Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 22

Mulkin Ya Sa Ana Yin Nufin Allah a Duniya

Mulkin Ya Sa Ana Yin Nufin Allah a Duniya

MANUFAR WANNAN BABIN

Mulkin ya cika dukan alkawuran Allah ga ’yan Adam da kuma duniya

1, 2. (a) Me ya sa zai yi wuya a wani lokaci mu yarda cewa akwai Aljanna? (b) Mene ne zai taimaka mana mu ƙara yin imani da alkawuran Allah?

 WANI amintaccen ɗan’uwa ya shigo cikin taro a gajiye bayan ya tashi daga wurin aiki. Maigidansa ya wulaƙanta shi, yana kula da iyalinsa da ƙyar, kuma yana alhini don matarsa tana rashin lafiya. Sa’ad da aka soma waƙa ta farko a taron, sai ya yi ajiyar zuci, yana farin ciki don yana Majami’ar Mulki tare da ’yan’uwansa. Waƙar da ake rerawa game da begen yin rayuwa a Aljanna ne, kuma an furta a kalmomin waƙar cewa ya ga kansa yana cikin wannan wurin. Ya daɗe yana son waƙar nan, kuma yayin da yake rera ta tare da iyalinsa, ya sami kwanciyar hankali.

2 Shin kai ma ka taɓa jin haka kuwa? Yawancinmu mun taɓa jin haka. Babu shakka, yanayin rayuwa a wannan duniyar za ta iya sa mu ga cewa kasancewa a cikin Aljanna a nan gaba ƙage ne. Muna cikin “miyagun zamanu,” kuma rayuwa a wannan duniya ba daɗi ko kaɗan. (2 Tim. 3:1) Mene ne zai taimaka mana mu san cewa begenmu na gaske ne? Yaya muka tabbata cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai yi sarauta bisa ’yan Adam? Bari mu tattauna kaɗan daga cikin annabcin da Jehobah ya yi da suka cika a kan bayinsa a zamanin dā. Bayan haka, za mu tattauna yadda waɗannan annabcin da kuma makamancinsu suke cika a yau. Hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu kuma a ƙarshe, za mu tattauna yadda waɗannan annabcin za su shafe mu a nan gaba.

Yadda Jehobah Ya Cika Alkawuransa a Dā

3. Wane alkawari ne ya ta’azantar da Yahudawa da ke bauta a ƙasar Babila?

3 Ka yi tunanin yadda rayuwa ta kasance wa Isra’ilawa a lokacin da suke bauta a ƙasar Babila a ƙarni na shida kafin zamaninmu. Isra’ilawa da yawa sun yi girma a ƙasar Babila, kuma rayuwa ba ta yi musu sauƙi ba. ’Yan Babila sun yi musu ba’a domin sun yi imani da Jehobah. (Zab. 137:1-3) Yahudawa masu aminci sun ci gaba da sa rai a kan wannan begen cikin shekaru da yawa. Wane bege ke nan? Jehobah ya yi alkawari cewa zai maido da su ƙasarsu. Jehobah ya ce za su ji daɗin rayuwarsu a nan. Ya ma ce wannan ƙasar da za su koma zai zama kamar lambun Adnin, wato aljanna! (Karanta Ishaya 51:3.) Jehobah ya yi wannan alkawarin don ya ƙarfafa bayinsa, kuma ya sa su daina shakka. Ta yaya? Ka yi la’akari da wasu takamammun annabci.

4. Ta yaya Jehobah ya tabbatar wa Yahudawa cewa za su sami kāriya a ƙasarsu?

4 Kāriya. Ba aljanna ta zahiri ba ce waɗannan Yahudawa da suke bauta a Babila za su koma ba, amma wata ƙasa mai nisa ce. Wannan ƙasar ta zama kango har shekara 70 kuma yawancinsu ba su taɓa ganin ƙasar ba. Zakuna da damisoshi da kuma wasu namomin daji masu ɓarna gama-gari ne a zamanin dā. Magidanci zai iya cewa, ‘Ta yaya zan iya kāre matata da kuma yarana? Tumakina da shanuna kuma fa, ta yaya zan iya kāre su ma?’ Irin wannan tunanin ba laifi ba ne. Ka yi tunani a kan alkawarin Allah da ke cikin littafin Ishaya 11:6-9 da kuma yadda yake da ban ƙarfafa. (Karanta.) Jehobah ya yi amfani da waɗannan kalmomin don ya tabbatar wa bayinsa da suke bauta a ƙasar Babila cewa su da dabbobinsu za su samu kāriya. Ya ce zaki zai ci ciyawa, wato ba zai yi wa dabbobin Yahudawa lahani ba. Amintattun Yahudawa ba za su ji tsoro ba. Me ya sa? Domin Jehobah ya yi musu alkawari cewa za su sami kāriya a ƙasar da za su koma da kuma a cikin hamada da daji.—Ezek. 34:25.

5. Waɗanne annabci ne suka taimaka wa Yahudawan da suka dawo daga bauta su kasance da tabbaci cewa Jehobah zai biya bukatunsu?

5 Yalwa. Akwai wasu abubuwa kuma da za su iya yin tunani a kai. ‘Shin zan iya ciyar da iyalina a cikin wannan ƙasar da za mu koma? A wane gida ne za mu zauna? Shin za mu sami aikin yi ne, kuma za mu ji daɗin rayuwa fiye da lokacin da muke bauta a Babila?’ Jehobah ya yi amfani da annabci don ya amsa waɗannan tambayoyin. Jehobah ya yi wa bayinsa alkawari cewa za su sami isashen ruwan saman da zai sa ƙasa ta ba da amfani “mai-albarka.” (Isha. 30:23) Jehobah ya kuma yi musu alkawari game da wurin zama da kuma aiki mai kyau. Ya ce: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba.” (Isha. 65:21, 22) Hakika, rayuwa za ta yi daɗi sosai a wannan ƙasar fiye da a ƙasar Babila da suke bautar gumaka. Amma, mene ne Jehobah zai yi game da matsalolinsu mafi girma, wadda ta sa aka kawo su bauta a ƙasar Babila?

6. Wace irin cuta ce bayin Allah suka daɗe suna fama da ita, kuma mene ne Jehobah ya tabbatar wa Yahudawan da suka dawo daga bauta?

6 Ibada. Tun kafin a kai mutanen Allah bauta a wannan ƙasar, dangantakarsu da Jehobah ta yi tsami. Jehobah ya yi amfani da annabi Ishaya don ya furta waɗannan kalmomin game da su. Ya ce: “Dukan kai yana ciwo, zuciya duk ta yi suwu.” (Isha. 1:5) Isra’ilawa sun zama makafi da kurame a dangatakarsu da Jehobah. Me ya sa? Domin sun ƙi jin umurnin Jehobah kuma sun yi tir da koyarwarsa. (Isha. 6:10; Irm. 5:21; Ezek. 12:2) Idan waɗannan Isra’ilawan da za su koma ƙasarsu ma suna da wannan matsalar, shin za su sami kāriya kuwa? Babu shakka, za su sake koma gidan jiya. Alkawarin da Jehobah ya yi ya ƙarfafa su sosai: “A cikin waccan rana kurame za su ji zantattukan littafi, idanun makafi kuma za su gani daga cikin duruduru da duhu.” (Isha. 29:18) Hakika, Jehobah zai sa dangantakarsa da bayinsa da suka tuba ta yi danƙo. Jehobah zai ci gaba da kāre da kuma koyar da su muddin suna bin umurninsa da koyarwarsa.

7. Ta yaya Jehobah ya cika alkawarinsa ga bayinsa da suke bauta, kuma me ya sa hakan abin ban ƙarfafa ne?

7 Shin Jehobah ya cika alkawuransa kuwa? Abubuwan da suka faru sun ba da amsar wannan tambayar. Jehobah ya albarkaci Yahudawan da suka koma ƙasarsu ta wajen sa su sami kāriya da yalwa da kuma dangantaka mai kyau da shi. Alal misali, Jehobah ya kāre su daga maƙwabtansu da suka fi su ƙarfi da kuma yawa. Namomin daji ba su cinye dabbobinsu ba. Hakika, ƙalilan cikin yanayin da Ishaya da Irmiya da kuma Ezekiyel suka annabta cewa za su faru ne waɗannan Yahudawan suka gani. Amma alkawuran da suka cika a kan bayin Allah daidai abubuwan da suke bukata ne a lokacin. Yayin da muke bimbini a kan abin da Jehobah ya yi wa bayinsa a zamanin dā, bangaskiyarmu za ta daɗa ƙarfi. Idan waɗannan annabcin da ƙalilan cikinsu suka cika sun sa mutane matuƙar farin ciki, ka yi tunanin yadda mutane za su yi farin ciki idan annabci masu ɗimbin yawa suka cika a nan gaba! Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya yi mana a yau.

Yadda Jehobah Ya Soma Cika Alkawuransa a Zamaninmu

8. A wace irin “ƙasa” ce bayin Allah suke zama a yau?

8 A yau, bayin Jehobah ba su riga sun zama al’umma guda ba kuma ba sa zama a ƙasa ɗaya. Maimakon haka, Kiristoci shafaffu sun zama al’umma ta alama, wato “Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16) Abokansu “waɗansu tumaki” suna zama tare da su a wannan “ƙasar,” wato suna bauta wa Jehobah tare cikin haɗin kai. Wannan ibadar ta zama jininsu. (Yoh. 10:16; Isha. 66:8) Shin wace irin “ƙasa” ce Jehobah ya ba mu? Aljanna ce ta alama. A cikin wannan Aljannar, muna shaida yanayin da ke kamar na aljanna ta zahiri a ibadarmu. Ka yi la’akari da wasu cikinsu.

9, 10. (a) A wace hanya ce annabcin da ke Ishaya 11:6-9 yake cika a yau? (b) Mene ne ya nuna cewa bayin Allah suna more salama?

9 Kāriya. A cikin annabcin da ke littafin Ishaya 11:6-9, mun ga kwatancin haɗin kai da kuma salamar da za ta kasance tsakanin namomin daji da kuma ’yan Adam da dabbobinsu. Shin wannan annabcin yana cika kuwa a alamance a yau? Ƙwarai kuwa! A cikin aya ta 9, mun koyi dalilin da ya sa waɗannan halittun ba za su jawo lahani ba: “Gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.” Shin “sanin” Jehobah yana canja halayen dabbobi kuwa? A’a. Halayen ’yan Adam ne za a canja domin su san Allah Maɗaukakin Sarki kuma su yi koyi da halinsa na salama. Shi ya sa muke shaida wannan yanayin a ibadarmu a yau. Mabiyan Kristi suna koyon yin watsi da munanan halayensu na dā da ke kamar na namomin daji kuma suna zama cikin kwanciyar hankali da ’yan’uwansu maza da mata. Sun cim ma wannan a ƙarƙashin Mulkin Allah.

10 Alal misali a wannan littafin, mun tattauna batun kasancewa da halin ba ruwanmu da harkokin wannan muguwar duniyar, wato ƙa’idodin Nassosi da suka sa muke hakan da kuma tsanantawar da muka fuskanta a sakamako. Shin ba abin mamaki ba ne cewa a wannan duniyar da ke cike da mugunta, akwai mutanen da suka ƙi saka hannu a rikici ko da hakan zai sa a kashe su? Hakan tabbaci ne cewa talakawan Mulkin Almasihu suna more salamar da Ishaya ya kwatanta! Yesu ya ce za a san mabiyansa da ƙaunar da suke nuna wa juna. (Yoh. 13:34, 35) Yesu yana yin amfani da “bawa mai-aminci, mai-hikima” da sannu-sannu wajen koya wa Kiristoci su kasance da salama da ƙauna da kuma hali mai kyau.—Mat. 24:45-47.

11, 12. Wane irin bala’in yunwa ne ke damun mutane a yau, amma ta yaya Jehobah yake wa bayinsa tanadi?

11 Yalwa. Mutane a wannan duniya ba su da dangantaka mai kyau da Allah. Littafi Mai Tsarki ya yi wannan gargaɗin: “Ga shi, in ji Ubangiji Yahweh, kwanaki suna zuwa inda zan aike yunwa a cikin ƙasan, ba yunwar gurasa ko ƙishin ruwa ba, amma na jin maganar Ubangiji.” (Amos 8:11) Shin talakawan Mulkin Allah suna fama da irin wannan yunwa kamar sauran mutane? Jehobah ya annabta bambancin da zai kasance tsakanin bayinsa da kuma maƙiyansa: “Bayina za su ci, amma ku za ku ji yunwa: ga shi, bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; ga shi, bayina za su yi farinciki, amma ku za ku ji kunya.” (Isha. 65:13) Shin ka shaida cikar wannan annabcin kuwa?

12 Muna samun koyarwar da ke ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, kuma ana mana tanadinsu babu fashi, kamar yadda ruwan kogi ba ya bushewa. Ana mana tanadin littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da sauti da bidiyo da koyarwa a taron ikilisiya da manyan taro da kuma a dandalin Yanar gizonmu babu fashi. Dukan waɗannan abubuwan suna ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah a wannan duniyar da babu ruwan mutane da Allah. (Ezek. 47:1-12; Joel 3:18) Shin ba ka farin cikin ganin cikar waɗannan alkawuran a rayuwarka? Kana amfani da waɗannan abubuwan da Jehobah yake tanadarwa a kai a kai kuwa?

Ikilisiyoyinmu suna taimaka mana mu sami koyarwa masu kyau da kāriya da kuma ƙoshin lafiya

13. Ta yaya ne ka ga cikar alkawarin da Jehobah ya yi game da buɗe idanun makafi da kunnuwan kurame a yau?

13 Ibada. Makancewa da kurumcewa na alama matsaloli ne da suka zama gama gari a yau. (2 Kor. 4:4) Amma, Yesu yana warkar da cututtuka a faɗin duniya. Shin ka taɓa ganin inda aka buɗe idanun makafi, kuma aka sa kurame su soma jin magana? Idan ka taɓa ganin inda mutane suka koyi gaskiya game da Allah, suka daina bin koyarwar addinin ƙarya da ta mai da su kamar makafi a dā, to, ka ga cikar wannan alkawarin: “A cikin waccan rana kurame za su ji zantattukan littafi, idanun makafi kuma za su gani daga cikin duruduru da duhu.” (Isha. 29:18) Dubban mutane a faɗin duniya suna samun irin wannan warkarwa a ibadarsu ga Jehobah. Kowane mutum da ya fita daga Babila Babba kuma ya soma ibada tare da mu a wannan aljanna ta alama ya nuna cewa alkawuran Jehobah suna cika!

14. Yin bimbini a kan mene ne zai ƙarfafa bangaskiyarmu?

14 Kowane babi na wannan littafin yana ɗauke da abubuwan da suka tabbatar mana cewa Yesu ya tattara mabiyansa cikin aljanna ta alama a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Bari mu ci gaba da yin bimbini a kan hanyoyi da yawa da muke samun albarka a wannan aljannar a yau. Yayin da muke yin hakan, za mu daɗa yin imani ga alkawuran da Jehobah ya yi mana game da nan gaba.

‘Bari Mulkinka Ya Zo’

15. Me ya sa za mu iya kasance da tabbaci cewa duniya za ta zama aljanna?

15 Tun asali, nufin Jehobah shi ne duniya ta zama aljanna. Ya saka Adamu da Hawwa’u a cikin aljanna, ya umurce su su cika duniya da ’ya’yansu kuma su kula da dukan halittunsa. (Far. 1:28) Adamu da Hawwa’u sun ƙi yin biyayya ga Allah, maimakon haka, sun saurari Shaiɗan kuma sun jawo wa ’ya’yansu ajizanci da zunubi da kuma mutuwa. Duk da haka, nufin Allah bai canja ba. Muddin Jehobah ya furta abu, dole ne ya cika. (Karanta Ishaya 55:10, 11.) Hakan ya tabbatar mana cewa ’ya’yan Adamu da Hawwa’u za su cika duniya kuma su mamaye ta a nan gaba. Ƙari ga haka, za su kula da halittun Jehobah da ke cikin aljanna. A lokacin, annabcin da aka yi cewa Yahudawa za su kasance a yanayin da ke kama da na aljanna zai cika baki ɗaya! Ka yi la’akari da waɗannan misalan.

16. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta kāriyar da za mu more a Aljanna?

16 Kāriya. Alkawarin da ke littafin Ishaya 11:6-9 zai cika a zahiri a nan gaba. Maza da mata da kuma ƙananan yara za su sami kāriya a duk inda suka shiga a wannan duniyar. ’Yan Adam da dabbobi ba za su yi lahani wa juna ba. Ka yi tunanin yadda za ka ji sa’ad da duniya baki ɗaya ta zama gidanka. Za ka yi iyo a koguna da teku, ka hau tuddai kuma ka yi yawo a cikin jeji ba tare da jin tsoron kome ba. Kuma ba za ka damu ba idan dare ya yi. Kalmomin da ke Ezekiyel 34:25 za su cika, kuma bayin Allah za su “zauna lafiya a jeji,” kuma su “yi barci a kurmi.”

17. Me ya sa za mu iya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai biya bukatunmu sa’ad da Mulkin ya soma sarauta bisa duniya baki ɗaya?

17 Yalwa. Ka yi tunanin lokacin da ba za a sake yin talauci da rashin lafiyayyen abinci da yunwa da kuma yaƙe-yaƙe ba. Abubuwa masu ɗimbin yawa da Jehobah yake tanadar wa bayinsa a yau tabbaci ne cewa Sarkin Mulkin Allah zai ciyar da talakawansa a dukan fannonin rayuwa. Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nuna cewa zai iya cika wannan alkawarin ta wajen yin amfani da gurasa da kuma kifi ƙalilan don ciyar da dubban mutane da suke yunwa. (Mat. 14:17, 18; 15:34-36; Mar. 8:19, 20) Sa’ad da Mulkin Allah yake sarauta bisa dukan duniya, irin waɗannan annabci na gaba za su cika: “Duk lokacin da kuka shuka amfanin gonakinku, Ubangiji zai aiko da ruwan sama ya sa su girma, zai ba ku kaka mai albarka, shanunku kuma za su sami makiyaya wadatacciya.”—Isha. 30:23, Littafi Mai Tsarki.

18, 19. (a) Mene ne ma’anar annabcin da ke Ishaya 65:20-22 a gare ka? (b) A wace hanya ce rayuwarmu za ta zama kamar “kwanakin itace”?

18 A yau, mutane da yawa ba sa tunanin cewa za su zauna a gida mai kyau ko kuma su yi aiki mai albarka. A wannan duniyar da maguɗi ya zama ruwan dare, mutane da yawa suna ji cewa suna aiki na sa’o’i da yawa ba tare da samun abin da za su biya wa kansu da iyalinsu bukata ba. Amma mawadata da masu kwaɗayi ne suke morewa. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da wannan annabcin ya cika a dukan duniya: ‘Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; gama kamar yadda kwanakin itace suke, hakanan kwanakin mutanena za su zama, zaɓaɓɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.’—Isha. 65:20-22.

19 Mene ne furucin nan kwanakin mutanena za su zama “kamar yadda kwanakin itace” yake nufi? Idan ka tsaya kusa da wani babban itace, shin ba ka yin mamakin shekarun da itacen ya yi, wataƙila kafin a haifi kakan-kakanninka? Idan ka kasance a yanayin da kake yanzu, wataƙila za ka mutu ka bar itacen kuma zai ci gaba da wanzuwa babu wata matsala. Alkawarin da Jehobah ya yi cewa za mu jima a cikin Aljanna ba tare da wata matsala ba abin ban ƙarfafa ne sosai! (Zab. 37:11, 29) Lokaci zai zo da har itatuwan da suke yin shekaru da yawa a yau, za su zama kamar ciyayi a idanunmu domin za su mutu amma mu za mu rayu har abada!

20. Ta yaya talakawan Mulkin Allah masu aminci za su sami koshin lafiya?

20 Ƙoshin lafiya. A yau, rashin lafiya da mutuwa suna shafan kowa a duniya. Ma’ana, dukanmu mun kamu da cutar da ake kira zunubi. Abu ɗaya tak da zai iya warkar da mu shi ne hadayar fansa ta Kristi. (Rom. 3:23; 6:23) A lokacin Sarautar Yesu ta shekara dubu, shi da abokan sarautarsa za su yi amfani da wannan fansar don su ’yantar da amintattun mutane daga zunubi. Annabcin Ishaya zai cika a wata muhimmiyar hanya: “Wanda yake zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba: mutanen da ke zaune a wurin za a gafarta masu zunubinsu.” (Isha. 33:24) Ka yi tunanin lokacin da babu mutumin da zai zama makaho ko kurma ko kuma gurgu. (Karanta Ishaya 35:5, 6.) Babu rashin lafiyar da Yesu ba zai iya warkarwa ba, ko da ta jiki ce ko ta ƙwaƙwalwa ko kuma ta motsin rai. Talakawan Mulkin masu aminci za su kasance da koshin lafiya!

21. Mene ne zai faru da mutuwa, kuma me ya sa wannan alkawarin yake da ban ƙarfafa?

21 Mene ne zai faru da mutuwa, wadda rashin lafiya take yawan jawowa? Littafi Mai Tsarki ya kira ta ‘maƙiya ta ƙarshe,’ kuma tana shafan dukan ’yan Adam ajizai. (1 Kor. 15:26) Amma shin mutuwa ta fi ƙarfin Jehobah ne? Ka lura da abin da Ishaya ya annabta: “Ya haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki.” (Isha. 25:8) Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance a lokacin. Ba za a sake yin jana’iza ko kuka ba, kuma makabartai ba za su kasance ba! Akasin haka, mutane za su zub da hawaye saboda farin ciki yayin da Jehobah ya cika alkawarinsa ta wajen tayar da matattu. (Karanta Ishaya 26:19.) A sakamakon haka, za a kawo ƙarshen dukan matsalolin da mutuwa take jawowa.

22. Mai zai faru sa’ad da Mulkin Almasihu zai cim ma nufin Allah a duniya?

22 A ƙarshen Sarautar Yesu ta shekara dubu, Mulkin zai cika nufin Allah a duniya kuma Kristi zai miƙa wa Ubansa sarautar. (1 Kor. 15:25-28) ’Yan Adam za su zama kamiltattu kuma za su kasance a shirye don gwaji na ƙarshe da Shaiɗan zai yi musu sa’ad da aka sako shi daga rami marar matuƙa. Bayan haka, Kristi zai halaka Shaiɗan da dukan magoya bayansa. (Far. 3:15; R. Yoh. 20:3, 7-10) Amma dukan amintattu da suke ƙaunar Jehobah za su sami albarka sosai a nan gaba. Hurarrun kalmomin da ke gaba sun kwatanta abin da zai faru. Waɗanne kalmomi ke nan? Kalmar Allah ta ce amintattu za su “tsira daga bautar ɓacewa zuwa cikin ’yancin darajar ’ya’yan Allah.”—Rom. 8:21.

Mulkin zai cika dukan alkawuran Jehobah game da ’yan Adam da kuma duniya

23, 24. (a) Me ya sa muke da tabbaci cewa Allah zai cika alkawuransa? (b) Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

23 Waɗannan alkawuran ba tatsuniya ko kuma mafarki ba ne. Babu abin da zai iya hana Jehobah cika alkawuransa! Me ya sa? Ka tuna da kalmomin Yesu da muka tattauna a babi na farko na wannan littafin. Ya koya wa almajiransa yin addu’a ga Jehobah. Ya ce: “Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Mat. 6:9, 10) Mulkin Allah ba ƙage ba ne. Sarauta ce ta gaske! Tana sarauta a cikin sama a yanzu haka. A cikin ƙarnuka da yawa yanzu, Mulkin ya cika alkawuran Jehobah a hanyoyin da yawa kuma muna ganin hakan a cikin ikilisiyar Kirista. Muna da tabbaci cewa dukan alkawuran Jehobah za su cika sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta bisa duniya!

24 Mun san cewa Mulkin Allah zai zo kuma mun san cewa Jehobah zai cika dukan alkawuransa. Me ya sa? Domin MULKIN ALLAH YANA SARAUTA! Ya kamata kowanenmu ya tambayi kansa, ‘Shin Mulkin yana sarauta a kaina kuwa?’ Bari mu yi iya ƙoƙarinmu domin mu kasance da aminci a matsayin talakawan Mulkin Allah. Idan muka yi hakan, za mu amfana daga sarautar da babu irinta har abadan abadin!