Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 4

Me Ya Sa Muka Fitar da Juyin Littafi Mai Tsarki Mai Suna New World Translation

Me Ya Sa Muka Fitar da Juyin Littafi Mai Tsarki Mai Suna New World Translation

Kwango (Kinshasha)

Ruwanda

Sashen fassarar Symmachus, wadda ke ɗauke da sunan Allah a Zabura 69:31, a ƙarni na uku ko na huɗu a zamaninmu

A shekaru da dama da suka wuce, Shaidun Jehobah sun yi amfani da juyin Littafi Mai Tsarki dabam-dabam, sun buga su kuma sun rarraba su wa mutane. Amma, mun ga cewa muna bukatar mu fitar da sabon juyin da zai taimaka wa mutane su san ainihin “gaskiya,” domin hakan shi ne nufin Allah ga kowa. (1 Timotawus 2:3, 4) Shi ya sa muka soma fitar da wasu sassan juyinmu na New World Translation a harshen Turanci na zamani a shekara ta 1950. An fassara wannan Littafi Mai Tsarki daidai wa daida a cikin harsuna fiye da 130.

Ana bukatar fassarar Littafi Mai Tsarki mai sauƙin ganewa. Yadda ake rubuta harsuna yana canjawa bayan wani lokaci, kuma kalmomi na dā masu wuyar fahimta aka yi amfani da su a juyi da yawa na Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, a kwanan baya, an sake gano tarin rubutun dā na Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya taimaka mana mu ƙara fahimtar harsunan Ibrananci da Aramaic da kuma Helenancin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da su.

Ana bukatar fassarar da take ɗauke da ainihin abin da Allah ya ce. Ya kamata masu fassara Littafi Mai Tsarki su bi ainihin abin da aka rubuta tun asali maimakon su canja Kalmar da Allah ya hure. Amma, a yawancin juyin Littafi Mai Tsarki, ba a yi amfani da sunan Allah, Jehobah ba.

Ana bukatar Littafi Mai Tsarki da zai ɗaukaka Mawallafinsa. (2 Sama’ila 23:2) A cikin New World Translation, an mai da sunan Jehobah a wuraren da suka bayyana sau 7,000 a cikin rubutun dā na Littafi Mai Tsarki, kamar yadda aka nuna a misalin da ke ƙasa. (Zabura 83:18) An yi shekaru da dama ana bincike domin a bi ainihin abin da ke cikin rubutun dā na Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya haifar da juyi mai kyau wanda ya bayyana nufin Allah. Ko kuna da juyin New World Translation a yarenku ko a’a, muna ƙarfafa ka ka mai da hankali sosai ga karanta Kalmar Jehobah a kowace rana.—Joshua 1:8; Zabura 1:2, 3.

  • Me ya sa muka tsai da shawara cewa ana bukatar sabon juyin Littafi Mai Tsarki?

  • Mene ne ya kamata duk wanda yake son ya koyi nufin Allah zai yi a kowace rana?