Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 17

“Gina Kanku Bisa Bangaskiyarku Maficin Tsarki”

“Gina Kanku Bisa Bangaskiyarku Maficin Tsarki”

“Gina kanku bisa bangaskiyarku maficin tsarki, . . . ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah.”—YAHUDA 20, 21.

1, 2. Wane aikin gini ne kake yi, kuma me ya sa ingancin aikinka yana da muhimmanci ƙwarai?

A CE kana aiki tuƙuru a wajen wani gini. Ka ɗan daɗe da fara ginin kuma za a jima ana yin sa. Aikin ya kasance da ƙalubale amma kuma ya gamsar da kai. Ka ƙudurta cewa ko da menene ya faru ba za ka yi sanyin gwiwa ba ko kuma ka ja da baya, domin ingancin aikinka zai shafi rayuwarka a yanzu da nan gaba. Me ya sa? Domin kai ne ainihin ginin da ake yi!

2 Almajiri Yahuda ya nanata cewa muna bukatar mu gina kanmu. Sa’ad da ya aririci Kiristoci ‘su tsare kansu cikin ƙaunar Allah,’ ya kuma ambata ainihin abin da zai taimaka mana mu yi haka a wannan ayar: Ka ‘gina kanka bisa bangaskiyarka maficin tsarki.’ (Yahuda 20, 21) A waɗanne hanyoyi ne za ka iya gina bangaskiyarka ta kasance da ƙarfi saboda ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah? Bari mu mai da hankali ga ɓangarori uku na wannan gini na ruhaniya da ke gabanka.

KA CI GABA DA GINA BANGASKIYA BISA BUKATUN ADALCI NA JEHOBAH

3-5. (a) Shaiɗan zai so ya yaudare ka ka kasance da wane irin ra’ayi game da bukatun Jehobah? (b) Menene ya kamata ya zama ra’ayinmu game da bukatun Allah, kuma yaya zai shafi yadda muke ji? Ka kwatanta.

3 Na farko, muna bukatar mu ƙarfafa bangaskiyarmu ga dokokin Allah. Sa’ad da kake nazarin wannan littafin, ka karanta wasu dokoki masu adalci na Jehobah game da hali. Menene ra’ayinka game da su? Shaiɗan zai so ya ruɗe ka ka yi tunanin cewa dokokin Jehobah da mizanansa suna hana sukuni kuma suna zaluntarwa. Ya daɗe yana amfani da wannan tsarin tun daga lambun Adnin. (Farawa 3:1-6) Zai iya yaudararka kuwa? Hakan ya dangana ne bisa ra’ayinka.

4 Alal misali: A ce kana tafiya cikin wani lambu mai ban sha’awa, sai ka lura cewa an katange wani sashen lambun da bango mai ƙwari. Wannan sashen da aka katange yana da kyau sosai. Da farko, za ka ga kamar wannan katangar tana hana ka jin daɗi. Amma da ka duba wurin da kyau sai ka ga mayunwacin zaki yana neman abincin da zai ci! Yanzu za ka gane cewa lalle wannan katangar, kāriya ce. Da akwai wani mugun zakin da ke binka a yanzu ne? Kalmar Allah ta yi gargaɗi: “Ku yi hankali shimfiɗe, ku yi zaman tsaro: magabcinku Shaiɗan, kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.”—1 Bitrus 5:8.

5 Shaiɗan mugu ne. Domin Jehobah ba ya son Shaiɗan ya kama mu, ya kafa dokoki domin ya kāre mu daga “dabarun” wannan mugun. (Afisawa 6:11) Saboda haka, a duk lokacin da muka yi bimbini a kan dokokin Allah, zai da ce mu yi la’akari da ƙaunar da Ubanmu na samaniya yake mana a cikinsu. Idan muka ɗauke su haka, dokokin Allah za su kasance tushe na farin ciki da kāriya. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a, shari’a ta yanci, ya lizima, . . . wannan za ya zama mai-albarka a cikin aikinsa.”—Yaƙub 1:25.

6. Wace hanya ce mafi kyau ta gina bangaskiya bisa dokoki da mizanan Allah? Ka ba da misali.

6 Rayuwa bisa dokokin Allah ita ce hanya mafi kyau na gina bangaskiya ga Mai ba da dokoki da kuma hikimar da ke cikin dokokinsa. Alal misali, “shari’ar Kristi” ta ƙunshi umurnin da Yesu ya ba mu na koyar da wasu ‘dukan iyakar abin da ya umurce mu.’ (Galatiyawa 6:2; Matta 28:19, 20) Kiristoci kuma suna ɗaukan umurnin da aka ba su na halartar taro domin bauta da kuma karfafa juna da muhimmanci. (Ibraniyawa 10:24, 25) Umurnin Allah sun haɗa da gargaɗi da aka bayar na yin addu’a ga Jehobah kullum kuma daga zuciyarmu. (Matta 6:5-8; 1 Tassalunikawa 5:17) Sa’ad da muka bi waɗannan dokokin, za mu ga cewa suna ba da ja-gora mai kyau. Yin biyayya da su yana kawo mana farin ciki da gamsuwa da ba za mu iya samu ba a wani wuri a duniyar nan da ke cike da masifa. Sa’ad da ka yi bimbini game da yadda ka amfana domin kana bin dokokin Allah, hakan bai ƙarfafa bangaskiyarka a kansu ba ne?

7, 8. Ta yaya Kalmar Allah ta ba da tabbaci ga waɗanda suke damuwa cewa ba za su iya kasancewa a hanyar adalci ba bayan wasu shekaru?

7 Wasu suna damuwa cewa, zai yi wuya a ci gaba da bin dokokin Jehobah a kullum. Suna tsoron cewa ba za su iya ba. Idan ka taɓa jin haka, ka tuna waɗannan kalmomi: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi. Da ma ka yi sauraro ga dokokina! da hakanan ne da salamarka ta yi kamar kogi, adalcinka kuma kamar raƙuman teku.” (Ishaya 48:17, 18) Ka taɓa yin tunanin yadda waɗannan kalmomin suke da ban ƙarfafa?

8 A nan Jehobah ya tuna mana cewa za mu amfani kanmu ta wajen yin koyi da shi. Ya yi mana alkawarin samun albarka biyu idan muka yi haka. Na farko, salamarmu za ta zama kamar kogi. Na biyu, adalcinmu kuma zai zama kamar raƙuman ruwa. Idan ka tsaya a bakin teku ka ga raƙuman ruwan suna zuwa ɗaya bayan ɗaya, babu shaka za ka ji cewa hakan zai ci gaba har abada. Ka sani cewa raƙuman ruwa za su ci gaba da zuwa, har abada. Jehobah ya ce adalcinka, wato, tafarkinka na yin abin da ke da kyau, zai iya zama kamar haka. Idan ka yi ƙoƙari ka kasance da aminci a gare shi, ba zai ƙyale ka ka faɗi ba! (Karanta Zabura 55:22.) Irin wannan alkawarin bai ƙarfafa bangaskiyarka ba ne ga Jehobah da kuma bukatunsa masu adalci?

“MU NACE BI ZUWA” MANYANTA

9, 10. (a) Me ya sa manyanta makasudi ne mai kyau ga Kiristoci? (b) Ta yaya ra’ayi na ruhaniya yake ba da farin ciki?

9 Ɓangare na biyu na aikin gininmu ya bayyana a cikin waɗannan kalmomi da aka hure: “Mu nace bi zuwa” manyanta. (Ibraniyawa 6:1) Manyanta makasudi ne mai kyau ga Kiristoci. Akasin kamilta wanda a yanzu ya fi ƙarfin ’yan adam, manyanta makasudi ne da za mu iya cim ma wa. Bugu da ƙari, Kiristoci suna samun ƙarin farin ciki a bautar Jehobah sa’ad da suka manyanta. Me ya sa?

10 Kirista da ya manyanta, mutum ne mai ruhaniya. Yana ganin abubuwa yadda Jehobah yake ganinsu. (Yohanna 4:23) Bulus ya rubuta: “Waɗanda ke bisa tabi’ar jiki al’amuran jiki su ke tattali; amma waɗanda ke bisa tabi’ar ruhu, al’amuran ruhu ne.” (Romawa 8:5) Ra’ayi na zahiri yana kawo farin ciki kaɗan ne kawai, domin yana kasancewa mai sonkai, marar hangen nesa kuma yana mai da hankali bisa abin duniya. Ra’ayi na ruhaniya yana kawo farin ciki, domin yana mai da hankali ne ga Jehobah, “Allah mai-albarka.” (1 Timothawus 1:11) Mutum mai ruhaniya yana ɗokin ya faranta wa Jehobah rai kuma yana farin ciki har sa’ad da yake fuskantar gwaji. Me ya sa? Domin gwaji yana ba da zarafin tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne kuma yana sa mu kasance da aminci, mu kuma faranta wa Ubanmu na samaniya rai.—Misalai 27:11; karanta Yaƙub 1:2, 3.

11, 12. (a) (b) Menene Bulus ya ce game da “wasa hankulanmu” na Kirista, kuma menene ma’anar kalmar nan da aka fassara “wasa”? (b) Wace wāsawa ce dole a yi wa jiki domin ta manyanta ta zama ƙwararre?

11 Ruhaniya da manyanta suna samuwa ne ta wajen koyo. Ka yi la’akari da wannan ayar: “Abinci mai-ƙarfi domin isassun mutane ne, watau waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Sa’ad da Bulus ya ce hankulanmu “wasassu” ne, ya yi amfani ne da kalmar Helenanci da ake yawan amfani da ita a wajen wasa a ƙarni na farko a Hellas, domin ana iya fassara ta ‘wasasse kamar ɗan wasan motsa jiki.’ Ka yi tunanin irin aikin da wannan ya ƙunsa.

Mai wasan motsa jiki yana wāsa jikinsa ta wajen aiki

12 Sa’ad da aka haife mu, jikinmu ba wasasse ba ne. Alal misali, jariri ba ya iya sanin inda ƙafafunsa da damtsensa suke. Saboda haka, jariri yake motsa hannu ko ta ina, har ya mari kansa a fuska, hakan na ɓata masa rai kuma ya ba shi mamaki. Amma a hankali, jiki zai wāsu. Jaririn zai fara rarrafe, ya fara tafiya, ya fara gudu. * Amma ɗan wasan motsa jiki kuma fa? Sa’ad da ka ga wannan ɗan wasa yana tsalle-tsalle da juye-juye daidai, babu wata tambaya, ka san cewa jikinsa ya wāsu. Wannan ƙwararen ɗan wasa ya ba da lokaci mai yawa yana koyo shi ya sa ya ƙware. Irin wannan wāsa jiki, Littafi Mai Tsarki ya ce, “amfaninta kaɗan” ne. Wasa hankulanmu na ruhaniya ya fi muhimmanci!—1 Timothawus 4:8.

13. Ta yaya za mu wāsa hankulanmu?

13 A wannan littafin, mun tattauna abubuwa masu yawa da za su taimake ka ka wasa hankalinka saboda ka kasance da aminci ga Jehobah a matsayinka na mutum mai ruhaniya. Cikin addu’a ka yi la’akari da mizanai da kuma dokoki sa’ad da za ka yanke shawara a rayuwarka ta yau da kullum. A dukan wata shawarar da ka fuskanta, ka tambayi kanka: ‘Wace doka ce ta Littafi Mai Tsarki ko kuma mizani ya shafi wannan batu? Ta yaya zan yi amfani da su? Wane tafarki ne zai faranta wa Ubana na samaniya rai?’ (Karanta Misalai 3:5, 6; Yaƙub 1:5) Kowace shawara da ka yanke a wannan hanyar za ta taimaka wajen wāsa hankalinka. Irin wannan wāsawa za ta taimake ka ka zama mutum mai ruhaniya da gaske.

14. Wace yunwa muke bukatar mu ji domin mu girma a ruhaniya, duk da haka, wane gargaɗi ya kamata mu riƙa tunawa?

14 Ko da yake muna iya manyanta, da akwai zarafin girma cikin ruhaniya. Girma ya dangana ne bisa abinci. Saboda haka, Bulus ya ce: “Abinci mai-ƙarfi domin isassun mutane ne.” Abu mai muhimmanci na ƙarfafa bangaskiya shi ne mu ci gaba da cin abinci mai-ƙarfi na ruhaniya. Sa’ad da ka fara amfani da abin da ka koya daidai, wannan hikima ce, kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hikima ita ce masamman.” Saboda haka, muna bukatar mu ji yunwar gaskiya mai tamani da Ubanmu yake bayarwa. (Misalai 4:5-7; 1 Bitrus 2:2) Hakika, samun ilimi da kuma hikima ta Allah ba wani dalili ba ne na fahariya. Muna bukatar mu riƙa bincika kanmu a kai a kai domin kada fahariya ko kuma wasu halaye su yi jijiya a zukatanmu. Bulus ya rubuta: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani; ku yi wa kanku ƙwanƙwanto.”—2 Korintiyawa 13:5.

15. Me ya sa ƙauna take da muhimmanci domin girma cikin ruhaniya?

15 Ana iya gama gina gida, amma duk da haka aikin zai ci gaba. Kula da kuma gyara yana da muhimmanci, kuma yin wasu ƙari yana iya wajaba sa’ad da yanayi ya canja. Menene muke bukata domin mu manyanta kuma mu riƙe ruhaniyarmu? Fiye da kome, ƙauna. Muna bukatar mu ci gaba da girma cikin ƙauna ga Jehobah da kuma ga ’yan’uwanmu masu bi. Idan ba mu da ƙauna, dukan iliminmu da ayyukanmu za su kasance banza, kamar yawan surutu. (1 Korintiyawa 13:1-3) Da ƙauna za mu manyanta a ruhaniya kuma mu ci gaba da girma cikin ruhaniya.

KA MAI DA HANKALINKA BISA BEGE DA JEHOBAH YA BAYAR

16. Wane irin tunani ne Shaiɗan yake sa a yi, amma wace kāriya ce Jehobah ya yi tanadi?

16 Bari mu tattauna wani ɓangare kuma na ƙarfafa kanmu. Domin ka ƙarfafa kanka a matsayin mabiyin Kristi na gaskiya, kana bukatar ka kula da yadda kake tunani. Shaiɗan, mai mulkin wannan duniyar, gwani ne wajen sa mutane su fara tunani marar kyau, damuwa, rashin gaskatawa, da kuma tsoro. (Afisawa 2:2) Irin wannan tunani yana da haɗari ga Kirista kamar yadda ruɓa take ga gidan katako. Abin farin ciki, Jehobah ya ba da kayan kāriya, wato, bege.

17. Ta yaya Kalmar Allah ta kwatanta muhimmancin bege?

17 Littafi Mai Tsarki ya lissafa ɓangarori dabam dabam na makaman yaƙi na ruhaniya da muke bukata domin mu yaƙi Shaiɗan da kuma duniyarsa. Wani ɓangare babba na wannan makaman shi ne kwalkwali, wato “bege na ceto.” (1 Tassalunikawa 5:7-9) A zamanin dā soja ya sani cewa ba zai jima a bakin yaƙi ba idan ba shi da kwalkwali. Sau da yawa ana yin sa ne da ƙarfe a saka masa fata, idan aka saka kwalkwalin duk wani bugun da aka yi wa kai ba zai yi lahani ba. Kamar yadda kwalkwali yake kāre kai, haka bege zai kāre tunaninmu.

18, 19. Wane misali ne Yesu ya kafa na kasancewa da bege, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

18 Yesu ya kafa misali mai kyau wajen kasancewa da bege. Ka tuna abin da ya jimre a darensa na ƙarshe a rayuwarsa ta duniya. Abokinsa na kusa ya ci amanarsa domin kuɗi. Wani kuma ya musanci saninsa. Sauran kuma suka gudu suka bar shi. Mutanensa suka juya masa baya, suna neman sojojin Roma su yi masa kisan azaba. Daidai ne a ce Yesu ya fuskanci gwaji irin wanda ba za mu taɓa fuskanta ba. Menene ya taimake shi? Ibraniyawa 12:2 ta amsa: “Domin farinzuciya da aka sa gabansa, yana rena kunya, ya kuwa zauna ga hannun dama na al’arshen Allah.” Yesu bai taɓa manta da “farinzuciya da ka aka sa gabansa” ba.

19 Wane farin zuciya ne aka saka a gaban Yesu? Ya sani cewa idan ya jimre, zai tallafa wajen tsarkake sunan Jehobah mai tsarki. Zai ba da tabbaci mafi girma cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Babu wani bege kuma da zai faranta wa Yesu rai fiye da wannan! Ya sani cewa Jehobah zai albarkaci tafarkinsa na aminci, ya kuma sani cewa a nan gaba zai sake saduwa da Ubansa. Yesu ya kasance da wannan bege na farin ciki har a lokacin da yake fuskantar wahala mai tsanani. Muna bukatar mu yi haka. Mu ma muna da farin ciki da aka saka a gabanmu. Jehobah ya ɗaukaka kowannenmu da gatar taimakawa wajen tsarkake sunansa. Za mu iya tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne ta wajen zaɓan Jehobah ya zama Mamallakinmu mu kuma tsare kanmu cikin ƙaunar Ubanmu ko da wane irin gwaji da jarraba za mu fuskanta.

20. Menene zai taimake ka ka tsare tunaninka da kuma begenka?

20 Jehobah yana so ya albarkaci bayinsa masu aminci, kuma yana ɗokin yin haka. (Ishaya 30:18; karanta Malachi 3:10) Yana farin ciki ba bayinsa muradin zuciyarsu. (Zabura 37:4) Saboda haka ka mai da hankali kan bege da yake gabanka. Kada ka ba da kanka ga tunanin Shaiɗan da na duniyarsa. Idan ka lura cewa ruhun duniya ya fara shiga tunaninka ko zuciyarka, ka yi addu’a sosai ga Jehobah domin ka sami ‘salama ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.” Saboda haka, salama da Allah yake bayarwa za ta kāre zuciyarka da tunaninka.—Filibbiyawa 4:6, 7.

21, 22. (a) Wane bege ne mai girma waɗanda suke cikin “taro mai-girma” suke so? (b) Wane ɓangare ne na begen Kiristoci ka fi so, kuma menene ƙudurinka?

21 Wannan bege ne mai ban sha’awa da ya kamata ka yi bimbini a kai. Idan kana cikin “taro mai-girma,” wanda zai “fito daga cikin babban tsananin,” ka yi tunanin rayuwar da za ka samu nan ba da daɗewa ba. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Bayan an hallaka Shaiɗan da aljannunsa, za ka sami sauƙin da ba za ka iya kwatantawa ba. Wanene a tsakaninmu ya taɓa rayuwa wadda babu matsi na rinjaya na Shaiɗan? Idan babu wannan matsi, zai kasance abin farin ciki mu mai da wannan duniya ta zama aljanna a ƙarƙashin ja-gorancin Yesu da kuma abokan sarautarsa 144,000. Muna farin ciki da tunanin lokacin da dukan cututtuka da naƙasa za su shuɗe, mu kuma marabci waɗanda muke ƙauna daga matattu, da kuma yin rayuwa kamar yadda Jehobah ya nufa! Sa’ad da muka kai kamilta, za mu sami babban albarka, wato, alkawarin da aka yi a Romawa 8:21, wadda ta ce za mu sami “’yanci na darajar ’ya’yan Allah.”

22 Jehobah yana so ka sami ’yanci mai girma, ’yanci da ba za ka taɓa tunaninsa ba. Tafarkin wannan ’yanci ya dangana ne ga biyayya. Bai dace ba ne ka ƙoƙarta sosai ka ci ga ba da yi wa Jehobah biyayya? Saboda haka, ko ta yaya, ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka cikin mafificin tsarki, saboda ka tsare kanka cikin ƙaunar Allah har abada abadin!

^ sakin layi na 12 Masana kimiyya sun ce muna koyon sanin yanayin jikinmu, saboda jiki ya san inda yake aiki da kuma inda gaɓaɓuwa suke. Alal misali, wannan sani yana sa mu iya tafa hannunmu da idanunmu a rufe. Wata babbar mace da ta yi rashin wannan sanin ta kasa tashi tsaye, da yin tafiya, ko kuma ta zauna domin wannan rashin.