Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Lokacin da iyalin Bethel da ke Brooklyn sun bikin Kirsimati na ƙarshe a 1926; dama: Mutane sun lura cewa Shaidun Jehobah sun fita dabam

SASHE NA 3

Ƙa’idodin Mulkin​—⁠Biɗan Adalcin Allah

Ƙa’idodin Mulkin​—⁠Biɗan Adalcin Allah

YAYIN DA kake wucewa, ka ɗaga wa maƙwabcinka hannu. A kwana kwanan nan, ka lura cewa yana yawan kallon kai da iyalinka. Shi ma ya ɗaga maka hannu sai ya ce ka zo. Da ka zo, sai ya ce maka: “Ina so in yi maka wata tambaya. Me ya sa kun bambanta da sauran mutane?” Sai ka ce, “Ban gane abin da kake nufi ba.” Ya ce, “Ku Shaidun Jehobah ne ko? Kun bambanta da sauran mutane. Ba ku yin sha’ani da sauran addinai, ba ku yin bukukuwa kuma ba ruwanku da siyasa da kuma yaƙi. Na kuma lura cewa ba ku shan taba sigari. Kuma iyalinka suna da ɗabi’a mai kyau. Me ya sa kuka fita dabam haka?”

Ka san cewa dalilin shi ne: Mu talakawan Mulkin Allah ne. Yesu Kristi wanda shi ne Sarkinmu yana mana gyara a kai a kai. Yana taimaka mana mu bi tafarkinsa kuma mu fita dabam da mutanen wannan muguwar duniya. A wannan sashen, za mu ga yadda Mulkin Almasihu yake yi wa bayin Allah gyara a ibadarsu da ɗabi’arsu da kuma a yadda ƙungiyar take tafiyar da al’amura domin ta ɗaukaka Jehobah.

A WANNAN SASHEN

BABI NA 10

Sarkin Ya Tsabtace Ibadar Mutanensa

Daga ina bikin Kirsimati da kuma gicciye suka samo tushensu?

BABI NA 11

Yin Gyara a Dabi’a Ya Nuna Cewa Allah Mai Tsarki Ne

Dakunan tsaro da kofofin haikali da Ezekiyel ya gani a wahayi suna da ma’ana ta musamman ga bayin Allah tun daga 1914.

BABI NA 12

An Tsara Su Don Su Yi wa ‘Allah na Salama’

Littafi Mai Tsarki ya bambanta yamutsi ba da tsari ba, amma da salama. Me ya sa? Ta yaya amsar ta shafi Kiristoci a yau?