Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?

Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?

IDAN kana karanta jarida ko kana kallon telibijin ko kuma kana sauraron rediyo, za ka riƙa ji ko ka ga labaran zalunci da yaƙe-yaƙe da kuma ta’addanci. Wataƙila kai ma kana shan wahala sanadiyyar rashin lafiya ko kuma don wani abokinka ko danginka ya rasu.

Za ka iya tunani:

  • Shin irin yanayin da Allah yake so ni da iyalina mu kasance a ciki ke nan?

  • A ina zan sami taimako don in magance matsalolina?

  • Za a taɓa samun salama a duniya kuwa?

Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyin.

LITTAFI MAI TSARKI YA CE ALLAH ZAI YI ABUBUWA MASU BAN MAMAKI A DUNIYA.

  • Mutane ba za su ƙara shan wahala ko tsufa ko kuma mutuwa ba.—Ru’ya ta Yohanna 21:4

  • “Gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa.”—Ishaya 35:6

  • “Za a buɗe idanun makafi.”—Ishaya 35:5

  • Za a ta da matattu.—Yohanna 5:28, 29

  • Ba wanda zai sake yin ciwo.—Ishaya 33:24

  • Kowa zai sami isashen abinci a duniya.—Zabura 72:16

KA AMFANA DAGA KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI

Za ka iya yin tunani cewa abin da ka karanta ɗazun nan ba zai taɓa faruwa ba. Amma Allah ya riga ya yi alkawari cewa zai yi waɗannan abubuwan a duniya nan ba da daɗewa ba kuma Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda zai yi hakan.

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana fiye da hakan ma. Ya gaya mana abin da ya kamata mu sani don mu yi farin ciki kuma mu more rayuwa yanzu. Ka yi tunanin abubuwan da suke damunka, waɗanda suka ƙunshi matsalar kuɗi da ciwo da kuma rasuwar wani abokinka ko danginka. Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka jimre waɗannan matsalolin kuma zai iya ƙarfafa ka ta wajen amsa tambayoyi kamar su:

Nazarin littafin nan da kake yi ya nuna cewa kana son ka san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Hakika, littafin nan zai taimaka maka ka yi hakan. Akwai tambayoyi a kowane sakin layi da za su iya taimaka maka ka fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. Miliyoyin mutane suna jin daɗin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Muna fatan kai ma za ka ji daɗin yin hakan. Bari Allah ya albarkace ka yayin da kake ƙoƙarin gane abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.