Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 27

Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?

Yaya Laburaren da ke Majami’ar Mulki Zai Amfane Mu?

Isra’ila

Jamhuriyar Czech

Bini

Cayman Islands

Za ka so ka yi wasu bincike don ka ƙara sanin Littafi Mai Tsarki? Kana son ka san wani nassi ko mutum ko wuri ko wani abu da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki? Ka taɓa tunanin ko Kalmar Allah za ta taimaka maka ka warware damuwarka? Ka je ka yi amfani da laburaren da ke Majami’ar Mulki.

Ana samun littattafan yin bincike a cikin laburaren. Wataƙila ba ka da dukan littattafan da suka bayyana Littafi Mai Tsarki, waɗanda Shaidun Jehobah suka wallafa a harshenku. Amma laburaren da ke Majami’ar Mulki yana ɗauke da yawancin littattafan da aka wallafa kwanan nan. Wataƙila akwai fassarar Littafi Mai Tsarki dabam-dabam da ƙamus mai kyau da wasu littattafan yin bincike a laburaren. Za ka iya yin amfani da laburaren kafin a soma taro ko bayan an kammala taro. Idan akwai kwamfuta a wurin, kana iya samun Watchtower Library a ciki. Watchtower Library wata fasaha ce da ake sakawa cikin kwamfuta kuma tana ɗauke da littattafanmu masu yawa, tana da sauƙi wajen bincika batu ko kalma ko kuma nassi.

Yana da amfani ga ɗalibai na taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu. Za ka iya yin amfani da laburaren da ke Majami’ar Mulki sa’ad da kake shirya aikin da aka ba ka a taro. Mai kula da taron Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu ne zai riƙa kula da laburaren. Shi ke da hakkin tabbatar da cewa an saka sababbin littattafai a laburaren kuma an tsara su yadda ya kamata. Mai kula da makaranta ko kuma malamin da ke koya maka Littafi Mai Tsarki zai iya nuna maka yadda za ka samu bayanin da kake so. Amma kada ka ɗauki littattafai daga laburaren Majami’ar Mulki ka kai gida. Hakika, bai kamata mu yi sakaci da littattafan ba, kuma kada mu yi rubutu a cikinsu.

Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa idan muna so mu samu “sanin Allah,” dole ne mu biɗe shi ‘kamar yadda ake biɗar ɓoyayyun dukiya.’ (Misalai 2:1-5) Laburaren da ke Majami’ar Mulki zai iya taimaka maka ka soma binciken da kake so.

  • Waɗanne kayan bincike ne ake samu a laburaren da ke Majami’ar Mulki?

  • Wane ne zai iya taimaka maka ka yi amfani da laburaren yadda ya kamata?