Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 11

Yin Gyara a Dabi’a Ya Nuna Cewa Allah Mai Tsarki Ne

Yin Gyara a Dabi’a Ya Nuna Cewa Allah Mai Tsarki Ne

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda Sarkin ya koya wa talakawansa su bi ƙa’idodin Allah game da ɗabi’a

Ka kwatanta a zuci cewa kana shiga ƙofar farfajiyar haikali mai girma na Jehobah

1. Mene ne Ezekiyel ya gani da ya burge mu sosai?

 YAYA za ka ji idan aka ba ka damar ganin abin da annabi Ezekiyel ya gani shekaru 2,500 da suka gabata? A ce kana gab da shiga cikin wani babban haikali mai walƙiya. Ga wani mala’ika mai alfarma yana jiranka don ya zagaya da kai a cikin haikalin. Ka hau matakalu bakwai da za su kai ka ɗaya daga cikin ƙofofi uku da ke haikalin. Waɗannan ƙofofin sun burge ka. Tsayinsu wajen kafa 100 ne. A bakin ƙofar, ka ga ɗakunan tsaro kuma ginshiƙan suna da zanen itatuwan giginya masu kyan gaske.—Ezek. 40:1-4, 10, 14, 16, 22; 41:20.

2. (a) Mene ne haikalin da aka bayyana a ru’ya yake wakilta? (Ka kuma duba ƙarin bayani.) (b) Mene ne za mu iya koya daga fasalolin kofofin haikalin?

2 Wannan shi ne babban haikali na alama da aka bayyana a cikin wahayi. Ezekiyel ya bayyana wannan wahayin dalla-dalla a cikin surori na 40 zuwa 48 na littafin annabci da ke ɗauke da sunansa. Wannan haikalin yana wakiltar tsarin da Jehobah ya kafa don bauta ta gaskiya. Kowane fasali na haikalin nan yana da alaƙa da ibadarmu a waɗannan kwanaki na ƙarshe. a Mene ne waɗannan manyan ƙofofi suke wakilta? Suna tuna mana cewa wajibi ne waɗanda suke so su bi tsarin da Jehobah ya kafa don bauta ta gaskiya su bi ƙa’idodinsa masu kyau da babu kamar su. Zane-zanen da ke jikin bangon ma suna wakiltar abu ɗaya da ƙofofin, domin a cikin Littafi Mai Tsarki, ana amfani da itatuwan giginya wajen kwatanta adalci. (Zab. 92:12) Ɗakunan tsaron kuma fa? Hakika, waɗanda suka ƙi bin ƙa’idodin da Allah ya kafa ba za su sami damar shiga wannan kyakkyawar hanyar bauta ta gaskiya ba.—Ezek. 44:9.

3. Me ya sa mabiyan Kristi suke bukatar gyara a kai a kai?

3 A wace hanya ce wannan wahayin da Ezekiyel ya gani ya cika? Kamar yadda muka koya a Babi na 2, Jehobah ya yi amfani da Kristi wajen yi wa mutanensa gyara a wata hanya ta musamman, daga shekara ta 1914 zuwa farkon shekara ta 1919. Shin ya daina gyarar ne bayan wannan lokacin? A’a! Tun daga ƙarnukan da suka gabata har zuwa yau, Kristi ya ci gaba da ɗaukaka ƙa’idodin Jehobah masu tsarki a batun ɗabi’a. Shin mabiyansa sun bukaci wannan gyarar kuwa? Ƙwarai kuwa. Domin yayin da Kristi yake janye mabiyansa daga cikin wannan duniya mai mummunar ɗabi’a da ke kama da taɓo, Shaiɗan yana ƙoƙarin mayar da su cikin wannan taɓon. (Karanta 2 Bitrus 2:20-22.) Bari mu bincika hanyoyi uku da aka yi wa Kiristoci na gaskiya gyara. Da farko, za mu tattauna wasu gyara da suka shafi ɗabi’a, sa’an nan mu tattauna wani mataki da aka ɗauka don a sa ƙungiyar Jehobah ta kasance da tsabta, kuma a ƙarshe, za mu tattauna batun da ya shafi tsarin iyali.

Gyara da Suka Shafi Ɗabi’a

4, 5. Wace dabara ce Shaiɗan ya daɗe yana amfani da ita, kuma da wane sakamako?

4 Tun da daɗewa, mutanen Jehobah sun yi sha’awar kasancewa da ɗabi’a mai kyau. Saboda haka, suna bin umurni da ake bayarwa game da hakan. Ku yi la’akari da misalan da ke gaba.

5 Lalata. Jima’i kyauta ce da Jehobah ya ba ma’aurata don su more a hanyar da ta dace. Amma Shaiɗan yana ƙoƙari ya mai da wannan kyakkyawar kyautar wani abu da zai ɓata wa Allah rai ta wurin yin amfani da ita don jarraba mutanen Allah. Shaiɗan ya yi amfani da wannan dabarar a zamanin Balaam, kuma ya yi nasara. A yau ma, yana yin amfani da ita sosai kuma yana samun nasara.—Lit. Lis. 25:1-3, 9; R. Yoh. 2:14.

6. Wane wa’adi ne aka wallafa a cikin Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona, yaya aka yi amfani da shi kuma me ya sa aka daina amfani da wa’adin? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

6 Domin a kāre mutanen Allah daga dabarun Shaiɗan, an wallafa wannan wa’adi a cikin fitowar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta 15 ga Yuni, 1908: “A kowane lokaci, kuma a kowane wuri, idan ina tare da wanda jinsinmu ba ɗaya ba a wurin da ba za a iya ganinmu ba, kuma ba matata ko mijina ba ne, zan bi da mutumin yadda na saba bi da shi ko ita a cikin jama’a.” b Duk da cewa ba a tilasta wa ’yan’uwa su ɗauki wannan wa’adin ba, amma da yawa cikinsu sun ɗauki wa’adin kuma sun aika da sunayensu don a buga a cikin Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona. Shekaru da yawa bayan haka, an gano cewa ko da yake wannan wa’adin yana taimaka wa ’yan’uwa da yawa, wasu sun mai da shi maganar baki kawai. Shi ya sa aka daina amfani da wa’adin. Amma, ƙungiyar ta ci gaba da bin ƙa’idodin wannan wa’adin.

7. Wace matsala ce aka tattauna a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1935, kuma wace ƙa’ida ce aka nanata?

7 Shaiɗan ya ci gaba da ƙoƙartawa don ya ɓata ɗabi’ar mutanen Allah. Saboda haka, a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1935, an tattauna wata matsalar da ta zama ruwan dare tsakanin mutanen Allah. Wasu suna gani kamar muddin suna yin wa’azi, suna da ’yancin yin abin da suka ga dama a wasu fannonin rayuwa. Hasumiyar Tsaro ta bayyana sarai cewa: “Ya kamata kowannenmu ya tuna cewa ba yin wa’azi ne kawai farilla da ake bukatar Kirista ya cika ba. Shaidun Jehobah su ne wakilan Allah, saboda haka, wajibi ne su wakilce shi da mulkinsa a hanyar da ta dace.” Sa’an nan, talifin ya bayyana umurnan Allah game da aure da kuma jima’i dalla-dalla. Hakan ya taimaka wa mutanen Allah su ‘guji fasiƙanci.’—1 Kor. 6:18.

8. Me ya sa an daɗe ana nanata ma’anar kalmar Helenanci da take nufin fasiƙanci a cikin Hasumiyar Tsaro?

8 A shekarun baya bayan nan, an nanata a cikin Hasumiyar Tsaro sau da sau ainihin ma’anar kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a cikin sabon alkawari na Littafi Mai Tsarki don fasiƙanci, wato por·neiʹa. Ba jima’i ne kaɗai wannan kalmar take nufi ba. Amma ta ƙunshi kowace irin ƙazanta ta lalata da ake yi a gidan karuwai. Da haka, an kāre mabiyan Kristi daga lalatar da ta yaɗu a duniya.—Karanta Afisawa 4:17-19.

9, 10. (a) Wane batu da ya shafi ɗabi’a ne aka tattauna a cikin Hasumiyar Tsaro a 1935? (b) Mece ce koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan shan giya?

9 Yin Maye. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris 1935, ta tattauna wani batu dabam da ya shafi ɗabi’ar mutanen Allah. Ta ce: “An lura cewa wasu suna zuwa wa’azi ko kuma yin wasu hidimomi a cikin ikilisiya bayan sun sha [giya]. A wane yanayi ne Littafi Mai Tsarki ya amince da shan giya? Zai dace bawan Allah ya riƙa shan giya har hakan ya shafi hidimarsa ga Ubangiji?”

10 Amsar ta nuna irin ra’ayin da Kalmar Allah take so mu kasance da shi idan ya zo ga batun shan giya. Littafi Mai Tsarki bai hana shan giya daidai wa daida ba, amma ya haramta buguwa. (Zab. 104:14, 15; 1 Kor. 6:9, 10) Game da batun shan giya kafin mutum ya yi hidimar Allah kuma, an sha tuna wa bayin Allah labarin ’ya’yan Haruna, waɗanda Allah ya halaka domin sun miƙa haramtacciyar hadaya a kan bagadin Allah. Jim kaɗan bayan mutuwarsu, labarin ya nuna cewa Allah ya ba da dokar da ta hana firistoci shan giya yayin da suke hidimomi masu tsarki. Hakan ya nuna cewa wataƙila giya ce ta sa ’ya’yan Haruna suka yi wannan abin da bai dace ba. (Lev. 10:1, 2, 8-11) Saboda wannan ƙa’idar, zai dace mabiyan Kristi a yau su guji shan giya yayin da suke yin hidimomi da suka shafi ibada.

11. Ta yaya ƙarin haske da bayin Allah suka samu a kan yawan shan giya da kuma maye ya zama albarka?

11 A shekarun baya bayan nan, mabiyan Kristi sun sami ƙarin haske game da yawan shan giya. Muna godiya domin ƙungiyar Jehobah ta taimaka wa ’yan’uwa da yawa su shawo kan wannan halin kuma su ji daɗin rayuwarsu. An taimaka wa wasu kuma su guji wannan halin. A gaskiya, bai kamata wani ya zub da mutuncinsa ko ɓata zumunci da iyalinsa da kuma ibadarsa ga Jehobah saboda shan giya ba.

“Ba ma tsammanin Ubangijinmu Kristi zai busa taba ko kuma ya saka wani abu a bakinsa da zai ƙazantar da shi.”​—C. T. Russell

12. Mene ne ra’ayin mabiyan Kristi game da taba tun kafin somawar kwanaki na ƙarshe?

12 Shan taba. Tun kafin a shiga kwanaki na ƙarshe, bayin Kristi sun soma yin tir da shan taba. A shekarun da suka gabata, wani ɗan’uwa tsoho, mai suna Charles Capen ya faɗi abin da ya faru tsakanin shi da Charles Taze Russell a rana ta farko da suka haɗu fiye da shekaru ɗari yanzu. A wannan lokacin, Capen yana da shekaru 13, kuma shi da ’yan’uwansa guda uku suna tsaye a kan matakalar hedkwatarmu ta farko a Amirka, wato Bible House a Allegheny, Pennsylvania. Yayin da Russell ya zo wucewa kusa da su, sai ya tambaye su: “In ji dai ba taba kuke sha ba? Ina jin warin taba.” Sai suka tabbatar masa cewa ba taba suke sha ba. Hakika, wannan ya bayyana musu irin ra’ayin da yake da shi game da shan taba. A cikin Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 1 ga Agusta, 1895, Ɗan’uwa Russell ya yi kalami a kan littafin 2 Korintiyawa 7:1, cewa: “Ban ga yadda Kirista zai ɗaukaka Allah ko kuma kyauta wa kansa ta wajen shan taba ba sam. . . . Ba ma tsammanin Ubangijinmu Kristi zai busa taba ko kuma ya saka wani abu a bakinsa da zai ƙazantar da shi.”

13. Wane ƙarin haske a batun ɗabi’a ne aka samu a 1973?

13 A shekara ta 1935, Hasumiyar Tsaro ta kira taba “ƙazantacciyar ciyawa” kuma ta bayyana cewa duk wanda yake tauna ko kuma shan taba ba zai ci gaba da yin hidima a Bethel ko hidimar majagaba ko kuma hidimar mai kula mai ziyara ba. A shekara ta 1973, an sami ƙarin haske a kan wannan batun. A cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, an bayyana cewa idan wani Mashaidi yana shan taba kuma ya ƙi ya daina, ba zai ci gaba da zama Mashaidin Jehobah ba. Me ya sa? Domin hakan yana gurɓata mutum, baya nuna ƙauna, kuma yana jawo mutuwa. Duk waɗanda suka ƙi daina shan taba za a yi musu yankan zumunci. c Hakika, Kristi ya ɗauki wani gagarumin mataki wajen yi wa mabiyansa gyara.

14. Wace ƙa’ida ce Allah ya kafa a kan jini, kuma ta yaya ba da jini ya zama gama-gari?

14 Yin amfani da jini a hanya marar kyau. A zamanin Nuhu, Allah ya haramta cin jini. Ya maimaita hakan a cikin Dokar da ya ba al’ummar Isra’ila, kuma ya sake ba da wannan umurni ga Kiristoci na gaskiya cewa su “hanu daga . . . jini.” (A. M. 15:20, 29; Far. 9:4; Lev. 7:26) Abin baƙin ciki, Shaiɗan ya buɗe wa mutane da yawa hanyar ƙeta wannan ƙa’idar da Allah ya ba da. A ƙarni na 19, likitoci sun soma gwada yin ƙarin jini, kuma bayan sun gano ire-iren jini, sai yin ƙarin jini ya zama gama-gari. A shekara ta 1937, an soma tara jini da kuma adana shi, kuma Yaƙin Duniya na Biyu ya bunƙasa yin ƙarin jini sosai. Hakan ya sa yin ƙarin jini ya yaɗu zuwa ko’ina a faɗin duniya.

15, 16. (a) Mene ne matsayin Shaidun Jehobah a batun ƙarin jini? (b) Wane taimako ne Kiristoci suka samu a batun karɓan ƙarin jini da kuma jinya da ba ta ƙunshi jini ba? Wane sakamako ne aka samu?

15 Tun shekara ta 1944, Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa karɓan ƙarin jini wata hanya ce ta cin jini. A shekara ta 1945, an ƙara bayyana matakin da ƙungiyarmu ta ɗauka a batun karɓan ƙarin jini. A shekara ta 1951, an wallafa jerin tambayoyi da kuma amsoshi don a taimaka wa bayin Allah su san yadda za su bi da likitoci a batun ƙarin jini. A duk faɗin duniya, Kiristoci sun yi tsayin daka wajen ƙin karɓan ƙarin jini duk da yawan ba’a da hamayya da kuma tsanantawa da ake musu. Amma, Kristi ya ci gaba da sa ƙungiyarsa ta tanadar da abubuwan da za su taimaka musu. An wallafa ƙasidu da talifofin Hasumiyar Tsaro dabam-dabam da suka bayyana wannan batun dalla-dalla.

16 A shekara ta 1979, wasu dattawa sun soma ziyartar asibitoci don su bayyana wa likitoci matsayinmu da Nassosin da suka sa muka ɗauki wannan matsayin da kuma wasu hanyoyin jinya da ba su ƙunshi yin ƙarin jini ba. A shekara ta 1980, an horar da dattawa 39 a Amirka musamman don wannan aikin. A kwana a tashi, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta yarda a kafa Kwamitin Hulɗa da Asibitoci a duk faɗin duniya. Wannan tsarin ya cim ma wani abin kirki kuwa? A yau, da akwai dubban likitoci da masu fiɗa da masu yin allurar barci da dai sauransu da suke ba da haɗin kai ga Shaidu majiyyata ta wajen yi musu jinya ba tare da ƙarin jini ba. Ana samun ƙarin asibitoci masu yin jinya ba tare da yin ƙarin jini ba kuma wasu daga cikinsu sun ce irin wannan jinyar ce ta fi inganci. Hakika, yin tunani a kan yadda Yesu ya kāre mabiyansa duk da cewa Shaiɗan yana ƙoƙarin ya gurɓata su yana burge mu, ko ba haka ba?—Karanta Afisawa 5:25-27.

Asibtoci da yawa sun amince da yin jinya ba tare da jinni ba kuma wasu sun ce wannan ita ce jinya da ta fi kyau

17. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don gyarar da Kristi yake yi wa mabiyansa?

17 Zai dace mu yi wa kanmu tambayar da ke gaba, ‘Shin ina godiya don gyarar da Kristi yake yi wa mabiyansa da kuma yadda yake koyar da su su bi ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a?’ Idan haka ne, ya kamata mu riƙa tuna cewa Shaiɗan yana ƙoƙari ya sa mu daina bin ƙa’idodin Allah don mu yi nisa da Jehobah da kuma Yesu. Amma, ƙungiyar Jehobah tana ba mu gargaɗi a kai a kai game da rashin ɗabi’a da ta yaɗu a duniya da kuma yadda za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan. Ya kamata mu ci gaba da kasancewa a faɗake, mu riƙa ji da kuma bin waɗannan gargaɗi da za su taimaka mana.—Mis. 19:20.

Yadda Ake Kāre Ikilisiya Daga Zargi

18. Wace tunasarwa ce game da waɗanda suka daina bin ƙa’idodin Allah da gangan muka samu daga wahayin Ezekiyel?

18 Gyara ta biyu da aka yi a batun ɗabi’a ta ƙunshi matakan da aka ɗauka don ikilisiya ta ci gaba da kasancewa da tsarki. Abin taƙaici shi ne, ba dukan waɗanda suka keɓe kansu ga yin nufin Allah kuma suka soma bin ƙa’idodinsa game da ɗabi’a ne suka cika alkawarinsu ba. Wasu sun canja ra’ayinsu kuma suka daina bin waɗannan ƙa’idodin da gangan. Mene ne za a yi da irin waɗannan mutanen? Wahayin haikali da aka saukar wa Ezekiyel, wanda aka tattauna a farkon wannan babin ya bayyana abin da ya kamata a yi da su. Ka tuna da manyan ƙofofin da aka ambata a wahayin. A bakin kowace ƙofa, akwai ɗakunan tsaro. Matsara suna tsare haikalin domin su hana “mara-kaciya a zuci” shiga ciki. (Ezek. 44:9) Hakan ya tuna mana cewa bauta ta gaskiya gata ne kuma waɗanda suka ƙudura su bi ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a ne kawai za su iya morarsa. Hakazalika, ba kowa ba ne yake da gatan bauta wa Allah tare da ’yan’uwa Kiristoci a yau.

19, 20. (a) Ta yaya Kristi ya yi wa mabiyansa gyara da sannu-sannu a yadda suke shari’anta waɗanda suka yi zunubi mai tsanani? (b) Waɗanne dalilai uku ne suke sa a yi yankan zumunci wa waɗanda suka yi zunubi kuma suka ƙi tuba?

19 Tun shekara ta 1892, Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta ce dukan Kiristocin da suka musanta cewa Kristi ya sadaukar da ransa don ya fanshi ’yan Adam, ko da sun yi hakan kai tsaye ko a’a, hakkinmu ne mu yi musu yankan zumunci. (Karanta 2 Yohanna 10.) A shekara ta 1904, littafin nan The New Creation ya bayyana cewa waɗanda suka ci gaba da aikata mummunan hali za su iya gurɓata ikilisiya. A dā, dukan ’yan’uwa a cikin ikilisiya ne suke haɗuwa don su binciki mutumin da ya yi zunubi mai tsanani. Amma, hakan ba ya cika faruwa. A shekara ta 1944, Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa ’yan’uwa da aka danƙa wa hakkin yin ja-goranci a cikin ikilisiya ne kaɗai za su riƙa kula da wannan batun. A shekara ta 1952, an wallafa wata Hasumiyar Tsaro da ta bayyana matakan da ya kamata a bi da kuma dalili na musamman da zai sa a yi wa mutum yankan zumunci bisa ga Littafi Mai Tsarki. Wannan dalilin shi ne, don a sa ikilisiya ta kasance da tsabta.

20 Tun daga wannan lokacin, Kristi ya ci gaba da taimaka wa mabiyansa su sami ƙarin haske kuma su yi gyara a kan yadda suke wa waɗanda suka yi zunubi mai tsanani shari’a. Ana horar da dattawa Kiristoci da kyau don su yi koyi da Jehobah a yin shari’a, ta wajen nuna adalci da kuma jin ƙai daidai wa daida. A yau, mun fahimci aƙalla dalilai uku na yi wa waɗanda suka yi zunubi kuma suka ƙi tuba yankan zumunci. Dalilan su ne: (1) don kada a zargi sunan Jehobah, (2) don a kāre ikilisiya daga mummunan tasirin zunubi mai tsanani, kuma na (3) don a sa mai zunubin ya tuba, idan zai yiwu.

21. Ta yaya yankan zumunci ya zama albarka ga bayin Allah a yau?

21 Kana ganin yadda yankan zumunci ya zama albarka ga mabiyan Kristi a yau kuwa? A ƙasar Isra’ila ta dā, sau da yawa mugun halin masu aikata laifi yakan shafi al’ummar, a wani lokaci ma waɗanda suke bin gurbinsu sukan fi waɗanda suke ƙaunar Jehobah da kuma yin nufinsa yawa. A sakamakon haka, al’ummar ta jawo zargi ga sunan Jehobah sau da yawa kuma hakan ya sa ta rasa tagomashinsa. (Irm. 7:23-28) A yau, Jehobah yana sha’ani ne da maza da mata da suka san muhimmancin dangantakarsu da shi. Tun da yake ana fitar da masu zunubi da suka ƙi tuba a tsakaninmu, Shaiɗan ba zai iya yin amfani da su wajen gurɓata ikilisiya ko kuma ɓata suna mai kyau da take da shi ba. A matsayin rukuni, muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da ba mu goyon baya. Ka tuna da alkawarin da Jehobah ya yi cewa: “Ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki.” (Isha. 54:17, Littafi Mai Tsarki) Shin muna ba da goyon baya ga dattawa da suke ɗaukan nawayar yin shari’a a cikin ikilisiya?

Yadda Za Mu Ɗaukaka Wanda Ya Ba Kowane Iyali Suna

22, 23. Me ya sa muke nuna godiya sosai ga Kiristoci da suka rayu wajen shekaru 100 da suka gabata, amma me ya nuna cewa sun bukaci su daidaita ra’ayinsu game da iyali?

22 Hanya ta uku da Kristi yake yi wa mabiyansa gyara ita ce a batun aure da kuma iyali. Shin an gyara ra’ayinmu game da iyali kuwa? Hakika. Alal misali, a duk lokacin da muka karanta yadda bayin Allah da suka rayu wajen shekaru 100 da suka gabata suka sadaukar da ransu, hakan yana burge mu sosai. Muna godiya sosai domin yadda suka saka hidimar Allah kan gaba a rayuwarsu. Amma a wasu lokuta, sukan wuce gona da iri. Ta yaya?

23 A yawancin lokuta, ’yan’uwa maza ma’aurata sukan yarda su yi aikin masu kula masu ziyara ko kuma wata hidima dabam nesa da gida na tsawon watanni da yawa ba tare da matansu ba. A wasu lokuta kuma, ana yawan ƙarfafa ’yan’uwa kada su yi aure kuma ba a cika tattauna yadda Kiristoci za su kyautata aurensu. Shin haka yanayin yake kuwa a yau? A’a!

Bai kamata ’yan’uwa su yi hidimar da za ta nisanta su da iyalansu ba

24. Ta yaya Kristi ya taimaki mutanensa su daidaita ra’ayinsu game da yin aure da kuma iyali?

24 A yau, bai kamata ’yan’uwa su yi hidimar da za ta nisanta su da iyalansu ba. (Karanta 1 Timotawus 5:8.) Ƙari ga haka, Kristi ya tabbatar da cewa mabiyansa a duniya suna samun shawarwari masu kyau a kai a kai daga Littafi Mai Tsarki a kan batun aure da kuma iyali. (Afis. 3:14, 15) A shekara ta 1978, an wallafa littafin nan Ka Sa Zaman Iyalinka Ta Sami Farinciki kuma shekaru 18 bayan haka, an wallafa littafin nan Asirin Farinciki na Iyali. Ban da haka ma, an ci gaba da wallafa talifofi da yawa a cikin Hasumiyar Tsaro don su taimaka wa ma’aurata su riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a yadda suke sha’ani da juna.

25-27. Ta yaya aka kula da bukatun yara da kuma matasa?

25 Yara da matasa kuma fa? Su ma an mai da hankali ga bukatunsu. Tun da daɗewa, ƙungiyar Jehobah tana tanadar da abubuwa masu ban taimako jifa-jifa domin yara manya da ƙanana. Amma yanzu, ana wallafa talifofi dabam-dabam a kai a kai. Alal misali, daga shekara ta 1919 zuwa 1921, an wallafa talifin nan Juvenile Bible Study” (Nazarin Littafi Mai Tsarki don Matasa) a cikin mujallar The Golden Age. Bayan haka, an wallafa ƙasidar nan The Golden Age ABC a shekara ta 1920 da kuma littafin nan Children a shekara ta 1941. A tsakanin shekara ta 1970 zuwa 1979, an wallafa littattafan nan Saurarawa ga Babban Malamin da Your Youth—Getting the Best out of It, da kuma Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1982, an soma wallafa jerin talifofin nan “Young People Ask” a cikin mujallar Awake! kuma hakan ya kai ga fitar da littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work a shekara ta 1989.

An yi farin cikin samun kasidar nan Abin da Na Koya a Littafi Mai Tsarki a taron gunduma a kasar Jamus

26 A yanzu haka, muna da kundi biyu na littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work kuma ana ci gaba da wallafa jerin talifofin a dandalinmu na jw.org. Ƙari ga haka, muna da littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami. Akwai abubuwa da yawa a dandalinmu don yara da matasa, kamar su labarin wani daga Littafi Mai Tsarki, ayyuka don nazarin Littafi Mai Tsarki, wasannin watsa ƙwaƙwalwa, bidiyoyi, labaran Littafi Mai Tsarki cikin hotuna da kuma darussa daga Littafi Mai Tsarki don yara ’yan shekara uku zuwa ƙasa. Hakika, tun daga lokacin da Kristi ya rungumi yara har zuwa yau, bai canja ra’ayinsa game da su ba. (Mar. 10:13-16) Yana so mu ƙaunace su kuma mu koya musu ƙa’idodin Allah sosai.

27 Yesu yana so a kāre yara daga lahani. Domin ɗabi’a tana daɗa taɓarɓarewa a duniyar nan, yin lalata da yara ya zama gama-gari. Saboda haka, an wallafa littattafai da kuma wasu abubuwa da suke ɗauke da shawarwari masu kyau don a taimaka wa iyaye su kāre ’ya’yansu daga wannan mummunan halin. d

28. (a) Kamar yadda aka kwatanta a wahayin Ezekiyel, mene ne muke bukatar yi idan muna so mu bauta wa Allah cikin gaskiya? (b) Mene ne ƙudurinka?

28 Babu shakka, idan muka yi tunani a kan yadda Kristi ya ci gaba da koyar da mabiyansa da kuma yi musu gyara don su iya bin ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a kuma su amfana daga yin hakan, wannan yana sa mu farin ciki, ko ba haka ba? Ka sake yin tunani a kan haikalin da Ezekiyel ya gani a wahayi. Ka tuna da manyan ƙofofin nan? Hakika, wannan haikalin ba na zahiri ba ne. Amma, muna ganin ya wanzu kuwa da gaske? Zuwa Majami’ar Mulki da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin wa’azi kawai ba za su sa mu shiga wannan haikalin ba, domin waɗannan ayyukan na zahiri ne. Munafuki zai iya yin dukan waɗannan abubuwan ba tare da shiga wannan haikalin ba. Amma idan muna yin waɗannan abubuwan, muna bin ƙa’idodin Jehobah game da ɗabi’a kuma muna bauta masa ba tare da munafunci ba, za mu shiga wannan haikalin, wanda shi ne wuri mafi tsarki kuma mu yi hidima a wurin. Wannan haikalin shi ne shirin da Jehobah ya yi don bauta ta gaskiya. Bari mu ɗaukaka wannan babban gatan da dukan zuciyarmu a kowane lokaci kuma mu ci gaba da kasancewa da tsarki kamar Jehobah ta wajen bin ƙa’idodinsa!

a A shekara ta 1932, Kundi na 2 na littafin nan Vindication ya bayyana cewa annabcin Littafi Mai Tsarki game da mayar da mutanen Allah ƙasarsu ya cika a zamaninmu a kan shafaffun Kiristoci ne, ba al’ummar Isra’ila ba. Waɗannan annabcin suna nuni ne ga lokacin da za a sake gano bauta ta gaskiya. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1999, ta bayyana cewa wahayin haikali da Ezekiyel ya gani annabci ne game da lokacin da za a sake gano bauta ta gaskiya, saboda haka, yana cika a wata muhimmiyar hanya a waɗannan kwanaki na ƙarshe.

b Wa’adin ya haramta namiji da tamace su kasance su kaɗai a cikin ɗaki da ƙofa a rufe, sai dai idan su ma’aurata ne ko kuma dangi. An yi shekaru ana maimaita wannan wa’adin kowace rana a Ibadar Safiya da ake yi a gidajen Bethel.

c Yin amfani da taba a hanyar da ba ta dace ba ya haɗa da sha, sheƙa, taunawa, da kuma nomansa don waɗannan manufofin.

d Alal misali, ka duba babi na 32 na littafin nan Ka Koya Daga Wurin Babban Malami da kuma shafuffuka na 3-11 na mujallar Awake! na Oktoba, 2007.