Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Hagu: Wani ɗan’uwa da aka kama sa’ad da yake wa’azi a birnin Eindhoven da ke ƙasar Holan, a shekara ta 1945; dama: Shin kuna da ’yancin yin wa’azi a yankinku?

SASHE NA 4

Nasarorin da Mulkin Ya Yi​—⁠Yadda Aka Tabbatar da Bishara ta Yin Shari’a

Nasarorin da Mulkin Ya Yi​—⁠Yadda Aka Tabbatar da Bishara ta Yin Shari’a

A CE kana wa’azi gida-gida, sai ka ji ƙarar jiniyar motar ’yan sanda daga nesa kuma ƙarar sai daɗa kusa take yi. Yayin da ka soma yi wa wani maigida wa’azi, sai ka lura cewa hankalin abokin wa’azinka ya rabu domin ’yan sandan sun zo sun faka motarsu kusa da ku. Ɗaya daga cikinsu ya fito ya tambaye ku: “Ku ne kuke zuwa gida-gida kuna magana game da Littafi Mai Tsarki? An sha kawo ƙarar ku wajenmu!” Sai kuka ba da amsa cikin ladabi kuma kuka bayyana cewa ku Shaidun Jehobah ne. Bayan hakan, me zai faru?

Babu shakka, hakan dangana ne da tarihin Shaidun Jehobah a ƙasarku. Ta yaya hukumar da ke ƙasarku ta bi da Shaidun Jehobah a shekarun da suka gabata? Akwai ’yancin addini a ƙasarku kuwa? Idan amsarka E ce, to wataƙila abin da ya taimaka shi ne yadda ’yan’uwanka Shaidun Jehobah suka ƙoƙarta wajen yin “kariyar bishara da tabbatar da ita” a cikin shekarun da suka shige. (Filib. 1:7, Littafi Mai Tsarki) A duk inda kake da zama, idan ka yi tunani a kan nasarar da Shaidun Jehobah suka yi a kotu hakan zai ƙarfafa bangaskiyarka. A wannan sashen, za mu tattauna wasu cikin nasarori masu muhimmanci da aka yi. Waɗannan nasarorin sun ba da tabbaci cewa Mulkin Allah ba ƙage ba ne, domin da a ce mun dogara ga kanmu, da ba za mu taɓa yin waɗannan nasarorin ba!

A WANNAN SASHEN

BABI NA 13

Masu Wa’azin Mulkin Sun Kai Ƙara Kotu

Ra’ayin alƙalai a wasu manyan kotuna na zamani ya zo ɗaya da na babban malami na dā mai suna Gamaliel.

BABI NA 14

Sun Goyi Bayan Mulkin Allah Ne Kaɗai

An kawo ƙarshen tsanantawa da Shaidun Jehobah suke fuskanta don sun ƙi yin siyasa, kuma ta hannun waɗanda ba a zata ba

BABI NA 15

Gwagwarmaya don Samun ’Yancin Yin Ibada

Bayin Allah sun yi gwagwarmaya don samun ’yancin yin biyayya ga dokokin Mulkin Allah.