Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 4

Sun Saurari Shaiɗan—Mene Ne Sakamakon?

Sun Saurari Shaiɗan—Mene Ne Sakamakon?

Adamu da Hauwa’u ba su yi biyayya ga Allah ba, sai suka mutu. Farawa 3:6, 23

Hauwa’u ta saurari macijin kuma ta ci ’ya’yan itacen. Bayan haka, ta ba Adamu, kuma ya ci.

Abin da suka yi bai dace ba, zunubi ne. Allah ya kore su daga gidansu ta Aljanna.

Rayuwa ta yi wa su da ’ya’yansu wuya. Sun tsufa kuma suka mutu. Ba su je inda ruhohi suke ba; sun daina wanzuwa.

Matattu ba su san kome ba. Farawa 3:19

Muna mutuwa ne domin duk mun fito daga Adamu da Hauwa’u. Matattu ba sa iya gani, ba sa iya ji kuma ba su iya yin kome.—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Ba nufin Jehobah ba ne cewa mutane su mutu. Ba da daɗewa ba zai ta da matattu. Idan suka saurare shi, za su rayu har abada.