Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 8

Kayan Aiki don Yin Wa’azi​—⁠Wallafa Littattafai Domin Mutane a Faɗin Duniya

Kayan Aiki don Yin Wa’azi​—⁠Wallafa Littattafai Domin Mutane a Faɗin Duniya

MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah yana yi mana tanadin abubuwan da muke bukata don mu koyar da kowane mutum a kowace al’umma da ƙabila da harshe

1, 2. (a) A ƙarni na farko, mene ne ya taimaka aka yaɗa bishara a dukan Daular Roma? (b) Mene ne ya tabbatar da mu cewa muna da goyon bayan Allah a yau? (Ka duba akwatin nan  “Bishara a Harsuna Sama da 670.”)

 BAƘIN da suka zo Urushalima sun yi mamaki sosai saboda abin da suke ji. Mutanen Galili suna magana da harsunan wasu ƙasashe kuma abin da suke faɗa ya jawo hankalin masu sauraro. Ranar Fentakos ta shekara ta 33 ce, kuma a ranar an ba almajiran Yesu baiwar yin magana da harsuna dabam-dabam ta hanyar mu’ujiza, hakan ya tabbatar da cewa Allah yana tare da su. (Karanta Ayyukan Manzanni 2:1-8, 12, 15-17.) Mutane daga ƙabilu dabam-dabam sun ji bisharar a ranar kuma bayan haka, sun yaɗa bisharar a dukan Daular Roma.—Kol. 1:23.

2 A yau, bayin Jehobah ba sa yin magana da harsuna dabam-dabam ta mu’ujiza. Duk da haka, suna fassara saƙon Mulkin Allah zuwa harsuna fiye da 670 kuma hakan ya fi wanda aka yi a ƙarni na farko. (A. M. 2:9-11) Bayin Jehobah sun wallafa littattafai masu ɗimbin yawa a harsuna dabam-dabam kuma hakan ya sa bisharar Mulkin Allah ta yaɗu a dukan duniya. a Babu shakka, hakan tabbaci ne cewa Jehobah yana yin amfani da Yesu Kristi don ya ja-gorance mu a wa’azin da muke yi. (Mat. 28:19, 20) Yayin da muke tattaunawa game da kayan aikin da muka yi amfani da su a cikin shekaru 100 da suka shige, ka lura da yadda Sarkin ya koyar da mu don mu ƙaunaci mutane da kuma yadda ya ƙarfafa mu mu koyar da Kalmar Allah.—2 Tim. 2:2.

Sarkin Ya Shirya Bayinsa don Su Yi Wa’azi

3. Me ya sa muke yin amfani da kayan aiki dabam-dabam a wa’azi?

3 Yesu ya kamanta “zancen mulkin” da iri kuma ya kamanta zuciyar mutum da ƙasa. (Mat. 13:18, 19) Kamar yadda manomi zai yi amfani da kayan aiki dabam-dabam don ya nome ƙasa kafin ya yi shuki, bayin Jehobah ma suna amfani da kayan aiki dabam-dabam don su taimaka wa miliyoyin mutane su karɓi saƙon Mulkin. An yi amfani da wasu daga cikin kayan aikin nan na ɗan lokaci. Amma har wa yau ana amfani da wasu daga cikinsu, kamar su littattafai da mujallu. Akasin hanyoyin yin wa’azi ga jama’a da muka tattauna a babi na bakwai, dukan kayan aikin da za mu tattauna a wannan babin sun taimaka mana mu yi wa mutane wa’azi ido-da-ido.—A. M. 5:42; 17:2, 3.

Ana kera garmaho da na’urar yin magana a birnin Toronto, Kanada

4, 5. Ta yaya aka yi amfani da garmaho a dā, amma mene ne ba ya iya yi?

4 Jawabai da aka ɗauka a faifai. A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1949, masu shela sun yi amfani da jawaban Littafi Mai Tsarki da aka ɗauka a faifan garmaho kuma sukan kunna wa mutane su saurara. Kowane jawabin bai kai minti biyar ba. A wasu lokatai, waɗannan jawaban suna da jigo kamar su “Allah-uku-cikin-ɗaya,” “Purgatory,” wato, Gidan Azaba, da kuma “Mulki.” Ta yaya aka yi amfani da waɗannan jawaban da aka ɗauka? Ɗan’uwa Clayton Woodworth, Jr., wanda ya yi baftisma a shekara ta 1930 a ƙasar Amirka, ya ce: “A lokacin ina ɗaukan ƙaramin garmaho da wasu kayayyakin da ake haɗawa don a ji jawabin da kyau. Idan na isa ƙofar mutum, sai in buɗe jakar da ke ɗauke da garmahon, sa’an nan in shirya garmaho ɗin kafin in ƙwanƙwasa ƙofar. Sa’ad da maigidan ya buɗe ƙofar, sai in ce masa, ‘Ina da wani saƙo mai muhimmanci da zan so ka saurara.’” Wane sakamako ne aka samu? Ɗan’uwa Woodworth ya ce: “Sau da yawa mutane suna sauraron jawabin. A wasu lokuta, sai kurum su rufe ƙofarsu. Wasu kuma sukan ɗauka cewa ina sayar da garmaho ne.”

Kafin shekara ta 1940, an riga an yi jawabai dabam-dabam har sama da 90 da aka dauka a cikin fayafayai sama da miliyan daya

5 Kafin shekara ta 1940, an riga an yi jawabai dabam-dabam har sama da 90 da aka ɗauka a cikin fayafayai sama da miliyan ɗaya. Ɗan’uwa John E. Barr, wanda majagaba ne a Biritaniya a lokacin, kuma daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah, ya ce: “A tsakanin shekara ta 1936 zuwa 1945, ba na rabuwa da garmaho. Wa’azi yana mini wuya idan ba na riƙe da shi. Jin muryar Ɗan’uwa Rutherford sa’ad da nake bakin ƙofar mutane yana ƙarfafa ni sosai, kuma ina ji kamar yana nan tare da ni. Amma garmaho ba ya taimakawa wajen koyarwa, wato, ba ya ratsa zuciyar mutane sosai.”

6, 7. (a) Mene ne amfanin katunan wa’azi kuma mene ne kasawar su? (b) Ta yaya Jehobah ya ba mu abin faɗa?

6 Katuna. Daga shekara ta 1933, an ƙarfafa masu shela su yi amfani da katuna sa’ad da suke yin wa’azi gida-gida. Waɗannan katunan suna da faɗi kusan na takardar da muke rubuta rahoton wa’azi da ita. Suna ɗauke da saƙo daga Littafi Mai Tsarki da kuma sunayen littattafai da maigidan zai iya karantawa. Mai shelan zai miƙa wa maigidan katin sai ya ce masa ya karanta saƙon da ke cikinsa. Lilian Kammerud wadda daga baya ta yi wa’azi a ƙasar Puerto Rico da Ajantina a matsayin mai wa’azi a ƙasashen waje, ta ce: “Ina son yin wa’azi da wannan katin sosai.” Me ya sa? Ta ce: “Ba dukanmu ba ne muka iya wa’azi ba, saboda haka, katin ya taimaka mini in saba da yin magana da mutane.”

Katin wa’azi (Italiya)

7 Ɗan’uwa David Reusch wanda ya yi baftisma a shekara ta 1918, ya ce, “Waɗannan katunan wa’azin sun taimaki ’yan’uwa da yawa, domin yawancinsu suna ganin ba za su iya yin wa’azi daidai ba.” Amma wannan kayan aikin yana da nasa kasawar. Ɗan’uwan ya ci gaba da cewa: “A wasu lokuta, muna haɗuwa da mutanen da suke tsammanin cewa ba ma iya magana. A wani ɓangaren, kamar hakan gaskiya ne domin yawancinmu ba ma buɗe baki mu yi wa’azi. Amma Jehobah yana shirya mu ne don mu yi wa mutane wa’azi da bakinmu. Nan ba da daɗewa ba, zai ba mu abin faɗa ta wajen koya mana yadda za mu yi amfani da Nassosi sa’ad da muke wa’azi gida-gida. An cim ma hakan ta Makarantar Hidima ta Allah da aka kafa a shekara ta 1943.”—Karanta Irmiya 1:6-9.

8. Ta yaya za ka ba Kristi dama ya koyar da kai?

8 Littattafai. Tun shekara ta 1914, bayin Jehobah sun wallafa littattafai dabam-dabam sama da guda 100 da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. An wallafa wasu cikin waɗannan littattafan musamman don su taimaka wa masu shela su yi koyarwa da kyau. Wata ’yar’uwa ’yar ƙasar Denmark mai suna Anna Larsen, wadda ta yi wajen shekaru 70 tana wa’azi, ta ce: “Jehobah ya yi amfani da Makarantar Hidima ta Allah da kuma wasu littattafai don ya koya mana yin wa’azi sosai. Na tuna cewa littafi na farko da aka wallafa don cim ma wannan manufar shi ne Theocratic Aid to Kingdom Publishers da aka fitar a shekara ta 1945. Bayan haka, sai aka fitar da littafin nan “Equipped for Every Good Work,” a shekara ta 1946. A yanzu, muna yin amfani da littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education, wanda aka wallafa a shekara ta 2001.” Babu shakka, Jehobah ya yi amfani da Makarantar Hidima ta Allah da kuma littattafai da aka wallafa don wannan makarantar wajen koyar da mu mu zama ƙwararrun “masu hidima.” (2 Kor. 3:5, 6, Littafi Mai Tsarki) Shin kai ɗalibi ne a Makarantar Hidima ta Allah? Shin kana kawo littafin nan Benefit From Theocratic Ministry School Education taro a kowane mako kuma kana buɗe shi sa’ad da mai kula da makaranta yake ƙaulin littafin? Idan kana yin hakan, kana ba Kristi dama ne ya koyar da kai don ka ƙware a yin wa’azi.—2 Kor. 9:6; 2 Tim. 2:15.

9, 10. Ta yaya littattafai suka taimaka wajen shuka irin gaskiya?

9 Jehobah ya kuma taimaka mana ta wajen sa ƙungiyarsa ta wallafa littattafan da suke taimaka mana mu bayyana koyarwa masu muhimmanci da ke Littafi Mai Tsarki. Littafin nan The Truth That Leads to Eternal Life ya taimaka sosai. An fara wallafa shi ne a shekara ta 1968, kuma ya ratsa zukatan mutane nan da nan. Hidimarmu ta Mulki ta watan Nuwamba na shekara ta 1968 ta ce, “Saboda yadda ake ta bukatar littafin nan na Truth, . . . an yi ta aiki dare da rana a ofishin buga littattafai na Shaidun Jehobah da ke Brooklyn a watan Satumba.” Talifin ya daɗa cewa: “A watan Agusta, odar da aka samu na littafin nan Truth ya haura da fiye da kofi miliyan ɗaya da rabi!” Kafin shekara ta 1982, an riga an wallafa sama da kofi miliyan 100 na littafin a harsuna 116. Daga shekara ta 1968 zuwa 1986, wato a cikin shekaru 14, littafin ya sa mun sami ƙarin masu shela fiye da miliyan ɗaya. b

10 A shekara ta 2005, an fitar da wani littafi mai suna Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. A yanzu haka, an riga an buga wajen kofi miliyan 200 a harsuna 256! Mene ne sakamakon hakan? A cikin shekaru bakwai, wato daga shekara ta 2005 zuwa 2012, mutane wajen miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu ne suka zama masu shela. A cikin waɗannan shekarun, adadin mutanen da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su ya haura daga miliyan shida zuwa sama da miliyan takwas da dubu ɗari bakwai. Babu shakka, Jehobah yana yi mana albarka domin ƙoƙarin da muke yi wajen yin shukin iri na gaskiya.—Karanta 1 Korintiyawa 3:6, 7.

11, 12. Bisa ga nassosin da aka rubuta a nan, an wallafa mujallunmu domin su wane ne?

11 Mujallu. A dā can, ana wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro ne kawai don “ƙaramin garke,” wato, waɗanda suke da begen zuwa sama. (Luk 12:32; Ibran. 3:1) A ranar 1 ga Oktoba, 1919, ƙungiyar Jehobah ta fitar da wata mujalla dabam, wadda aka wallafa domin jama’a. Wannan mujallar ta sami karɓuwa sosai a wajen Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da kuma waɗanda suke karɓan mujallar, kuma an yi shekaru ana rarraba ta fiye da Hasumiyar Tsaro. Suna na farko da aka ba mujallar shi ne The Golden Age. An canja sunanta zuwa Consolation a shekara ta 1937, kuma aka sake canja sunanta zuwa Awake! a shekara ta 1946.

12 A cikin shekarun da suka shige, fasali da kuma salon mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! sun canja, amma manufarsu na yin shelar Mulkin Allah da kuma taimaka wa mutane su yi imani da Littafi Mai Tsarki ba su canja ba. A yau, ana wallafa Hasumiyar Tsaro ta nazari da kuma ta wa’azi. Ana wallafa Hasumiyar Tsaro ta nazari ne musamman don ‘iyalin gidan’ Kristi, wato “ƙaramin garke” da “waɗansu tumaki.” c (Mat. 24:45; Yoh. 10:16) Ana kuma wallafa Hasumiyar Tsaro ta wa’azi ne musamman domin waɗanda ba su san gaskiya ba tukun amma suna daraja Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. (A. M. 13:16) Mujallar Awake! tana mai da hankali ne ga waɗanda ba su san Littafi Mai Tsarki da kuma Jehobah Allah na gaskiya sosai ba.—A. M. 17:22, 23.

13. Me ya burge ka sosai game da mujallunmu? (Ku tattauna akwatin nan “ Littattafan da Aka Fi Bugawa a Faɗin Duniya.”)

13 Daga farkon shekara ta 2014, an wallafa mujallar Awake! sama da kofi miliyan 44 da kuma Hasumiyar Tsaro wajen miliyan 46 a kowane wata. An fassara Awake! zuwa harsuna wajen 100, ita kuma Hasumiyar Tsaro an fassara ta zuwa harsuna fiye da 200. Hakan ya sa suka zama mujallun da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a faɗin duniya! Bai kamata waɗannan gagaruman abubuwan da ake cim ma su ba mu mamaki ba. Me ya sa? Domin mujallun suna ɗauke ne da saƙon da Yesu ya ce za a yi wa’azinsa a dukan duniya.—Mat. 24:14.

14. Mene ne muka rarraba da ƙwazo, kuma me ya sa?

14 Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1896, Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun canja sunan da suka yi rajistar littattafanmu da kuma Littafi Mai Tsarki da shi zuwa Watch Tower Bible and Tract Society. Wannan canjin ya kawo sunan Littafi Mai Tsarki a cikin sunan kuma hakan ya dace domin Littafi Mai Tsarki ne ainihin littafin da ake amfani da shi wajen yaɗa bishara ta Mulkin Allah. (Luk 24:27) Saboda haka, sun nuna ƙwazo wajen rarraba Littafi Mai Tsarki kuma sun ƙarfafa mutane su karanta shi. Alal misali, a shekara ta 1926, mun buga Nassosin Helenanci na Kirista mai suna The Emphatic Diaglott wanda Benjamin Wilson ya fassara. Daga shekara ta 1942, mun buga kuma mun rarraba juyin King James Version wajen kofi 700,000. Shekaru biyu bayan haka, mun soma buga juyin American Standard Version, wanda yake ɗauke da sunan Allah a wurare 6,823. Kafin shekara ta 1950, mun riga mun rarraba sama da kofi 250,000.

15, 16. (a) Me yake burge ka game da juyin New World Translation? (Ku tattauna akwatin nan “ Hanzarta Fassarar Littafi Mai Tsarki.”) (b) Ta yaya za ka bari Jehobah ya motsa ka?

15 A shekara ta 1950, an fitar da juyin Nassosin Helenanci na Kirista mai suna New World Translation of the Christian Greek Scriptures. A shekara ta 1961 kuma, an fitar da cikakken Littafi Mai Tsarki mai jigo New World Translation of the Holy Scriptures. Wannan juyin ya ɗaukaka Jehobah domin ya mai da sunan Allah a daidai wuraren da sunan ya bayyana a Nassosin Ibrananci na asali. Sunan Allah ya kuma bayyana sau 237 a juyin Nassosin Helenanci. An sha juya New World Translation of the Holy Scriptures kuma a shekara ta 2013 an sake juya ta don a tabbatar da cewa fassarar ta yi daidai kuma tana da sauƙin karantawa. Kafin shekara ta 2013, an buga cikakke ko rabin juyin New World Translation sama da kofi miliyan 201 a harsuna 121.

16 Mene ne wasu suka ce bayan sun karanta wannan juyin Littafi Mai Tsarki a nasu yaren? Wani ɗan ƙasar Nepal ya ce: “Tsohon juyin Littafi Mai Tsarki na yaren Nepal yana da wuyar fahimta domin an yi amfani da kalmomi masu wuya ainun. Amma a yau, mun fahimci Littafi Mai Tsarki sosai, domin an fassara shi da kalmomin da muke yin amfani da su yau da kullum.” Sa’ad da wata mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta soma karanta juyin Littafi Mai Tsarki a harshen Sango, sai ta fashe da kuka kuma ta ce, “Wannan shi ne ainihin yaren da yake motsa ni sosai.” Kamar wannan matar, kowannenmu zai iya barin Jehobah ya motsa mu ta wajen muna karanta Kalmarsa kowace rana.—Zab. 1:2; Mat. 22:36, 37.

Yin Godiya don Tanadin Kayan Aiki da Kuma Koyarwa

17. Ta yaya za ka nuna cewa kana godiya don koyarwa da kuma kayan aikin da aka yi mana tanadinsu, kuma wane sakamako ne za ka samu ta yin hakan?

17 Shin kana godiya don koyarwa da kuma kayan aikin da Sarkinmu Yesu Kristi ya yi mana tanadinsu? Shin kana keɓe lokaci don ka karanta littattafan da ƙungiyar Jehobah ta wallafa kuma kana amfani da abin da ka karanta don ka taimaka wa wasu? Idan kana yin hakan, za ka zama kamar wata ’yar’uwa mai suna Opal Betler, wadda ta yi baftisma a ranar 4 ga Oktoba, 1914. ’Yar’uwar ta ce: “Da daɗewa ni da maigidana [Edward] mun yi amfani da garmaho da kuma katuna don yin wa’azi. Mun yi wa’azi gida-gida muna rarraba littattafai da ƙasidu da kuma mujallu. Mun yi kamfen muna rarraba warƙoƙin da ke ɗauke da saƙon Littafi Mai Tsarki. Daga baya, an koya mana yadda za mu riƙa yin . . . [abin da yanzu ake kira koma ziyara] da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen da suke son saƙonmu. Na shagala da waɗannan ayyukan sosai a rayuwata kuma ina farin ciki matuƙa.” Yesu ya yi alkawari cewa mabiyansa za su shagala da yin shuki da girbi kuma za su yi farin ciki tare. Kamar Opal, miliyoyin mutane suna shaida cikar wannan alkawarin.—Karanta Yohanna 4:35, 36.

18. Wane gata ne muke da shi?

18 Mutane da yawa da ba su riga sun zama bayin Sarkin ba tukun suna iya yi wa mutanen Allah kallon marasa ilimi da kuma “talakawa.” (A. M. 4:13) Amma ka yi tunani a kan wannan, Sarkin ya yi amfani da mutanensa da ake musu kallon marasa ilimi wajen buga littattafan da aka fi fassarawa da kuma rarrabawa a faɗin duniya! Mafi muhimmanci ma, ya koyar da mu kuma ya motsa mu mu yi amfani da waɗannan kayan aikin don yaɗa bishara ga mutane a dukan al’umma. Babu shakka, muna da babban gata na yin aiki tare da Kristi wajen shuka iri na gaskiya da kuma girbe almajirai.

a A cikin shekaru goma da suka shige kurum, bayin Jehobah sun wallafa littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki sama da biliyan 20. Ƙari ga haka, sama da mutane biliyan biyu da miliyan ɗari bakwai da ke amfani da Intane za su iya shiga dandalinmu na jw.org.

b Wasu littattafan nazari da suka taimaka wa masu shela su koyar da gaskiya su ne The Harp of God (an buga shi a shekara ta 1921), “Let God Be True” (an buga shi a shekara ta 1946), Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya (an buga shi a shekara ta 1982), da Sanin da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada (an buga shi a shekara ta 1995).

c Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuli, 2013, shafi na 23 sakin layi na 13, wadda ta tattauna sabuwar fahimtarmu a kan waɗanda suke cikin “iyalin gidan” Kristi.