Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Mulkin Allah?

Mene Ne Mulkin Allah?

Shin za ka ce . . .

  • wani abu ne da ke cikin zuciyarka?

  • wani wuri ne a sama?

  • gwamnati ce a sama?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE

“Allah na sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada.”—Daniyel 2:44, Littafi Mai Tsarki.

‘An haifa mana yaro, mulkin za ya kasance a kafaɗarsa.’—Ishaya 9:6.

ABIN DA ZA KA IYA MORA

  • Gwamnati mai adalci wadda za ta amfane ka.—Ishaya 48:17, 18.

  • A sabuwar duniyar da ke tafe, za ka yi rayuwa cikin ƙoshin lafiya da farin ciki.—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

ZA MU IYA GASKATA DA LITTAFI MAI TSARKI KUWA?

Hakika, aƙalla saboda waɗannan dalilai biyu:

  • Yesu ya nuna abin da Mulkin Allah zai cim ma. Yesu ya koya wa mabiyansa su riƙa addu’a cewa Mulkin Allah ya zo kuma nufin Allah ya cika a duniya. (Matta 6:9, 10) Yesu ya nuna yadda za a amsa wannan addu’ar.

    Sa’ad da yake duniya, Yesu ya ciyar da mayunwata, ya warkar da marasa lafiya, kuma ya ta da matattu! (Matta 15:29-38; Yohanna 11:38-44) A matsayin Sarkin Mulkin Allah mai jiran gado, Yesu ya ɗan nuna abubuwa masu kyau da Mulkin zai yi wa talakawansa.—Ru’ya ta Yohanna 11:15.

  • Yanayin duniya ya tabbatar da cewa Mulkin Allah zai zo ba da daɗewa ba. Yesu ya annabta cewa gab da lokacin da Mulkin zai kawo zaman lafiya a duniya, yaƙe-yaƙe, matsananciyar yunwa, da girgizar ƙasa za su addabi duniyarmu.—Matta 24:3, 7.

    Muna ganin abubuwan nan a yau. Shi ya sa muke da tabbaci cewa Mulkin Allah zai kawo ƙarshen dukan matsalolin nan ba da daɗewa ba.

KA YI TUNANI A KAN WANNAN TAMBAYAR

Ya rayuwa za ta kasance a karkashin Mulkin Allah?

Littafi Mai Tsarki y aba da amsar a ZABURA 37:29 da kuma ISHAYA 65:21-23.