ladan da muke nema da ya fi hakan. Bari yanzu mu tattauna wani batu da ya shafi wannan: ra’ayin Jehobah game da aiki.

^ sakin layi na 9 A cikin ikilisiya, yin mugun ƙarya don a ɓata wasu, zai iya sa dattawa su ɗauki mataki na shari’a.

^ sakin layi na 14 Game da matakin da ya kamata a ɗauka idan aka sami matsala a kasuwanci, ka duba Rataye, a shafi na 222-223.

^ sakin layi na 15 Suna amfani da ma’auni guda don yin sayayya kuma suna amfani da ɗayan don sayarwa, da haka su cuci mutane. Suna kuma iya yin amfani da ma’aunin da hannunsa ɗaya ya fi ɗayan tsawo ko nauyi don su cuci masu saye a hannunsu da kuma waɗanda suke sayar wa kaya.