Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 19

Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah

Aikin Gini da Ke Ɗaukaka Jehobah

MANUFAR WANNAN BABIN

Aikin gine-gine a faɗin duniya da ke tallafa wa Mulkin

1, 2. (a) Wane abu ne bayin Allah suke farin cikin yi tun da daɗewa? (b) Mene ne Jehobah yake ɗauka da tamani?

 BAYIN Jehobah masu aminci sun daɗe suna gina wuraren ibada da suke girmama sunansa kuma suna yin hakan da farin ciki. Alal misali, Isra’ilawa sun tanadar da kayayyakin gini hannu sake kuma sun gina mazauni da himma sosai.—Fit. 35:30-35; 36:1, 4-7.

2 Ba kayan gini ba ne suke ɗaukaka Jehobah, kuma ba su ne ya fi ɗauka da tamani ba. (Mat. 23:16, 17) Abubuwan da Jehobah yake ɗaukawa da tamani sosai su ne ibada da himma da kuma sadaukarwa da bayinsa suke yi domin waɗannan abubuwan suna ɗaukaka shi. (Fit. 35:21; Mar. 12:41-44; 1 Tim. 6:17-19) Hakan yana da muhimmanci sosai. Me ya sa? Domin gini yakan rushe. Alal misali, mazauni da kuma haikalin da aka gina a zamanin dā sun lalace. Ko da yake waɗannan ginin sun lalace, amma Jehobah bai manta da karimci da kuma himmar da bayinsa masu aminci suka nuna a lokacin da ake gina su ba.—Karanta 1 Korintiyawa 15:58; Ibraniyawa 6:10.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan babin?

3 Bayin Jehobah a yau ma sun yi aiki tuƙuru don su gina wuraren ibada. Kuma abin da muka cim ma a ƙarƙashin ja-gorancin Sarkinmu Yesu Kristi, yana da ban al’ajabi sosai! Hakika, Jehobah ya albarkaci ƙoƙarinmu. (Zab. 127:1) A wannan babin, za mu tattauna wasu daga cikin ayyukan gine-gine da aka yi da kuma yadda hakan ya ɗaukaka Jehobah. Za mu kuma karanta kalaman wasu da suka taimaka wajen cim ma wannan aikin.

Gine-ginen Majami’un Mulki

4. (a) Me ya sa muke bukatar ƙarin wuraren ibada? (b) Me ya sa aka harhaɗa wasu ofisoshin reshe? (Ka duba akwatin nan “ Dalilin Faɗaɗa Wasu Ofisoshin Reshe.”)

4 Kamar yadda aka tattauna a Babi na 16, Jehobah ya bukaci mu riƙa yin taro don mu yi masa ibada. (Ibran. 10:25) Abubuwan da muke koya a taronmu suna ƙarfafa bangaskiyarmu kuma suna sa mu daɗa ƙwazo a yin wa’azi. Yayin da kwanaki na ƙarshe suke ƙurewa, Jehobah yana hanzarta wannan aikin. Dubban mutane suna shigowa cikin ƙungiyarsa kowace shekara saboda wannan aikin. (Isha. 60:22) Yayin da talakawan Mulkin suke ƙaruwa, ana daɗa bukatar wuraren buga littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, muna bukatar ƙarin wuraren ibada.

5. Me ya sa wannan sunan “Majami’ar Mulki” ya dace? (Ka kuma duba akwatin nan “ Cocin The New Light.”)

5 A farko-farkon tarihin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, ɗaliban sun ga cewa suna bukata su soma gina wuraren yin taro. A jihar West Virginia da ke Amirka ne mai yiwuwa aka gina wurin ibada na farko a shekara ta 1890. Kafin shekara ta 1940, Shaidun Jehobah sun gina ko kuma gyara wuraren taro, amma ba a ba waɗannan wuraren takamaiman suna ba. A shekara ta 1935, Ɗan’uwa Rutherford ya kai ziyara a tsibirin Hawaii, inda ake gina wajen taro na ibada a ƙarƙashin ja-gorancin sabon ofishin reshe da aka gina a wurin. Sa’ad da aka tambayi Ɗan’uwa Rutherford sunan da ya kamata a ba wannan ginin, sai ya ce: “Kuna ganin ba zai fi dacewa mu kira shi ‘Majami’ar Mulki’ ba, tun da yake wa’azin bisharar Mulkin muke yi?” (Mat. 24:14) Sunan da aka ba wa wannan majami’ar ke nan. Ba da daɗewa ba, aka ba da wannan suna da ya dace ga yawancin wuraren ibada da bayin Jehobah suke amfani da su a faɗin duniya.

6, 7. Mene ne aka cim ma ta wajen gina Majami’un Mulki a cikin ƙanƙanin lokaci?

6 A tsakanin shekara ta 1970 zuwa 1979, bayin Jehobah sun bukaci Majami’un Mulki da yawa. Saboda haka, ’yan’uwa a Amirka sun ƙirƙiro hanyar gina Majami’un Mulki masu kyau da kuma inganci a cikin ’yan kwanaki. Daga lokacin zuwa shekara ta 1983, an gina irin waɗannan Majami’un Mulki wajen 200 a Amirka da Kanada. Domin a cim ma wannan aikin sosai, ’yan’uwa sun soma kafa kwamitocin gine-gine na yanki. Wannan tsarin ya cim ma manufarsa sosai, saboda haka ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta mai da shi tsari na dindindin a shekara ta 1986. A shekara ta 1987, an riga an kafa Kwamitocin Gine-gine na Yanki guda 60 a ƙasar Amirka. a A shekara ta 1992, an kafa Kwamitin Gine-gine na Yanki a ƙasar Ajantina da Afirka ta Kudu da Faransa da Jamus da Meziko da Ostareliya da kuma Sifen. Hakika, ’yan’uwa masu ƙwazo da suke gina Majami’un Mulki da Majami’un Manyan Taro sun cancanci mu ba su goyon baya, domin hidimar da suke yi sashe ne na ibada ga Jehobah.

7 Waɗannan Majami’un Mulki da ake gina su a cikin ’yan kwanaki sun zama shaida a yankunan da aka gina su. Alal misali, a ƙasar Sifen, an wallafa wannan kanun labari “Faith Moves Mountains” (Bangaskiya Tana Cim Ma Gagarumin Abu) a wata jarida. An yi wata tambaya a jaridar game da Majami’ar Mulkin da aka gina a birnin Martos cewa: “Ta yaya mutane masu ba da kai suka fito daga yankuna dabam-dabam [a ƙasar Sifen] zuwa birnin Martos don su gina wannan wuri mai kyau da tsari a cikin ƙanƙanin lokaci, a wannan duniyar da ke cike da masu son kai?” Wannan jaridar ta amsa tambayar ta wajen yin ƙaulin kalamin ɗaya daga cikin Shaidu da suka ba da kai don aikin. Ya ce: “Hakan ya yiwu ne domin Jehobah ne yake koyar da mu.”

Yin Gine-gine a Ƙasashe Masu Tasowa

8. Wane sabon tsari ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta kafa a shekara ta 1999, kuma me ya sa?

8 A ƙarshen ƙarni na 20, mutane da yawa a ƙasashe masu tasowa sun shigo ƙungiyar Jehobah. ’Yan’uwa a ƙasashen nan sun yi iyakacin ƙoƙarinsu don su gina wuraren taro. Amma a wasu ƙasashen, Shaidun Jehobah sun sha ba’a domin Majami’un Mulki da ke wuraren ba su kyan gani idan aka misalta su da wasu wuraren ibada. Daga shekara ta 1999, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta amince da wani tsarin da zai hanzarta gina Majami’un Mulki a ƙasashe masu tasowa. An yi amfani da kuɗaɗe daga ƙasashe masu arziki domin a sami ‘daidaituwa.’ (Karanta 2 Korintiyawa 8:13-15.) Kuma ’yan’uwa maza da mata daga ƙasashe da yawa sun ba da kai don su taimaka a yin ginin.

9. Wane aiki ne aka ɗauka cewa zai fi ƙarfinmu, amma me aka cim ma yanzu?

9 Da farko, kamar dai aikin zai fi ƙarfinmu. Rahoton da aka bayar a shekara ta 2001 ya nuna cewa ana bukatar Majami’un Mulki fiye da 18,300 a ƙasashe masu tasowa guda 88. Hakika, da taimakon Sarkinmu Yesu Kristi da kuma ruhun Allah, babu abin da zai gagare mu. (Mat. 19:26) A cikin wajen shekaru 15, wato daga shekara ta 1999 zuwa 2013, wannan sabon tsarin ya taimaka wa bayin Allah su gina Majami’un Mulki guda 26,849. b Jehobah ya ci gaba da yi ma wa’azin da muke yi albarka, shi ya sa a shekara ta 2013, an bukaci ƙarin Majami’un Mulki wajen 6,500 a waɗannan ƙasashen kuma a yanzu, ana bukatar darurruwan Majami’u a kowace shekara.

Gina Majami’un Mulki a ƙasashen da babu isashen kuɗi yana da nasa ƙalubale

10-12. Ta yaya gina sababbin Majami’un Mulki ya ɗaukaka Jehobah?

10 Ta yaya waɗannan sababbin Majami’un Mulkin da aka gina suka ɗaukaka sunan Jehobah? Wani rahoto daga ofishin reshe da ke ƙasar Zimbabuwe ya ce: “Wata guda bayan an gina sabuwar Majami’ar Mulki, yawan mutanen da ke halartan taro yakan ninka na dā sau biyu.” A ƙasashe da yawa, da alama cewa mutane suna jinkirin zuwa taronmu sai mun gina wurin ibada mai kyau. Da zarar an gina Majami’ar Mulki, tana cika nan da nan, har a bukaci wata sabuwa. Amma ba kyan fasalin Majami’un Mulki ba ne ke jawo mutane ga Jehobah ba. Ƙauna ta Kirista da maginan suke nunawa tana sa mutane su daraja ƙungiyar Jehobah. Ka yi la’akari da wasu misalai.

11 Indunusiya. Sa’ad da wani mutum da ya ga lokacin da ake gina wata Majami’ar Mulki ya gano cewa dukan maginan suna aikin ba da kai ne, sai ya ce: “Kun ba ni mamaki sosai! Na ga yadda kowannenku yake aiki da zuciya ɗaya kuma da farin ciki, ko da yake ba a biyan ku ko sisi. A ganina, babu wani addini kamar naku!”

12 Yukiren. Wata mata da ta saba wucewa kowace rana a inda ake gina wata Majami’ar Mulki ta kammala a zuciyarta cewa Shaidun Jehobah ne ma’aikatan kuma Majami’ar Mulki ce suke ginawa. Sai ta ce wa Shaidun: “Na ji labarin Shaidun Jehobah daga wajen ƙanwata wadda ita ma Mashaidiya ce. Yanzu da na ga yadda kuke aiki da kuma nuna ƙauna, na ƙudura in zama Mashaidiya.” Wannan matar ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma ta yi baftisma a shekara ta 2010.

13, 14. (a) Wane darasi ne ka koya daga matakin da wasu ma’aurata suka ɗauka bayan sun lura da abin da ke faruwa a inda ake gina Majami’ar Mulki? (b) Mene ne za ka iya yi domin wurin da kuke ibada ya ɗaukaka Jehobah?

13 Ajantina. Wasu ma’aurata sun je sun sami wani ɗan’uwa da ke ja-gorar ginin wata Majami’ar Mulki. Mijin ya ce, “Mun daɗe muna kallon yadda kuke gina wannan wurin, kuma . . . muna so mu koya game da Allah a cikin wannan ginin.” Sai ya yi tambaya, “Me ya wajaba mu yi don mu halarci taro a nan?” Ma’auratan sun amince a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su, amma kafin su yarda, sun ce sai an yi hakan da kowa a cikin iyalinsu. Hakika, ’yan’uwan sun yarda da hakan.

14 Mai yiwuwa ba ka sami gatan taimakawa a gina Majami’ar Mulkin da kake halartan taro a ciki ba, amma akwai abubuwa da dama da za ka iya yi da za su sa Majami’ar Mulkin ta ɗaukaka sunan Jehobah. Alal misali, za ka iya kasance da ƙwazo wajen gayyatar ɗalibanka da waɗanda kake koma ziyara wurinsu da kuma mutane a yankinku don su halarci taro a Majami’ar Mulki. Za ka kuma iya taimaka wajen share da kuma adana Majami’ar Mulkin. Idan ka yi ajiyar kuɗi, za ka iya ba da gudummawa don a kula da Majami’ar Mulkin da kake halartan taro a ciki ko kuma gina wasu Majami’un Mulki a wurare dabam-dabam a faɗin duniya. (Karanta 1 Korintiyawa 16:2.) Dukan waɗannan ayyukan suna ƙara ɗaukaka Jehobah.

Ma’aikata da Ke ‘Ba da Kansu da Yardan Rai’

15-17. (a) Su wane ne suke yin yawancin aikin ginin? (b) Mene ne ka koya daga kalaman ma’auratan da suka yi aikin gine-gine a ƙasashe da yawa?

15 Sa’ad da ake gina Majami’un Mulki da Majami’un Manyan Taro da kuma ofisoshin reshe, ’yan’uwa da ke yankin ne suke yin yawancin aikin da ake yi. Amma sau da yawa, ’yan’uwa maza da mata daga ƙasashe dabam-dabam da suka ƙware a aikin gini suna zuwa don su taimaka. Waɗannan ’yan’uwan suna tsara rayuwarsu a hanyar da za ta ba su damar yin aiki a ƙasashen waje na wasu makonni. Wasu kuma suna ba da kai don su yi aikin na shekaru da yawa, kuma da hakan, suna taimakawa a aikin gini a wurare dabam-dabam.

Timo da Lina Lappalainen (Ka duba sakin layi na 16)

16 Aikin gine-gine a ƙasashe dabam-dabam yana da nasa ƙalubale, amma duk da haka, yana kawo farin ciki. Alal misali, Timo da Lina sun je ƙasashe da yawa a nahiyoyin Asiya da Turai da kuma Amirka ta Kudu don su taimaka da ginin Majami’un Mulki da Majami’un Manyan Taro da kuma ofisoshin reshe. Timo ya ce: “Wajen kowace shekara biyu a cikin shekaru 30 yanzu, ana canja mini inda nake aikin gini.” Lina, wadda ta auri Timo shekaru 25 da suka shige, ta ce: “Na yi hidima tare da Timo a ƙasashe goma yanzu. Ba shi da sauƙi mutum ya saba da sabon abinci ko yanayi ko yare ko sabon yankin wa’azi ko kuma abokai.” c Amma kwalliya ta biya kuɗin sabulu kuwa? Lina ta ce, “Waɗannan ƙalubalen sun kawo mana albarka sosai. Mun shaida ƙauna ta Kirista kuma ’yan’uwa suna karɓan mu hannu bibbiyu. Ƙari ga haka, Jehobah ya kula da mu sosai kuma mun ga cikar alkawarin da Yesu ya yi wa almajiransa a Markus 10:29, 30. Mun sami ’yan’uwa mata da maza da iyaye Kirista sau ɗari.” Timo ya ce: “Yin amfani da iyawarmu a hanya mafi kyau, wato bunƙasa kayayyakin Sarkin, yana sa mu farin ciki sosai.”

17 Wani ɗan’uwa mai suna Darren da matarsa Sarah, waɗanda suka taimaka da aikin gini a ƙasashen Afirka da Asiya da Amirka ta Tsakiya da Turai da Amirka ta Kudu da Fasifik ta Kudu sun ce a ganinsu, sun sami albarka da ta fi sadaukarwa da suka yi. Duk da ƙalubalen da suka fuskanta, Darren ya ce: “Yin aiki da ’yan’uwa daga ƙasashe dabam-dabam a faɗin duniya babban gata ne. Hakan ya sa na fahimci cewa kamar tsintsiya da ke da maɗauri ɗaya, haka ma ƙaunar da muke yi wa Jehobah tana haɗa kanmu a faɗin duniya.” Sarah ta ce: “Na koyi abubuwa da yawa daga ’yan’uwana maza da mata masu al’ada dabam-dabam! Yayin da nake ganin sadaukarwa da suke yi don su bauta wa Jehobah, hakan yana motsa ni in ci gaba da yin iyakacin ƙoƙarina.”

18. Ta yaya annabcin da ke Zabura 110:1-3 yake cika a yau?

18 Sarki Dauda ya yi annabci cewa ko da yake talakawan Mulkin Allah za su fuskanci matsaloli da dama, amma za su ‘ba da kansu da yardan rai’ don su tallafa wa Mulkin. (Karanta Zabura 110:1-3.) Dukan waɗanda suke yin aikin da ke tallafa wa Mulkin suna cika wannan annabcin. (1 Kor. 3:9) Ofisoshin reshe da dama da ɗarurruwan Majami’un Manyan Taro da kuma dubban Majami’un Mulki da aka gina a faɗin duniya suna ba da tabbaci cewa Mulkin Allah ya tabbata kuma yana da iko bisa mutane a yau. Dama da muke da shi na yi wa Sarkinmu Yesu Kristi hidima ta wajen yin aikin da ke ɗaukaka Jehobah babban gata ne, ko ba haka ba? Hakika Jehobah ya cancanci wannan ɗaukakar!

a A shekara ta 2013, an zaɓi ’yan’uwa fiye da 230,000 da suka ba da kansu da yardan rai don su yi aiki tare da Kwamitin Gine-gine na Yanki guda 132 a ƙasar Amirka. A kowace shekara a wannan ƙasar, waɗannan kwamitocin sun ja-goranci aikin gina sababbin Majami’un Mulki guda 75 kuma sun taimaka a gyara Majami’un Mulki guda wajen 900.

b Wannan adadin bai ƙunshi Majami’un Mulkin da aka gina a ƙasashen da ba sa ƙarƙashin wannan kwamitin ba.

c Masu aikin gini a ƙasashen waje suna daɗewa sosai a aikin gini, duk da haka, suna taimaka wa ikilisiyar da ke yankin a yin wa’azi da yamma ko kuma a ƙarshen mako.