Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 3

Rahab Ta Ba da Gaskiya ga Jehobah

Rahab Ta Ba da Gaskiya ga Jehobah

A ce yanzu muna birnin Yariko. Wannan birnin yana ƙasar Kan’ana ne kuma mutanen da ke wurin ba su ba da gaskiya ga Jehobah ba. Akwai wata mata mai suna Rahab a wannan birnin.

A lokacin da Rahab take ƙarama, ta ji labarin yadda Musa ya raba Jar Teku kuma ya fitar da ’ya’yan Isra’ila daga ƙasar Masar. Ta kuma ji yadda Jehobah ya taimake su su yi nasara a kan waɗanda suke yaƙi da su. Yanzu ta ji cewa Isra’ilawa suna kusa da Yariko.

Rahab ta boye ’yan leken asirin domin ta ba da gaskiya ga Jehobah

Wata rana da yamma, Isra’ilawa biyu suka je leƙen asiri a Yariko, kuma sun sauƙa a gidan Rahab. A daren ranar, sarkin Yariko ya ji cewa ’yan leƙen asiri guda biyu sun shigo birnin kuma suna gidan Rahab. Sai sarkin ya aiki wasu mazaje su je su kamo su. Amma Rahab ta ɓoye su a saman gidanta sai ta gaya wa mutanen sarkin cewa: ‘I, mazajen sun zo wurina, amma sun riga sun bar birnin. Idan kun bi su yanzu, za ku kama su!’ Ka san abin da ya sa Rahab ta ɓoye ’yan leƙen asirin nan?— Ta yi hakan ne domin ta ba da gaskiya ga Jehobah kuma ta san cewa Jehobah zai ba ’ya’yan Isra’ila ƙasar Kan’ana.

Kafin ’yan leƙen asirin su bar gidan Rahab, sun gaya mata cewa ita da iyayenta da kuma ’yan’uwanta za su tsira idan aka halaka Yariko. Ka san abin da suka gaya mata ta yi?— Sun ce: ‘Ki karɓi wannan jar igiyar kuma ki ɗaura a bakin tagarki. Idan kika yi hakan, duk wanda yake cikin gidanki zai tsira.’ Rahab ta yi abin da ’yan leƙen asirin suka gaya mata ta yi. Ka san abin da ya faru bayan haka?—

Jehobah ya ceci Rahab da iyayenta da kuma ’yan’uwanta

Kwanaki kaɗan bayan haka, Isra’ilawa suka zagaya birnin kuma ba su ce kome ba. Sun yi hakan sau ɗaya kowace rana har kwana shida. Amma a rana ta bakwai, sun zagaya birnin sau bakwai kuma dukansu suka yi ihu da babbar murya. Sai Jehobah ya sa ganuwar birnin ta rushe gaba ɗaya. Amma gidan da aka ɗaura jar igiya a tagarsa bai rushe ba, duk da cewa an gina gidan a jikin ganuwar birnin! Ka ga gidanta a cikin wannan hoto?— Rahab da iyayenta da kuma ’yan’uwanta sun tsira!

Mene ne ka koya daga labarin Rahab?— Rahab ta ba da gaskiya ga Jehobah domin dukan abubuwa masu ban mamaki da ta koya game da shi. Kai ma kana koyan abubuwa da yawa masu ban mamaki game da Jehobah. Ka ba da gaskiya ga Jehobah kamar yadda Rahab ta yi?— Mun san ka yi hakan!

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Joshua 2:1-24; 6:1-5, 14, 15, 20-25

  • Ibraniyawa 11:31