Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 1

Su Wane Ne Shaidun Jehobah?

Su Wane Ne Shaidun Jehobah?

Denmark

Taiwan

Benezuela

Indiya

Shaidun Jehobah nawa ne ka sani? Mai yiwuwa wasu daga cikinmu maƙwabtanka ne ko abokan aikinka ko kuma ajinku ɗaya a makaranta. Wataƙila mun taɓa tattauna Littafi Mai Tsarki da kai. Su wane ne ne mu, kuma me ya sa muke gaya wa mutane a fili abubuwan da muka yi imani da su?

Mu mutane ne kamar ka. Mun fito ne daga al’ummai da al’adu dabam-dabam. Wasu daga cikinmu suna bin wani addini ne a dā, wasu kuma ba su yi imani da Allah ba a dā. Amma kafin mu zama Shaidu, mun zauna kuma mun bincika koyarwar da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai. (Ayyukan Manzanni 17:11) Mun amince da abin da muka koya, sa’an nan muka yanke shawarar bauta wa Jehobah Allah.

Muna amfana daga nazarin Littafi Mai Tsarki. Kamar sauran mutane, muna fama da matsaloli da kuma kasawarmu. Amma domin muna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarmu ta yau da kullum, hakan ya inganta rayuwarmu sosai. (Zabura 128:1, 2) Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa muke gaya wa mutane abubuwa masu kyau da muka koya daga Littafi Mai Tsarki.

Muna yin abubuwan da Allah ya ce. Abubuwan da muke koya daga Littafi Mai Tsarki, tare da faɗin gaskiya da yin alheri suna kyautata lafiyar jikinmu kuma suna sa mu daraja mutane. Ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki suna sa mutane su zama masu kirki, kuma suna ƙarfafa haɗin kai da halaye masu kyau a cikin iyali. Domin mun san cewa “Allah ba mai-tara ba ne,” mun ɗauki kanmu kamar iyali guda wadda ta yi imani da abu guda. Ko da yake mu maƙwabtanka ne, muna da abin da ya bambanta mu da sauran mutane.—Ayyukan Manzanni 4:13; 10:34, 35.

  • Kamar sauran mutane, waɗanne abubuwa ne ke shafan Shaidun Jehobah?

  • Waɗanne halaye masu kyau ne Shaidun Jehobah suka koya daga yin nazarin Littafi Mai Tsarki?