Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 1

Mene Ne Albishirin?

Mene Ne Albishirin?

1. Mene ne albishirin da Allah yake mana?

Allah yana son mutane su ji daɗin rayuwa a duniya. Ya halicci duniya da dukan abubuwan da ke cikinta domin yana ƙaunar ’yan Adam. Nan ba da daɗewa ba, zai sa mutane daga dukan ƙasashe su ji daɗin rayuwa. Zai kawar da abubuwan da ke jawo wa ’yan Adam wahala.​—Karanta Irmiya 29:11.

Babu gwamnatin ɗan Adam da ta taɓa kawar da mugunta da rashin adalci da cuta da kuma mutuwa. Amma, ka san wani abin farin ciki? Nan ba da daɗewa ba, Allah zai cire gwamnatin ’yan Adam kuma zai kafa gwamnatinsa. Talakawan gwamnatin Allah za su more salama da koshin lafiya.​—Karanta Ishaya 25:8; 33:24; Daniyel 2:44.

2. Me ya sa ake bukatar wannan albishirin da gaggawa?

Za a daina shan wahala sa’ad da Allah ya halaka miyagun mutane. (Zafaniya 2:3) A wane lokaci ne hakan zai faru? Kalmar Allah ta annabta wannan mugun yanayin da ke yi wa ’yan Adam barazana a yau zai faru. Miyagun abubuwa da ke faruwa a yau sun nuna cewa Allah yana gab da halaka miyagu.​—Karanta 2 Timotawus 3:1-5.

3. Me ya kamata mu yi?

Ya kamata mu koya game da Allah daga Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Yana kama da wasiƙa da mahaifi mai ƙauna ya rubuta wa ’ya’yansa. Littafi Mai Tsarki yana koya mana yadda za mu ji daɗin rayuwa da kuma yadda za mu samu rai na har abada a nan gaba a duniya. Wasu ba za su yi farin ciki ba don kana nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma tun da Allah ya yi mana alkawari cewa za mu ji daɗin rayuwa a nan gaba, bai kamata mu ƙyale kowa ya sa mu sanyin gwiwa ba.​—Karanta Misalai 29:25; Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7.