Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 4

Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa

Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa

MANUFAR WANNAN BABIN

Bayin Allah suna ɗaukaka sunan Allah sosai

1, 2. Ta yaya fassarar New World Translation take ɗaukaka sunan Allah?

 A SAFIYAR ranar Talata, 2 ga Disamba, 1947, wani ƙaramin rukunin ’yan’uwa shafaffu daga Bethel da ke garin Brooklyn a Amirka sun yi shiri don su cim ma wani gagarumin aiki. Aikin yana bukatar ƙwazo sosai kuma sun ci gaba da yinsa har shekara 12. A ranar 13 ga Maris, shekara ta 1960, sun kammala aikin da suke yi na fassara Littafi Mai Tsarki. Watanni uku bayan haka, wato a ranar 18 ga Yuni, 1960, Ɗan’uwa Nathan Knorr ya fitar da cikakken Littafi Mai Tsarki mai suna New World Translation of the Holy Scriptures a taron gundumar da aka yi a birnin Manchester, a Ingila. Fitar da wannan sabon Littafi Mai Tsarki ya sa mahalartan taron farin ciki sosai. Sai mai jawabin ya ce: ‘Yau ranar farin ciki ce ga Shaidun Jehobah a faɗin duniya!’ Wani abu na musamman da ke cikin wannan Littafi Mai Tsarki shi ne yadda aka yi amfani da sunan Allah a wuraren da suke a Littafi Mai Tsarki na asali.

An fitar da juyin New World Translation of the Christian Greek Scriptures a taron Theocracy’s Increase Assembly a shekara ta 1950 (Hagu: Yankee Stadium, New York City; dama: Ghana)

2 An cire sunan Allah a juyin Littafi Mai Tsarki da yawa. Amma, shafaffun bayin Jehobah sun yi tsayayya da ƙulle-ƙullen da Shaiɗan yake yi don ya hana ’yan Adam sanin sunan Allah. Gabatarwar fassarar New World Translation of the Holy Scriptures da aka fitar a ranar ta ce: “Wani abu na musamman game da wannan Littafi Mai Tsarki shi ne sunan Allah da aka saka a wuraren da suke tun asali.” Hakika, an saka sunan Allah, wato Jehobah fiye da sau 7,000 a cikin fassarar New World Translation of the Holy Scriptures. Babu shakka, wannan fassarar ta ɗaukaka sunan Ubanmu da ke sama, Jehobah!

3. (a) Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gano game da ma’anar sunan Allah? (b) Mene ne ma’anar abin da ke littafin Fitowa 3:13, 14? (Ka duba akwatin nan  “Ma’anar Sunan Allah.”)

3 A shekaru da yawa da suka shige, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa sunan Allah yana nufin “Ni ina yadda Ni ke.” (Fit. 3:14) Saboda haka, Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Janairu, 1926 ta ce: “Sunan Jehobah yana nuni ga . . . Allahn da ba shi da mafari da kuma ƙarshe.” Amma sa’ad da mafassaran New World Translation of the Holy Scriptures suka soma aikinsu, Jehobah ya taimaka musu su fahimci cewa ba hakan kaɗai ne sunansa yake nufi ba, amma shi Allah ne mai manufa mai girma kuma yana ɗaukan mataki don cika manufofinsa. Sun koyi cewa sunan Jehobah yana nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Hakika, ya halicci sararin sama da mala’iku da mutane kuma yana ci gaba da cika nufinsa. Me ya sa yake da muhimmanci a ɗaukaka sunan Allah kuma yaya za mu iya yin hakan?

Tsarkake Sunan Allah

4, 5. (a) Mene ne muke roƙo sa’ad da muka ce: “A tsarkake sunanka”? (b) Ta yaya Allah zai tsarkake sunansa kuma a yaushe zai yi hakan?

4 Jehobah yana so a ɗaukaka sunansa. Hakika, abu na farko da Allah yake so shi ne a tsarkake sunansa, kamar yadda muka gani a roƙo na farko da Yesu ya yi a cikin addu’arsa ta misali: “A tsarkake sunanka.” (Mat. 6:9) Mene ne muke roƙo sa’ad da muka yi wannan addu’ar?

5 Kamar yadda muka koya a Babi na 1na wannan littafin, roƙon nan “A tsarkake sunanka” ɗaya ne cikin roƙo uku da ke cikin addu’ar Yesu ta misali da suka shafi nufin Jehobah. Sauran biyun su ne: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi.” (Mat. 6:10) Kamar yadda muke roƙon Jehobah ya ɗauki mataki don Mulkinsa ya zo kuma a yi nufinsa, hakan ma muke roƙonsa ya tsarkake sunansa. Wato, muna gaya wa Jehobah ya ɗauki mataki don ya cire dukan zargin da aka yi wa sunansa tun tawayen da aka yi a gonar Adnin. A wace hanya ce Jehobah zai amsa wannan addu’ar? Ya ce: ‘Ni ma sai in tsarkake sunana mai-girma, wanda aka ɓata shi a wurin al’ummai.’ (Ezek. 36:23; 38:23) Jehobah zai tsarkake sunansa a gaban dukan halittu a lokacin yaƙin Armageddon sa’ad da yake kawar da dukan mugunta.

6. Ta yaya za mu saka hannu wajen tsarkake sunan Allah?

6 Tarihi ya nuna cewa Jehobah yana ba wa bayinsa damar saka hannu a tsarkake sunansa. Sunan Allah yana da tsarki kuma ba za mu iya tsarkake shi fiye da yadda yake ba. Tun da haka ne, ta yaya za mu iya tsarkake sunansa? Ishaya ya ce: “Ubangiji mai-runduna shi za ku tsarkake.” Kuma Jehobah ya ce game da bayinsa: ‘Za su tsarkake sunana; . . . su ji tsoron Allah na Isra’ila.’ (Isha. 8:13; 29:23) Saboda haka, muna tsarkake sunan Allah ta wajen ɗaukansa da muhimmanci fiye da wasu sunaye. Ƙari ga haka, muna ɗaukan ma’anarsa da muhimmanci kuma muna taimaka wa mutane su ɗauke shi da tsarki. Hanya ta musamman da muke nuna cewa muna daraja sunan Allah ita ce ta wajen ɗaukan Jehobah a matsayin Sarkinmu da kuma yi masa biyayya da zuciya ɗaya.—Mis. 3:1; R. Yoh. 4:11.

Ya Shirya Su Su Amsa Sunansa Kuma Su Ɗaukaka Sunan

7, 8. (a) Me ya sa ya ɗauki lokaci kafin mutanen Allah su soma yin amfani da sunansa? (b) Mene ne za mu tattauna yanzu?

7 Bayin Allah a zamaninmu sun yi amfani da sunan Allah a littattafanmu tun daga shekara ta 1870. Alal misali, Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta watan Agusta, 1879 da kuma littafin waƙa da aka wallafa a shekarar mai suna Songs of the Bride, suna ɗauke da sunan Allah. Duk da haka, kamar dai Jehobah bai yarda a kira bayinsa da sunansa mai tsarki ba har sai bayan sun yi wasu gyara. Mene ne Jehobah ya yi don waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki su cancanci amsa sunansa?

8 Abubuwan da suka faru tsakanin shekara ta 1870 zuwa 1930 sun nuna yadda Jehobah ya sa bayinsa suka daɗa fahimtar wasu muhimman gaskiya game da sunansa. Bari mu tattauna uku daga cikin gaskiyar nan.

9, 10. (a) Me ya sa talifofin Hasumiyar Tsaro na dā suka fi mai da hankali ga Yesu? (b) Wane irin canji ne aka samu tun daga shekara ta 1919, kuma da wane sakamako? (Ka duba akwatin nan  “Yadda Hasumiyar Tsaro ta Ɗaukaka Sunan Allah.”)

9 Na farko, bayin Jehobah sun kasance da ra’ayin da ya dace game da muhimmancin sunan Allah. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ɗauka cewa shirin da Allah ya yi don a fanshe mu ne jigon Littafi Mai Tsarki. Shi ya sa Hasumiyar Tsaro take yawan mai da hankali ga Yesu a lokacin. Alal misali, sunan Yesu ya ninka na Jehobah sau goma a cikin mujallar a shekarar da aka fara wallafa ta. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1976 ta ce, a lokacin an ɗauki Yesu da muhimmanci fiye da kima. Amma da sannu-sannu, Jehobah ya taimaka musu su san cewa sunan Allah ne ya fi muhimmanci a cikin Littafi Mai Tsarki. Ta yaya hakan ya shafe Ɗaliban Littafi Mai Tsarki? Mujallar ta ci gaba da cewa, “sun soma ɗaukaka sunan Jehobah fiye da na Yesu” musamman daga shekara ta 1919. Hakika, daga shekara ta 1920 zuwa 1929, Hasumiyar Tsaro ta ambata sunan Allah fiye da sau 6,500!

10 Yadda waɗannan ’yan’uwan suka ɗaukaka sunan nan Jehobah ya nuna cewa suna son sunan Allah. Kamar Musa bawan Allah na dā, suna “shelar sunan Ubangiji,” Jehobah. (K. Sha 32:3; Zab. 34:3) A sakamako, Jehobah ya lura da yadda suke son sunansa kuma ya albarkace su kamar yadda aka ambata a cikin Nassi.—Zab. 119:132; Ibran. 6:10.

11, 12. (a) A wace hanya ce aka yi wasu gyara a littattafanmu jim kaɗan bayan shekara ta 1919? (b) Wane aiki ne Jehobah yake son bayinsa su mai da wa hankali, kuma me ya sa?

11 Na biyu, Kiristoci na gaske sun san ainihin aikin da Allah ya ba bayinsa. Jim kaɗan bayan shekara ta 1919, a ƙarƙashin ja-gorancin ruhun Jehobah, ’yan’uwa shafaffu da suke ja-gora a lokacin sun yi nazarin littafin annabcin Ishaya. A sakamakon haka, an yi wasu gyara a littattafanmu. Me ya sa waɗannan gyaran suka zama ‘abinci a lotonsa’?—Mat. 24:45.

12 Kafin shekara ta 1919, ba a taɓa yin bayani a kan nassin nan da ya ce: “Ku ne shaiduna, in ji Ubangiji, barana kuma wanda na zaɓa” a cikin Hasumiyar Tsaro dalla-dalla ba. (Karanta Ishaya 43:10-12.) Amma jim kaɗan bayan shekara ta 1919, littattafanmu sun soma mai da hankali ga wannan ayar, kuma sun ƙarfafa dukan shafaffu su saka hannu a aikin da Jehobah ya ɗanka musu, wato yin wa’azi. Tsakanin shekara ta 1925 zuwa 1931, an tattauna Ishaya sura ta 43 cikin fitowar Hasumiyar Tsaro guda 57 kuma kowace fitowa ta bayyana yadda surar ta shafi Kiristoci. Hakika, a waɗannan shekarun, Jehobah yana so bayinsa su san aikin da ya kamata su yi. Me ya sa? Domin ya “fara gwada su.” (1 Tim. 3:10) Kafin a kira Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da sunan Allah, suna bukatar su nuna ta ayyukansu cewa su Shaidun Jehobah ne da gaske.—Luk 24:47, 48.

13. Ta yaya Kalmar Allah ta bayyana batu mafi muhimmanci da ake bukata a sasanta?

13 Na uku, bayin Jehobah sun san amfanin tsarkake sunan Allah. Tsakanin shekara ta 1920-1929, sun fahimci cewa tsarkake sunan Allah shi ne batu mafi muhimmanci da za a warware. Ta yaya Kalmar Allah ta bayyana wannan gaskiyar? Ka yi la’akari da misalai biyu. Mene ne ainihin dalilin da ya sa Allah ya ’yantar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar? Jehobah ya ce: Domin ‘a sanar da sunana cikin dukan duniya.’ (Fit. 9:16) Kuma me ya sa Jehobah ya tausaya wa Isra’ilawa sa’ad da suka yi tawaye? Jehobah ya sake cewa: “Abin da na yi domin girman sunana ne, kada a ɓāta shi a ganin al’ummai.” (Ezek. 20:8-10) Waɗanne darussa ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka koya daga dukan waɗannan nassosin?

14. (a) Mene ne bayin Allah suka fahimta a tsakanin shekara ta 1927-1929? (b) A wace hanya ce wannan fahimtar ta shafi yin wa’azi? (Don ƙarin bayani, ka duba akwatin nan  “Dalili Mai Kyau Na Yin Wa’azi.”)

14 A tsakanin shekara ta 1927-1929, bayin Allah sun fahimci ma’anar abin da annabi Ishaya ya rubuta wajen shekaru 2,700 da suka shige. Ya ce: ‘Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.’ (Isha. 63:14, Littafi Mai Tsarki) Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimci cewa tsarkake sunan Allah ne batu mafi muhimmanci ba samun ceto ba. (Isha. 37:20; Ezek. 38:23) A shekara ta 1929, littafin nan Prophecy ya ce: “[Tsarkake] sunan Jehobah shi ne batu mafi muhimmanci da ke gaban dukan halittu.” Wannan gyara da aka yi ta motsa bayin Allah su yi shela game da Jehobah kuma su kawar da kowane zargi da ake yi wa sunansa.

15. (a) Mene ne ’yan’uwanmu suka samu a farkon shekara ta 1930? (b) Wane lokaci ne ya yi?

15 A farkon shekarar 1930, ’yan’uwanmu sun sami fahimta mai kyau game da muhimmancin sunan Allah, tare da aikin da Allah ya ba su, da kuma fahimta mai zurfi game da muhimmancin tsarkake sunan Allah. Yanzu lokaci ya yi da Jehobah zai ba bayinsa gatan amsa sunansa a gaban jama’a. Don mu fahimci yadda hakan ya faru, bari mu tattauna wasu abubuwan da suka auku a dā.

Jehobah Ya Zaɓi ‘Wata Jama’a Domin Sunansa’

16. (a) A wace muhimmiyar hanya ce Jehobah yake ɗaukaka sunansa? (b) A dā, su waye ne mutanen farko da suka amsa sunan Allah?

16 Wata hanya mai muhimmanci da Jehobah ya ɗaukaka sunansa ita ce, ya zaɓi mutane a duniya su amsa sunansa. Daga shekara ta 1513 kafin zamaninmu, al’ummar Isra’ila ce Jehobah ya ba gatan amsa sunansa. (Isha. 43:12) Amma, sun rasa wannan dangantaka mai kyau da Allah a shekara ta 33 a zamaninmu domin sun kasa cika alkawarin da suka yi da Allah. Jim kaɗan bayan haka, Jehobah ya “fara ziyarci Al’ummai, domin shi ciro wata jama’a daga cikinsu domin sunansa.” (A. M. 15:14) Wannan sabuwar al’ummar da Allah ya zaɓa sun zama “Isra’ila na Allah,” wanda ya ƙunshi mabiyan Kristi shafaffu da suka fito daga ƙasashe dabam-dabam.—Gal. 6:16.

17. Mene ne Shaiɗan ya yi nasarar yi?

17 An soma kiran almajiran Yesu ‘Kiristoci’ wajen shekara ta 44 a zamaninmu. (A. M. 11:26) Da farko, sunan yana wakiltar Kiristoci na gaskiya kaɗai. (1 Bit. 4:16) Amma, kamar yadda Yesu ya nuna a kwatancin alkama da zawan, Shaiɗan ya yi nasarar sa Kiristoci na ƙarya su soma amsa wannan sunan. Saboda haka, an yi shekaru da yawa ba a iya bambanta Kiristoci na gaskiya da na ƙarya ba. Amma a lokacin girbin, wato daga shekara ta 1914, an sami canji. Me ya sa? Domin mala’iku sun soma ware Kiristoci na gaskiya daga na ƙarya.—Mat. 13:30, 39-41.

18. Mene ne ya taimaka wa ’yan’uwanmu su gane cewa suna bukatar canja sunansu?

18 Bayan an naɗa bawan nan mai aminci a shekara ta 1919, Jehobah ya taimaka wa mutanensa su fahimci aikin da ya ba su. Nan da nan suka fahimci cewa yin wa’azi gida-gida ya bambanta su da Kiristoci na ƙarya. Da suka fahimci hakan, sai suka gane cewa sunan nan, “Ɗaliban Littafi Mai Tsarki” bai bambanta su sosai ba don ainihin burinsu shi ne su yi wa’azi game da Allah kuma su ɗaukaka sunansa, ba yin nazarin Littafi Mai Tsarki kaɗai ba. Shin wane suna ne zai dace da aikin da suke yi? An amsa wannan tambayar a shekara ta 1931.

Tsarin ayyukan taron gunduma, 1931

19, 20. (a) Wace zartarwa mai ƙayatarwa ce aka yi a taron gunduma a shekara ta 1931? (b) Yaya ’yan’uwa suka ji don wannan sabon sunan?

19 A watan Yuli na shekara ta 1931, wasu Ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda 15,000 sun hallara a birnin Columbus, Ohio, a ƙasar Amirka don wani babban taro. Sa’ad da suka ga cewa an rubuta wasu manyan harufa guda biyu, wato J da W a bangon tsarin ayyukan taron. Mutane suna ta mamaki ‘Ko mene ne ma’anar haruffan nan?’ Wasu sun ɗauka cewa yana nufin ‘Just Watch’ (Ka Kalla), wasu kuma sun ce ‘Just Wait’ (Ka Dakata). A ranar Lahadi, 26 ga Yuli, Ɗan’uwa Joseph Rutherford ya gabatar da wata zartarwa da ke ɗauke da wannan bayani mai ƙayatarwa: “Muna so a soma kiranmu da sunan nan, Shaidun Jehobah.” A lokacin ne dukan masu sauraro suka fahimci cewa waɗannan harufa suna nufin Jehovah’s Witnesses (Shaidun Jehobah) kuma an ɗauko sunan ne daga littafin Ishaya 43:10.

20 Masu sauraro sun yi murna kuma sun yi ta tafawa saboda wannan zartarwar. An ji wannan zartarwar a gidajen rediyo a ƙasashe da yawa a faɗin duniya! Ɗan’uwa Ernest Barber da matarsa Naomi da ke Ostareliya sun ce: “Sa’ad da ’yan’uwa a birnin Melbourne suka ji tafin da aka yi a Amirka a cikin rediyo, sai suka tashi tsaye suka yi ta tafawa. Ba za mu taɓa manta abin da ya faru ba!” a

Ana Ɗaukaka Sunan Allah a Dukan Duniya

21. Ta yaya sabon sunan nan ya sa aka ƙara ƙwazo a yin wa’azi?

21 Kasancewa da suna da aka ɗauko daga Littafi Mai Tsarki ya sa Shaidun Jehobah sun ƙara ƙwazo a yin wa’azi. Wasu majagaba ma’aurata, Edward da Jessie Grimes a Amirka da suka halarci taron gunduma ta shekara ta 1931 a birnin Columbus, sun ce: “Mun bar gida a matsayin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, amma mun dawo a matsayin Shaidun Jehobah. Mun yi farin ciki cewa mun sami sunan da zai taimaka mana mu ɗaukaka sunan Allahnmu.” Bayan taron gundumar, wasu Shaidu sun yi amfani da wani sabon tsari don su yi hakan. Sun gabatar da kansu ga mutanen da suke so su yi wa wa’azi ta wajen ba su wani kati mai ɗauke da wannan saƙon: “Mashaidin JEHOBAH yana wa’azi game da Mulkin JEHOBAH Allahnmu.” Hakika, mutanen Allah sun yi farin ciki cewa suna amsa sunan Jehobah, kuma a shirye suke su yi wa’azi a dukan duniya don sanar da muhimmancin sunan.—Isha. 12:4.

“Mun bar gida a matsayin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, amma mun dawo a matsayin Shaidun Jehobah”

22. Me ya nuna cewa bayin Jehobah suna da suna da ya bambanta su da sauran addinai?

22 Shekaru da yawa sun wuce tun daga lokacin da Jehobah ya motsa shafaffu su soma amfani da sunansa. Tun shekara ta 1931, shin Shaiɗan ya yi nasara wajen hana mutane sanin bayin Allah? Ya yi nasara kuwa wajen hana mutane bambanta mu daga wasu addinai? A’a! A maimakon haka, sunan nan Shaidun Jehobah ya bambanta mu sosai da sauran addinai. (Karanta Mikah 4:5; Malakai 3:18.) Hakika, an san mu sosai da amsa sunan Allah kuma ana saurin gane cewa mutum Mashaidin Jehobah ne idan yana yawan amfani da sunan. Maimakon addinan ƙarya su hana mutane sanin ibada ta gaskiya, Jehobah ya sa ibada ta gaskiya ta ‘kafu a ƙwanƙolin duwatsu.’ (Isha. 2:2) Babu shakka, a yau ana ɗaukaka bautar Jehobah da kuma sunansa sosai.

23. Bisa ga Zabura 121:5, wace muhimmiyar gaskiya game da Jehobah ce take ƙarfafa mu?

23 Sanin cewa Jehobah zai kāre mu daga harin Shaiɗan yanzu da kuma a nan gaba abin ƙarfafa ne! (Zab. 121:5) Muna da dalili mai kyau na amincewa da abin da kalaman marubucin zabura, sa’ad da ya ce: “Mai albarka ce al’ummar nan wadda Ubangiji ne Allahnta; mutanen da ya zaɓa domin gādonsa.”—Zab. 33:12.

a Don ƙarin bayani game da yin amfani da rediyo, ka duba Babi na 7, shafi na 72-74.