Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 19

Wane Ne Bawan Nan Mai Aminci Mai Hikima?

Wane Ne Bawan Nan Mai Aminci Mai Hikima?

Dukanmu muna amfana daga ilimin nan game da Allah

Gab da mutuwarsa, Yesu ya tattauna da almajiransa guda huɗu, wato, Bitrus da Yakubu da Yohanna da Andarawus. Yayin da yake gaya musu alamar bayyanuwarsa a kwanaki na ƙarshe, Yesu ya yi wata tambaya mai muhimmanci: ‘Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin ya ba su abincinsu a lotonsa?’ (Matta 24:3, 45; Markus 13:3, 4) Yesu ya tabbatar wa almajiransa cewa a matsayinsa na ‘ubangijinsu,’ zai naɗa waɗanda za su riƙa koya musu kalmar Allah babu fashi, a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Su wane ne za su kasance bawan nan?

Ƙaramin ruƙuni ne na shafaffun mabiyan Yesu. “Bawan” yana tanadar da ilimi game da Jehobah ga waɗanda suke bauta Masa. Mun dogara ga bawa mai aminci ya ci gaba da yi mana tanadin ‘abinci a kan kari.’—Luka 12:42, Littafi Mai Tsarki.

Yana kula da gidan Allah. (1 Timotawus 3:15) Yesu ya ɗora wa bawan nan nauyin kula da aikin da ake yi a sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya, wato, kula da dukiyarta, ba da ja-gora game da yadda za a yi wa’azi da kuma koyar da mu ta hanyar ikilisiyoyinmu. Don ya tanadar da abin da muke bukata a kan kari, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yana yaɗa maganar Allah ta hanyar littattafan da muke amfani da su wajen yin wa’azi, da kuma koyarwar da muke samu a taronmu na ikilisiya da manyan taro.

Bawan nan ya kasance da aminci wajen koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma bin umurnin da aka ba shi na yin wa’azin bishara, kuma ya kasance da hikima a yadda yake kula da duk wani abin da Yesu ya saka a ƙarƙashin kulawarsa a duniya. (Ayyukan Manzanni 10:42) Jehobah yana ci gaba da jawo mutane masu yawa su zama shaidunsa kuma yana amfani da bawa nan mai hikima wajen tanadar da isashen ilimin da zai sa su san Allah.—Ishaya 60:22; 65:13.

  • Wane ne Yesu ya naɗa ya koya wa almajiransa game da Allah?

  • A waɗanne hanyoyi ne bawan nan ya kasance da aminci da kuma hikima?