Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Wata ’yar’uwa a Alabama, Amirka, ta saka faifain jawabin Dan’uwa Rutherford, a shekara ta 1930; Dama: Siwizalan

SASHE NA 1

Gaskiya Game da Mulki​— Yin Tanadin Abubuwan da Za Su Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah

Gaskiya Game da Mulki​— Yin Tanadin Abubuwan da Za Su Ƙarfafa Dangantakarmu da Allah

A CE ka karanta wa ɗalibinka wani nassi kuma sai ya kalle ka cike da mamaki domin yadda ya fahimci batun da kuka tattauna. Sai ya ce, “Kana nufin Littafi Mai Tsarki yana koyar da cewa za mu yi rayuwa a Aljanna a wannan duniyar har abada?” Sai wanda kuke wa’azi tare ya yi murmushi kuma ya ce, “Me ka karanta a Littafi Mai Tsarki yanzu?” Cike da mamaki ɗalibinka ya kaɗa kansa ya ce, “A gaskiya ban taɓa sanin hakan ba sai yau.” Sai ka tuna cewa ya yi irin wannan furucin ’yan makonnin da suka shige sa’ad da ya koyi cewa sunan Allah shi ne Jehobah.

Hakan ya taɓa faruwa da kai kuwa? Bayin Allah da yawa sun shaida hakan. Wasu abubuwa za su iya tuna mana da kyauta mai tamani da muke da ita, wato gaskiyar da aka koya mana daga Littafi Mai Tsarki! Ka ɗan dakata ka yi tunani a kan wannan tambayar: Ta yaya ka sami wannan kyautar? Za mu tattauna tambayar nan a wannan sashen. Yadda bayin Allah suke samun ƙarin haske game da koyarwar Allah da sannu-sannu yana tabbatar da mu cewa an kafa Mulkin Allah. A cikin shekaru ɗari yanzu, Sarki, Yesu Kristi, yana aiki wurjanjan don ya ga cewa an koya wa bayin Allah gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

A WANNAN SASHEN

BABI NA 3

Jehobah Ya Bayyana Nufinsa

Mulkin yana cikin shirin da Allah ya yi da farko kuwa? Ta yaya Yesu ya ba da ƙarin haske a kan Mulkin?

BABI NA 4

Jehobah Ya Ɗaukaka Sunansa

Mene ne Mulkin Allah ya cim ma game da sunan Allah? Ta yaya za ka saka hannu wajen tsarkake sunan Jehobah?

BABI NA 5

Sarkin Yana Bayyana Mana Mulkin Dalla-dalla

Ka sami ƙarin bayani game da Mulkin, masu sarautan da talakawan da kuma ma’anar kasancewa da aminci ga Mulkin.