Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 20

Hidimar Agaji

Hidimar Agaji

MANUFAR WANNAN BABIN

Ƙauna tana motsa Kiristoci su ɗauki mataki a lokacin bala’i

1, 2. (a) Wane mawuyacin hali ne Kiristoci da ke Yahudiya suka sami kansu a ciki? (b) Ta yaya Kiristoci da ke Yahudiya suka san cewa ’yan’uwansu a wasu wurare suna ƙaunarsu?

 A WAJEN shekara ta 46 a zamaninmu an yi yunwa mai tsanani a Yahudiya. Saboda ƙarancin abinci, Yahudawa almajiran Yesu ba su iya sayan abinci ba don ya yi tsada sosai. A sakamakon haka, sun yi fama da yunwa sosai. Amma a wannan lokacin, Jehobah ya kula da su a wata muhimmiyar hanya da ba su taɓa tsammani ba. A wace hanya ke nan?

2 Sa’ad da Kiristoci da ke zama a Antakiya da Suriya suka ga yadda Kiristoci a Urushalima da Yahudiya suke shan wahala, sai suka yi gudummawar kuɗi don taimaka wa waɗannan ’yan’uwansu masu bi. Bayan haka, sai suka zaɓi ’yan’uwa biyu da aka yarda da su, wato Barnaba da Shawulu, don su kai kayan agaji ga dattawan ikilisiyar da ke Urushalima. (Karanta Ayyukan Manzanni 11:27-30; 12:25.) Ka yi tunanin yadda ’yan’uwa mabukata da ke Yahudiya suka ji saboda ƙaunar da Kiristoci da ke Antakiya suka nuna musu. Hakika, hakan ya ƙarfafa su sosai!

3. (a) Ta yaya bayin Allah a yau suke bin gurbin Kiristoci na farko da ke Antakiya? Ka ba da misali. (Ka kuma duba akwatin nan “ Gagarumin Aikin Agaji da Muka Soma Yi a Zamaninmu.”) (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan babin?

3 A ƙarni na farko, wannan shi ne agaji na farko da Kiristoci a wata ƙasa suka aika wa ’yan’uwansu Kiristoci da ke zama a wata ƙasa dabam. A yau, muna bin gurbin ’yan’uwanmu da ke Antakiya. Muna taimakon ’yan’uwanmu da ke wani wuri idan muka ji cewa bala’i ya shafe su ko kuma sun shiga wani mawuyacin hali. a Don mu fahimci alaƙar da ke tsakanin aikin agaji da kuma sauran ayyukan ibada, bari mu tattauna tambayoyi uku game da hidimar agaji: Me ya sa muka ɗauki aikin agaji a matsayin hidima ga Allah? Mene ne ake cim ma ta aikin agaji? Ta yaya muke amfana daga hidima ta agaji?

Abin da Ya Sa Aikin Agaji “Tsarkakkiyar Hidima” Ce

4. Mene ne Bulus ya bayyana wa ’yan’uwa da ke Korinti game da hidimar Kirista?

4 A wasiƙa ta biyu da Manzo Bulus ya rubuta zuwa ga ’yan’uwa a Korinti, ya bayyana cewa hidimar da Kiristoci suke yi tana da fannoni biyu. Ko da yake ya rubuta wasiƙar ne ga shafaffun Kiristoci, amma abin da ya faɗa ya shafi “waɗansu tumaki” na Kristi. (Yoh. 10:16) Fanni ɗaya na hidimar shi ne “hidima ta sulhu,” wato wa’azi da koyarwa da muke yi. (2 Kor. 5:18-20; 1 Tim. 2:3-6) Fanni na biyu kuma shi ne hidimar agaji da muke yi wa ’yan’uwanmu masu bi. Wannan ne Bulus ya ambata sa’ad da ya yi maganar “hidima ga tsarkaka.” (2 Kor. 8:4) Wannan kalmar “hidima” da aka ambata sa’ad da aka yi maganar ‘hidima ta sulhu’ da kuma ‘hidima ga tsarkaka,’ kalma ce da aka fassara daga harshen Helenanci, wato di·a·ko·niʹa. Me ya sa aka yi amfani da wannan kalmar a waɗannan ayoyin?

5. Me ya sa Bulus ya ce aikin agaji hidima ce ga Allah?

5 Sa’ad da Bulus ya yi amfani da kalmar nan “hidima” wajen kwatanta yin wa’azi da kuma na agaji, yana nuna cewa ba da agaji fanni ɗaya ne na hidimar da muke yi a cikin ikilisiyar Kirista. Kafin ya ambaci hakan, ya ce: ‘Akwai hidimomi kuma iri iri, Ubangiji kuwa ɗaya ne. Akwai kuma aike aike iri iri, . . . Amma dukan waɗannan shi wannan ruhu ɗaya ya ke aikata su.’ (1 Kor. 12:4-6, 11) Hakika, Bulus ya kwatanta hidimomi dabam-dabam da ake yi a cikin ikilisiya da ‘bauta’ ko kuma tsarkakkiyar hidima. b (Rom. 12:1, 6-8) Shi ya sa ya ga cewa ya dace ya yi amfani da lokacinsa don ‘yi wa tsarkakku hidima!’—Rom. 15:25, 26.

6. (a) Me ya sa Bulus ya ce aikin agaji sashe ne na ibadarmu ga Allah? (b) Ka bayyana yadda muke gudanar da aikin agaji a faɗin duniya a yau. (Ka duba akwatin nan “ Sa’ad da Bala’i Ya Auku!” a shafi na 214.)

6 Bulus ya taimaka wa Korintiyawa su fahimci cewa ba da agaji hidima ce kuma ibada ce ga Jehobah. Yana nufin Kiristoci da suke ba da agaji suna yin hakan ne don suna ‘biyayya . . . ga bisharar Kristi.’ (2 Kor. 9:13) Wato, Kiristoci suna taimaka wa ’yan’uwansu masu bi ne don suna bin koyarwar Kristi. Bulus ya ce waɗannan ayyukan alheri da suke yi a madadin ’yan’uwansu yana bayyana “mafificin alherin Allah.” (2 Kor. 9:14; 1 Bit. 4:10) Saboda da haka, sa’ad da Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1975, ta yi magana game da taimaka wa ’yan’uwanmu, ta ce: “Kada mu yi tunanin cewa Jehobah Allah da Ɗansa Yesu ba sa ɗaukan irin wannan hidimar da muhimmanci.” Babu shakka, ba da agaji fanni ne da ke da muhimmanci a bautarmu ga Jehobah.—Rom. 12:1, 7; 2 Kor. 8:7; Ibran. 13:16.

Abubuwan da Ake Cim Ma ta Wajen Ba da Agaji

7, 8. Mene ne abu na farko da ake cim ma a aikin agaji? Ka bayyana.

7 Waɗanne abubuwa ne ake cim ma a ba da agaji? Bulus ya ba da amsar wannan tambayar a cikin wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Korintiyawa. (Karanta 2 Korintiyawa 9:11-15.) A cikin waɗannan ayoyin, Bulus ya ambaci abubuwa uku da ake cim ma idan muka saka hannu a “aikin nan na alheri,” wato ba da agaji. Bari mu tattauna su ɗaya bayan ɗaya.

8 Na farko, ba da agaji da muke yi yana ɗaukaka Jehobah. Ka lura da yadda Bulus ya taimaka wa ’yan’uwansa su girmama Jehobah Allah a littafin 2 Korintiyawa 9:11-15 da aka ambata a baya. Manzon ya ce su riƙa yin “godiya ga Allah” kuma su “yawaita godiya ga Allah.” (Ayoyi 11 da 12) Ya ce ba da agaji yana sa Kiristoci su “ɗaukaka Allah” kuma su ɗaukaka “alherin Allah marar misaltuwa.” (Ayoyi 13 da 14) Bulus ya ambaci “godiya ga Allah” kafin ya kammala maganarsa game da hidimar agaji.—Aya ta 15; 1 Bit. 4:11.

9. Ta yaya aikin agaji zai sa mutane su daina kasancewa da mummunan ra’ayi? Ka ba da misali.

9 Ga bayin Allah a yau, ba da agaji hanya ce ta ɗaukaka Jehobah da kuma nuna cewa suna bin koyarwarsa. (1 Kor. 10:31; Tit. 2:10) Hakika, ba da agaji muhimmiyar hanya ce ta taimaka wa mutane su daina kasancewa da mummunan ra’ayi game da Jehobah Allah da kuma Shaidunsa. Alal misali: A wani yanki, wata mata ta saka wata alama a ƙofar gidanta da ke cewa: “Shaidun Jehobah, Kada Ku Zo Wa’azi a Nan.” Sa’ad da bala’i ya addabi yankin, sai matar ta lura da wasu masu aikin agaji da suke gyara gidan wani da bala’in ya shafa kusa da gidanta. Ta yi kwanaki tana lura da yadda masu aikin suke fara’a, sai ta je wurin don ta san ko su wane ne waɗannan mutanen. Sa’ad da ta gane cewa masu aikin agajin Shaidun Jehobah ne, abin ya burge ta kuma ta ce, “Na yi muku bahaguwar fahimta.” Mene ne sakamakon haka? Matar nan ta cire wannan alamar daga ƙofarta.

10, 11. (a) Waɗanne misalai ne suka nuna cewa muna cim ma maƙasudi na biyu a aikin agaji? (b) Wace ƙasida ce ta taimaka wa masu aikin agaji? (Ka duba akwatin nan “ Sabuwar Ƙasida Don Masu Aikin Agaji.”)

10 Na biyu, muna ‘biyan bukatun’ ’yan’uwanmu masu bi. (2 Kor. 9:12a) Muna marmarin taimaka wa ’yan’uwanmu da kuma sauƙaƙa musu wahala idan bukata ta kama. Me ya sa? Don dukan waɗanda ke cikin ƙungiyar Jehobah suna nan kamar ‘jiki ɗaya’ ne, kuma “idan gaɓa ɗaya kuwa ya sha raɗaɗi, dukan gaɓaɓuwa suna shan raɗaɗi tare da shi.” (1 Kor. 12:20, 26) Saboda haka, ƙauna da tausayi suna motsa ’yan’uwa maza da mata a yau su bar aikinsu nan take kuma su tattara kayan aiki zuwa inda aka yi bala’i don taimaka wa ’yan’uwansu. (Yaƙ. 2:15, 16) Alal misali, bayan tsunami ya addabi Japan a shekara ta 2011, ofishin reshe na Amirka ya aika wasiƙa zuwa ga Kwamitocin Gine-gine na Yanki da ke Amirka. Wasiƙar ta ce ana bukatar “’yan’uwa kaɗan da suka cancanta” don su taimaka da sake gina Majami’un Mulki a Japan. “Mutane nawa ne suka amsa wannan kira? Cikin makonni, kusan ’yan’uwa 600 ne suka ba da sunansu cewa za su taimaka, kuma sun amince su biya kuɗin jirgi daga aljihunsu zuwa Japan! Ofishin reshe na Amirka ya ce: “Yawan mutanen da suka amsa wannan kira ya ba mu mamaki sosai.” Sa’ad da wani ɗan’uwa ya tambayi wani mai taimako da ya zo daga wata ƙasa dalilin da ya sa ya ba da kai don ya taimaka, amsar da aka ba shi ita ce: “’Yan’uwanmu da ke Japan suna kamar gaɓar ‘jikinmu’ ne. Muna jin wahalar da suke sha.” Masu aikin agaji suna sadaukar da kai don su taimaka wa ’yan’uwansu, wani lokaci ma sukan sa ransu cikin haɗari don suna ƙaunar ’yan’uwansu. c1 Yoh. 3:16.

11 Ƙari ga haka, mutanen da ba Shaidun Jehobah ba suna godiya don aikin agajin da muke yi. Alal misali, bayan wani bala’i ya addabi jihar Arkansas, a Amirka, a shekara ta 2013, wata jarida ta ba da rahoto game da yadda Shaidun Jehobah suke saurin zuwa inda aka yi bala’i don su taimaka. Jaridar ta ce: “Shaidun Jehobah sun ƙware sosai wajen tsara aikin agaji don suna zuwa inda bala’i ya auku ba tare da ɓata lokaci ba.” Hakika, muna ‘biyan bukatun’ ’yan’uwanmu da kyau kamar yadda manzo Bulus ya faɗa.

12-14. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu cim ma maƙasudi na uku na aikin agaji? (b) Waɗanne kalamai ne suka nuna cewa ci gaba da ayyuka na ibada yana da muhimmanci?

12 Na uku, muna taimaka wa waɗanda bala’i ya shafa su sake ci gaba da ayyukansu na ibada. Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Bulus ya ambata cewa agajin da ’yan’uwa suka karɓa zai motsa su su miƙa “godiya mai-yawa zuwa ga Allah.” (2 Kor. 9:12b) Babu shakka, hanya mafi muhimmanci da waɗannan za su nuna godiyarsu ga Allah ita ce ta sake ci gaba da ayyukansu na ibada ba tare da ɓata lokaci ba. (Filib. 1:10) A shekara ta 1945, an ambata a cikin Hasumiyar Tsaro cewa: “Bulus ya ce a yi . . . gudummawa don tana taimaka wa . . . Kiristoci mabukata su sami abin biyan bukata da damar yin wa’azi da ƙwazo.” Hakazalika, abin da aikin agaji yake cim ma ke nan a yau. Idan ’yan’uwa suka sake ci gaba da wa’azi, suna ƙarfafa maƙwabtansu da ke baƙin ciki kuma ta hakan, suna ƙarfafa kansu.—Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.

13 Wasu da suka ci gaba da hidima bayan sun sami agaji sun ce sun sami ƙarfafa sa’ad da suka fita wa’azi. Bari mu yi la’akari da abin da suka faɗa. Wani ɗan’uwa ya ce: “Mun amfana sosai sa’ad da muka fita wa’azi. Yayin da muke ƙoƙarin ƙarfafa wasu, mun sami kwanciyar hankali don mun ɗan manta da damuwarmu.” Wata ’yar’uwa ta bayyana cewa: “Mai da hankali ga ayyukan ibada ya sa na manta da bala’in da ya faru. Ya sa hankalina ya kwanta.” Wata ’yar’uwa ta ƙara da cewa: “Ko da yake ba za mu iya sarrafa wasu abubuwa da ke faruwa ba, fita wa’azi ya sa iyalinmu ta kasance da bege. Yi wa wasu magana game da alkawarin sabuwar duniya ya sa mun ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai sake mai da kome sabo.”

14 Wani aiki na ibada kuma da muke taimaka wa ’yan’uwanmu da bala’i ya shafa su sake ci gaba da yi ba tare da ɓata lokaci ba shi ne halartan taro. Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata ’yar’uwa mai suna Kiyoko da ta ba shekaru hamsin da biyar baya. Wani tsunami ya addabe su sakamakon haka, ta yi asarar dukan mallakarta. Abin da suka rage kawai su ne tufafi da takalma da take sanye da su. Hakan ya sa ta damu sosai kuma ta rasa abin za ta yi. Sai wani dattijo ya gaya mata cewa za su riƙa yin taron Kirista a cikin motarsa. Kiyoko ta ce: “Wani dattijo da matarsa da ni da wata ’yar’uwa ne muka zauna a cikin motar. An gudanar da taron a sawwaƙe, amma wani abin mamaki ya faru, na manta gaba ɗaya cewa tsunami ya faru. Na sami kwanciyar rai. A wannan taron, na fahimci cewa tarayya da ’yan’uwa Kirista yana da amfani sosai.” Wata ’yar’uwa ta yi kalami game da taron da ta halarta bayan da wani bala’i ya addabe su, ta ce: “Waɗannan taron sun taimaka min in jure!”—Rom. 1:11, 12; 12:12.

Aikin Agaji Yana Kawo Albarka na Dindindin

15, 16. (a) Wace albarka ce ’yan’uwa da ke Korinti da kuma wasu wurare za su samu ta wajen yin aikin agaji? (b) Ta yaya muke amfana daga aikin agaji a yau?

15 Sa’ad da manzo Bulus yake tattauna batun hidimar agaji, ya bayyana wa Korintiyawa da wasu Kiristoci albarka da irin wannan aikin yake kawowa. Da yake magana a madadin Kiristoci da ke Urushalima da suka karɓi agaji, ya ce: ‘Su kuwa da kansu, yayinda suna roko dominku, suna begenku saboda mafificin alherin Allah da ke cikinku.’ (2 Kor. 9:14) Hakika, karimci da Korintiyawa suka yi zai sa Kiristoci Yahudawa su yi addu’a a madadinsu da kuma waɗanda suka fito daga al’ummai, kuma hakan zai sa ’yan’uwa Yahudawa su ƙara ƙaunar su.

16 Ta yaya za mu amfana daga abin da Bulus ya faɗa game da albarkar da ake samu don aikin agaji? Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1945, ta bayyana cewa: “Sa’ad da bayin Allah suka yi gudummawa don biyan bukatun ’yan’uwansu da ke zama a wani ɓangare dabam, hakan yana ƙara haɗa kanmu!” Abin da masu aikin agaji suke mora ke nan. Wani dattijo da ya taimaka a wani aikin agaji sa’ad da ambaliyar ruwa ta addabi wani yanki, ya ce: “Saka hannu a aikin agaji ya sa na yi kusa da ’yan’uwana sosai.” Wata ’yar’uwa da ta amfana daga aikin agaji ta ce: “’Yan’uwantaka da muke mora a ƙungiyar Jehobah ce kawai za mu ɗan kwatanta Aljanna a duniya da shi.”—Karanta Misalai 17:17.

17. (a) Ta yaya kalmomin da ke Ishaya 41:13 ya ke cika a aikin agaji? (b) Ka ba da wasu misalai da ke nuna yadda aikin agaji yake ɗaukaka Jehobah da kuma ƙara haɗa kanmu. (Ka duba akwatin nan “’ Yan’uwa a Faɗin Duniya Sun Taimaka da Aikin Agaji.”)

17 Sa’ad da masu aikin agaji suka isa inda bala’i ya auku, ’yan’uwanmu da abin ya shafa sukan ga cikar wannan alkawarin da Allah ya yi sa’ad da ya ce: “Ni Ubangiji Allahnka zan riƙe hannun damanka, . . . Kada ka ji tsoro, ni taimake ka.” (Isha. 41:13) Wata ’yar’uwa da ta tsira daga wani bala’i ta ce: “Sa’ad da na ga abin da ya faru, na karaya, amma Jehobah ya taimake ni. Ba zan iya kwatanta taimakon da ’yan’uwa suka yi mini ba.” Bayan wani bala’i ya addabi yankinsu, wasu dattawa guda biyu sun rubuta wasiƙa a madadin ikilisiyoyinsu, sun ce: “Girgizar ƙasar ta sa mu baƙin ciki sosai amma mun amfana daga taimakon da Jehobah yake tanadarwa ta wurin ’yan’uwanmu. A dā muna karanta yadda ake yin aikin agaji ne kawai, amma yanzu mun ga yadda ake gudanarwa da idanunmu.”

Za Ka Iya Taimakawa?

18. Mene ne za ka iya yi ɗaukawa idan kana so ka yi aikin agaji? (Ka duba akwatin nan “ Aikin Agaji Ya Yi Tasiri a Rayuwarsa.”)

18 Za ka so ka mori farin cikin da ke tattare da aikin agaji? Idan kana so, ka tuna cewa ana zaɓan masu aikin agaji ne daga masu aikin gine-gine na Majami’ar Mulki. Saboda haka, ka gaya wa dattawa da ke ikilisiyarku cewa kana so ka cika afilkeshan ɗin. Wani dattijo da ya daɗe yana aikin agaji, ya ba da wata shawara cewa: “Kada ka je inda bala’i ya auku idan ba ka sami wasiƙa daga Kwamitin Aikin Agaji ba.” Idan muka bi shawarar nan, aikin agajin da muke yi zai kasance da tsari.

19. Ta yaya masu aikin agaji suke sa a san cewa mu almajiran Yesu ne da gaske?

19 Aikin agaji muhimmiyar hanya ce ta yin biyayya ga umurnin da Yesu ya bayar cewa mu kasance da ‘ƙauna ga junanmu.’ (Yoh. 13:34, 35) Hakika, kasancewa da masu aikin agaji da son rai da ke ɗaukaka Jehobah yayin da suke tanadar da agaji wa waɗanda ke wa’azin Mulkin Allah ba ƙaramar albarka ba ce!

a Wannan babin ya tattauna aikin agaji da ake yi don taimaka wa ’yan’uwa masu bi. Amma, a yawancin lokaci, aikin agaji da muke yi yana amfanar waɗanda ba Shaidun Jehobah ba.—Gal. 6:10.

b Bulus ya yi amfani da jam’in kalmar nan di·aʹko·nos (mai hidima) sa’ad da yake kwatanta “dikon.”—1 Tim. 3:12.

c Ka duba talifin nan “Aiding Our Family of Believers in Bosnia,” da ke shafuffuka na 23-27 na Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1994, a Turanci.