Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 11

Sun Yi Rubutu Game da Yesu

Sun Yi Rubutu Game da Yesu

Ka ga mazajen da ke cikin wannan hoton?— Sunayensu Matta da Markus da Luka da Yohanna da Bitrus da Yaƙub da Yahuda da kuma Bulus. Dukansu sun rayu a lokaci ɗaya da Yesu, kuma sun yi rubutu game da shi. Yanzu za mu ƙara koya game da su.

Mene ne ka sani game da wadannan mutanen?

Guda uku a cikin mazajen nan manzanni ne da suka yi wa’azi tare da Yesu. Ka san su?— Matta da Yohanna da kuma Bitrus ne. Manzo Matta da manzo Yohanna sun san Yesu sosai kuma kowannensu ya rubuta littafi guda game da Yesu. Ƙari ga haka, manzo Yohanna ya rubuta littafin da ake kira Ru’ya ta Yohanna da kuma wasiƙu uku. Waɗannan wasiƙun su ne Yohanna ta Ɗaya da Yohanna ta Biyu da Yohanna ta Uku. Manzo Bitrus ya rubuta wasiƙu biyu a cikin Littafi Mai Tsarki. Ana kiran wasiƙun nan Bitrus ta Ɗaya da Bitrus ta Biyu. A cikin wasiƙarsa ta biyu, Bitrus ya yi rubutu a kan lokacin da Jehobah ya yi magana daga sama game da Yesu, cewa: ‘Wannan ɗana ne. Ina ƙaunarsa sosai kuma ina jin daɗinsa.’

Sauran mazajen da ke cikin hoton ma sun rubuta littattafai da suka taimaka mana mu san Yesu. Ɗaya daga cikinsu shi ne Markus. Wataƙila yana nan a lokacin da aka kama Yesu, kuma ya ga dukan abubuwan da suka faru. Wani kuma shi ne Luka. Shi likita ne kuma wataƙila ya zama Kirista bayan mutuwar Yesu.

Akwai ƙannen Yesu guda biyu da suka rubuta Littafi Mai Tsarki kuma suna cikin hoton nan. Ka san sunayensu?— Yaƙub da Yahuda ne. Da farko, ba su amince da Yesu ba. Sun ma ɗauka cewa ya soma hauka. Amma, daga baya sun amince da Yesu kuma sun zama Kiristoci.

Mutumin da ya rage a cikin mazajen da ke hoton nan da suka rubuta Littafi Mai Tsarki shi ne Bulus. Kafin Bulus ya zama Kirista, sunansa Shawulu ne. Ya ƙi jinin Kiristoci kuma ya yi musu mugunta. Ka san abin da ya sa Bulus ya zama Kirista?— Wata rana, Bulus yana tafiya a kan hanya sai kawai ya ji muryar wani daga sama. Yesu ne yake magana! Ya ce wa Bulus: ‘Me ya sa kake wahal da waɗanda suka gaskata da ni?’ Bayan haka Bulus ya canja halinsa kuma ya zama Kirista. Bulus ya rubuta littattafai guda 14 a cikin Littafi Mai Tsarki. Na farko shi ne littafin Romawa, kuma na ƙarshe littafin Ibraniyawa ne.

Muna karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana, ko ba haka ba?— Ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki, muna koyan abubuwa da yawa game da Yesu. Za ka so ka ƙara koya game da Yesu?—

KARANTA NASSOSIN NAN

  • 2 Bitrus 1:16-18

  • Markus 3:21; 14:51

  • Yahuda 1

  • Ayyukan Manzanni 9:1-18