Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA 6

Mene Ne Muka Koya Daga Labarin Babbar Rigyawa?

Mene Ne Muka Koya Daga Labarin Babbar Rigyawa?

Allah ya halaka miyagun amma ya ceci Nuhu da iyalinsa. Farawa 7:11, 12, 23

An yi kwana 40 ana ta ruwan sama dare da rana, kuma ruwan ya rufe dukan duniya. Dukan mugayen mutanen suka mutu.

Mala’ikun da suka yi tawaye suka rikiɗa suka zama aljanu.

Waɗanda suke cikin jirgin ruwan sun tsira. Ko da yake Nuhu da iyalinsa sun mutu daga baya, Allah zai ta da su daga matattu kuma za su rayu har abada.

Allah zai sake halaka miyagu kuma zai ceci mutane masu aminci. Matta 24:37-39

Shaiɗan da aljanu suna ci gaba da yaudaran mutane.

A yau, kamar zamanin Nuhu, mutane da yawa sun yi watsi da ja-gora mai kyau na Jehobah. Ba da daɗewa ba, Jehobah zai halaka dukan mugaye.—2 Bitrus 2:5, 6.

Kamar Nuhu, akwai wasu mutanen da suke saurarar Allah kuma suna yin abin da ya ce; su ne Shaidun Jehobah.