Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 24

Yaya Muke Samun Kuɗin Gudanar da Ayyukanmu a Faɗin Duniya?

Yaya Muke Samun Kuɗin Gudanar da Ayyukanmu a Faɗin Duniya?

Nepal

Togo

Birtaniya

A kowace shekara, ƙungiyarmu tana buga miliyoyin Littafi Mai Tsarki tare da littattafai, tana rarraba su ba tare da gaya wa mutane su biya kaza ba. Muna gina Majami’un Mulki da ofisoshin reshe kuma muna kula da su. Muna tallafa wa dubban masu hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje, kuma muna kai kayan agaji sa’ad da bala’i ya auku. Saboda haka, kana iya tambaya, ‘Ta yaya ake samun kuɗaɗen yin waɗannan ayyukan?’

Ba ma gaya wa mutane su ba da ushiri kuma ba ma yawo da faranti don karɓan baiko. Ko da yake muna kashe kuɗi sosai wajen gudanar da wa’azin da muke yi, ba ma roƙon kuɗi. Shekaru sama da ɗari da suka shige, fitowa ta biyu ta mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce, mun gaskata cewa Jehobah ne yake tallafa wa aikinmu kuma ba za mu “taɓa roƙon mutane su ba mu tallafi ba.” Kuma ba mu taɓa yin hakan ba!—Matta 10:8.

Ana tallafa wa aikinmu ne ta wajen ba da gudummawa da son rai. Mutane da yawa suna son yadda muke koyar da Littafi Mai Tsarki kuma suna bayar da gudummawa saboda hakan. Shaidun Jehobah suna amfani da lokacinsu da ƙuzari da kuɗinsu da sauransu, wajen yin nufin Allah a faɗin duniya, kuma suna yin hakan ne da farin ciki. (1 Labarbaru 29:9) Akwai akwatuna a Majami’ar Mulki da kuma wuraren manyan taronmu inda waɗanda suke son su ba da gudummawa suke iya saka gudummawarsu. Ƙari ga haka, ana iya ba da gudummawa ta dandalinmu na jw.org/ha. A yawancin lokaci, muna samun gudummawar kuɗin nan ne daga mutanen da ba su da abin hannu. Mutanen nan suna kama ne da gwauruwa talaka wadda Yesu ya yaba wa. Duk da cewa talaka ce, ta ba da gudummawa da zuciya ɗaya. (Luka 21:1-4) Saboda haka, kowane mutum zai iya yin “ajiya” domin ya ba da gudummawa ‘bisa yadda ya yi niyya a zuciyarsa.’—1 Korintiyawa 16:2; 2 Korintiyawa 9:7.

Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da motsa mutanen da suke son su ‘girmama shi da wadatarsu,’ su tallafa wa aikin wa’azin Mulki domin nufinsa ya cika.—Misalai 3:9.

  • Mene ne ya bambanta ƙungiyarmu da sauran addinai?

  • Yaya ake amfani da gudummawar da mutane suka bayar da son rai?