Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

RATAYE

Yadda Za a Bi da Wanda Aka Yi wa Yankan Zumunci

Yadda Za a Bi da Wanda Aka Yi wa Yankan Zumunci

Abubuwa kalilan ne za su yi mana ciwo fiye da zafin da za mu ji sa’ad da aka kori wani danginmu ko kuma aboki na kud da kud daga ikilisiya. Yadda muka bi da umurnin Littafi Mai Tsarki game da wannan batu zai nuna zurfin ƙaunarmu ga Allah da kuma amincinmu ga tsarinsa. * Ka yi la’akari da wasu tambayoyin da suka taso game da wannan batu.

Yaya za mu bi da mutumin da aka yanke zumunci da shi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yi tarayya da mutum mai-fasikanci, ko mai-ƙyashi, ko mai-bautan gumaka, ko mai-alfasha, ko mai-maye, ko mai-ƙwace, idan ana kiransa ɗan’uwa; da irin wannan, ko ci kada a yi.” (1 Korintiyawa 5:11) Game da dukan waɗanda ba su “lizima cikin koyarwar Kristi ba,” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku karɓe shi cikin gidanku, kada ku yi masa gaisuwa kuma: gama wanda ya yi masa gaisuwa yana tarayya cikin miyagun ayukansa.” (2 Yohanna 9-11) Ba ma tarayya ta ruhaniya ko tattaunawa da mutumin da aka yanke zumunci da shi. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 1981, shafi na 25 na Turanci, ta ce: “Faɗin ‘Barka dai’ ga mutum, zai iya zama mataki na fari da zai kai ga taɗi ko abota. Za mu so mu ɗauki wannan mataki na fari da mutumin da aka yanke zumunci da shi?”

Gudun irin wannan mutumin ya wajaba ne? Hakika, domin dalilai masu yawa. Na farko, batu ne na aminci ga Allah da kuma Kalmarsa. Muna yi wa Jehobah biyayya ba kawai a lokacin da yin hakan yake da sauƙi ba, amma har a lokacin da yin haka yake da wuya. Ƙaunar Allah tana motsa mu mu yi wa dukan dokokinsa biyayya, da yake mun sani cewa shi mai adalci ne mai ƙauna kuma dokokinsa na kirki ne. (Ishaya 48:17; 1 Yohanna 5:3) Na biyu, janye wa daga mai laifi da ya ƙi tuba zai kāre mu da ikilisiya daga haɗari na ruhaniya da kuma na ɗabi’a kuma ya kāre suna mai kyau na ikilisiya. (1 Korintiyawa 5:6, 7) Na uku, matsayinmu bisa mizanin Littafi Mai Tsarki zai iya amfanar wanda aka yanke wa zumunci. Ta wajen tallafa wa matakin da kwamitin shari’a suka ɗauka, za mu iya taɓa zuciyar mai laifi da har zuwa yanzu ya ƙi ya karɓi taimako da dattawa suke so su yi masa. Idan waɗanda yake ƙauna suka guje shi wataƙila wannan zai taimake shi ya “koma cikin hankalinsa,” ya ga tsananin laifin da ya yi, kuma ya ɗauki matakai ya koma ga Jehobah.—Luka 15:17.

To yaya idan wanda aka yanke zumunci da shi dangi ne? A irin wannan yanayi, dangantaka na iyali zai iya jawo gwaji ƙwarai na aminci. Yaya za mu bi da dangi da aka yanke zumunci da shi? Ba za mu iya magana a kan dukan yanayi da zai taso ba, amma bari mu mai da hankali a kan guda biyu.

A wasu yanayi, wanda aka yanke wa zumuncin zai kasance yana zaune a gida tare da wasu cikin iyali. Tun da yanke zumunci da aka yi da shi bai kawo ƙarshen dangantaka ta iyali ba, za a iya ci gaba da ayyuka na yau da kullum da shi. Duk da haka, domin ayyukansa, mutumin ya zaɓi ya rushe dangantaka ta ruhaniya da yake tsakaninsa da iyalinsa. Saboda haka, ’yan iyalin da suke da aminci za su yanke zumunci na ruhaniya da ke tsakaninsu da shi. Alal misali, idan wanda aka yanke zumunci da shi yana nan, ba zai saka baki ba sa’ad da iyalin suka taru don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, idan wanda aka yanke zumunci da shi ɗan yaro ne, iyayen har ila suna da hakkin su koyar da shi kuma su yi masa horo. Saboda haka, iyaye masu ƙauna za su kafa tsarin nazari da yaron. *Misalai 6:20-22; 29:17.

A wasu yanayi kuma, wataƙila dangin da aka yanke zumunci da shi ba a gida yake da zama ba. Ko da yake zai kasance da bukatar saduwa da iyalin a wasu lokatai domin a biya wasu bukatun iyali, dukan irin wannan saduwa ya kamata a rage ta. Iyalai masu aminci ba sa neman dalilai na hulɗa da dangi da aka yanke zumunci da shi da ba ya tare da su. Maimakon haka, aminci ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa za ya motsa mu mu ɗaukaka umurnin Nassosi na yanke zumunci. Tafarkinsu na aminci zai kasance da muhimmanci ga mai laifi kuma ya taimake shi ya amfana daga horon da aka yi masa. *Ibraniyawa 12:11.

^ sakin layi na 1 Mizanin Littafi Mai Tsarki game da wannan ya kuma shafi waɗanda suka ware kansu daga ikilisiya.

^ sakin layi na 2 Domin ƙarin bayani game da yara ƙanana da aka yanke zumunci da su da suke tare da iyayensu, dubi Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Oktoba, 2001, shafi na 16-17 na Turanci, da kuma ta 15 ga Nuwamba, 1988, shafi na 20 na Turanci.

^ sakin layi na 3 Domin ƙarin bayani game da yadda za a bi da dangi da aka yanke zumunci da shi, dubi Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Afrilu, 1988, shafuffuka na 26-31, da kuma 15 ga Satumba, 1981, shafuffuka na 26-31 na Turanci.