Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA HUƊU

Wane ne Yesu Kristi?

Wane ne Yesu Kristi?

1, 2. (a) Shin sanin wani da ya yi suna yana nufin cewa ka san shi sosai? Ka bayyana. (b) Waɗanne ra’ayoyi dabam-dabam ne mutane suke da shi game da Yesu?

AKWAI mutane da yawa a duniya da suka yi suna. Wataƙila ka san ɗaya daga cikinsu. Amma sanin sunan mutum kawai ba ya nufin cewa ka san shi sosai. Hakan ba ya nufin cewa ka san kome game da rayuwarsa da kuma halayensa.

2 Wataƙila ka taɓa jin labarin Yesu ko da yake ya rayu a duniya kusan shekara dubu biyu da suka shige. Amma yawancin mutane ba su san wane irin mutum ne Yesu ba. Wasu sun ce shi mutumin kirki ne kawai wasu kuma sun ce shi annabi ne. Ƙari ga haka, wasu sun gaskata cewa shi Allah ne. Mene ne ra’ayinka game da Yesu?—Ka duba Ƙarin bayani na 12.

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu san Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi?

3 Yana da muhimmanci ka san gaskiya game da Yesu. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yohanna 17:3) Hakika, idan ka san gaskiya game da Jehobah da kuma Yesu, za ka rayu a aljanna a duniya har abada. (Yohanna 14:6) Ƙari ga haka, sanin Yesu zai taimaka maka don shi ne ya kafa misali mafi kyau na yadda za mu yi rayuwa da kuma bi da mutane. (Yohanna 13:34, 35) Mun koyi gaskiya game da Allah a Babi na 1. Yanzu kuma za mu koya abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu.

MUN SAMI ALMASIHU!

4. Mene ne ma’anar laƙabin nan “Almasihu” da kuma “Kristi”?

4 Shekaru da dama kafin a haifi Yesu, Jehobah ya yi alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa zai aiko da Almasihu ko Kristi. “Almasihu” kalmar Ibrananci ne, “Kristi” kuma kalmar Helenanci ne. Waɗannan laƙabin suna nufin cewa Allah zai zaɓi Almasihu kuma ya ba shi matsayi na musamman. Almasihu zai sa dukan alkawuran Allah su cika. Yesu zai kuma iya taimaka maka yanzu. Amma kafin a haifi Yesu, mutane da yawa sun yi tunani, ‘Wane ne zai zama Almasihu?’

5. Shin almajiran Yesu sun amince cewa shi Almasihu ne?

5 Almajiran Yesu ba su yi shakka cewa Yesu ne Almasihu ba. (Yohanna 1:41) Alal misali, Siman Bitrus ya gaya wa Yesu: “Kai Kristi ne.” (Matta 16:16) Ta yaya za mu tabbata cewa Yesu ne Almasihu?

6. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa mutanen kirki su gane Almasihu?

6 Shekaru da yawa kafin a haifi Yesu, annabawan Allah sun yi bayanai da za su taimaka wa mutane su gane Almasihu. Ta yaya hakan zai taimaka wa mutane? Alal misali, a ce an gaya maka ka je tashar mota ka ɗauko wani baƙo da ba ka taɓa gani ba. Idan an kwatanta maka mutumin da kyau, babu shakka, za ka iya gane shi har ku zo tare. Hakazalika, Jehobah ya yi amfani da annabawa don su faɗa abin da Almasihu zai yi da kuma abin da zai same shi. Yadda dukan annabcin suka cika ya taimaka wa mutanen kirki su gane Almasihu.

7. Waɗanne annabci biyu ne suka tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu?

7 Ga biyu cikin waɗannan annabcin. Da farko, shekara ɗari bakwai kafin a haifi Yesu, Mikah ya yi annabci cewa za a haifi Almasihu a wani ƙaramin gari a Bai’talami. (Mikah 5:2) Kuma a wurin ne aka haifi Yesu. (Matta 2:1, 3-9) Na biyu, Daniyel ya annabta cewa Almasihu zai bayyana a shekara ta 29. (Daniyel 9:25) Waɗannan biyu ne kawai cikin annabci da yawa da suka tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu da aka yi alkawarinsa.—Ka duba Ƙarin bayani na 13.

Yesu ya zama Almasihu ko Kristi sa’ad da ya yi baftisma

8, 9. Me ya faru a lokacin da Yesu ya yi baftisma da ya tabbatar da cewa shi ne Almasihu?

8 Jehobah ya bayyana dalla-dalla cewa Yesu ne Almasihu. Allah ya yi alkawarin nuna wa Yohanna Mai-baftisma alamar da za ta sa ya san ko waye ne Almasihu. Yohanna ya ga wannan alamar sa’ad da Yesu ya zo wurinsa a Kogin Urdun a shekara ta 29 don a yi masa baftisma. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Yesu kuwa, sa’anda aka yi masa baftisma, ya fita daga cikin ruwa nan da nan kuwa sammai suka buɗe masa, ya ga ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya yana zuwa bisansa; ga kuwa murya daga cikin sammai, ta ce, Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” (Matta 3:16, 17) A lokacin da Yohanna ya ga alamar kuma ya ji muryar Allah, sai ya gane cewa Yesu ne Almasihu. (Yohanna 1:32-34) Jehobah ya shafe Yesu da ruhunsa a ranar kuma ya zama Almasihu. Shi ne Allah ya zaɓa ya zama Shugaba da kuma Sarki.—Ishaya 55:4.

9 Annabcin Littafi Mai Tsarki da maganar da Jehobah ya yi da kuma alamar da Jehobah ya nuna a lokacin da Yesu ya yi baftisma sun tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu. Amma daga ina ne Yesu ya fito, kuma wane irin mutumi ne shi? Bari mu tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.

DAGA INA NE YESU YA FITO?

10. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da rayuwar Yesu kafin ya zo duniya?

10 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Yesu ya yi shekaru da yawa a sama kafin ya zo duniya. Annabi Mikah ya ce asalin Almasihu “tun daga zamanin dā” ne. (Mikah 5:2) Yesu da kansa ma ya faɗi sau da yawa cewa ya yi rayuwa a sama kafin ya zo duniya. (Karanta Yohanna 3:13; 6:38, 62; 17:4, 5.) Kafin Yesu ya zo duniya, yana da dangantaka mai kyau da Jehobah.

11. Me ya sa Jehobah yake ƙaunar Yesu sosai?

11 Jehobah yana ƙaunar Yesu sosai. Me ya sa? Domin Allah ya halicce shi kafin aka yi sauran abubuwa. Saboda haka, ana kiran Yesu “ɗan fari ne gaban dukan halitta.” * (Kolosiyawa 1:15) Jehobah yana kuma ƙaunar Yesu don shi ne kaɗai ya halitta da kansa. Shi ya sa ake kiransa Ɗa ‘makaɗaici.’ (Yohanna 3:16, Littafi Mai Tsarki) Ƙari ga haka, Yesu ne kaɗai Jehobah ya yi amfani da shi don ya halicci sauran abubuwa. (Kolosiyawa 1:16) Kuma Yesu ne kaɗai aka kira ‘Kalma,’ domin Jehobah ya yi amfani da shi wajen ba da saƙonni da umurni ga mala’iku da kuma mutane.—Yohanna 1:14.

12. Ta yaya muka san cewa matsayin Yesu da na Allah ba ɗaya ba ne?

12 Wasu mutane sun gaskata cewa matsayin Yesu da na Allah ɗaya ne. Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗi hakan ba. Littafi Mai Tsarki ya ce an halicci Yesu ne kuma hakan ya nuna cewa Yesu yana da farko. Amma Jehobah, wanda ya halicci dukan abu ba shi da farko. (Zabura 90:2) Yesu Ɗan Allah ne kuma bai taɓa ce shi Allah maɗaukaki ne ba. Littafi Mai Tsarki ya koyar dalla-dalla cewa Uban ya fi Ɗan girma. (Karanta Yohanna 14:28; 1 Korintiyawa 11:3.) Jehobah ne kaɗai “Allah Mai Iko Duka.” (Farawa 17:1, LMT) Shi ne mafi girma da kuma mafi iko a sama da duniya.—Ka duba Ƙarin bayani na 14.

13. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu “surar Allah marar ganuwa” ne?

13 Jehobah da Ɗansa Yesu, sun yi aiki tare na biliyoyin shekaru kafin a halicci sama da ƙasa. Babu shakka, sun ƙaunaci juna sosai. (Yohanna 3:35; 14:31) Yesu ya yi koyi da halayen ubansa sosai shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira shi “surar Allah marar ganuwa.”—Kolosiyawa 1:15.

14. Ta yaya aka haifi Ɗan Allah a duniya?

14 Yesu wanda shi ne Ɗa da Jehobah yake ƙauna ya amince ya bar sama kuma ya zo duniya don a haife shi a matsayin mutum. Ta yaya hakan ya faru? Jehobah ya ƙaurar da ran Ɗansa daga sama zuwa mahaifar wata budurwa mai suna Maryamu ta hanyar mu’ujiza. Ta hakan, Yesu bai bukaci uba ɗan Adam ba. Saboda haka, Maryamu ta haifi ɗa marar zunubi kuma ta sa masa suna Yesu.—Luka 1:30-35.

WANE IRIN MUTUMI NE YESU?

15. Me zai taimaka maka ka san Jehobah da kyau?

15 Za ka iya koyan abubuwa da yawa game da Yesu da rayuwarsa da kuma halayensa ta wajen karanta littafin Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna. Ana kiran waɗannan littattafan Linjila. Da yake Yesu yana kamar Ubansa, abin da za ka karanta zai taimaka maka ka san Jehobah da kyau. Shi ya sa Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”—Yohanna 14:9.

16. Mene ne Yesu ya koyar? Daga ina ne Yesu ya samo koyarwarsa?

16 Mutane da yawa sun kira Yesu “Malami.” (Yohanna 1:38; 13:13) Ɗaya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da Yesu ya koyar shi ne “bishara ta mulkin.” Mene ne wannan Mulkin? Gwamnatin Allah ce da za ta yi sarauta bisa duniya kuma za ta kawo albarka ga waɗanda suka yi biyayya da Allah. (Matta 4:23) Dukan abubuwan da Yesu ya koyar daga Jehobah ne. Yesu ya ce: Abin da na ‘koyar ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.’ (Yohanna 7:16) Yesu ya san cewa Jehobah yana son mutane su ji albishirin nan cewa Mulkin Allah zai yi sarauta bisa duniya.

17. A ina ne Yesu ya koyar da mutane? Me ya sa Yesu ya yi aiki tuƙuru don ya koyar da mutane?

17 A ina ne Yesu ya yi wa’azi? A duk inda ya sami mutane. Ya yi wa’azi a birane da ƙauyuka da kasuwa da haikali da majami’u da kuma gidajen mutane. Bai jira mutane su zo wurinsa ba, maimakon haka, shi yake zuwa wurinsu. (Markus 6:56; Luka 19:5, 6) Yesu ya yi aiki tuƙuru kuma ya ba da lokaci sosai da kuzari wajen koyar da mutane. Me ya sa? Don ya san cewa Allah yana so ya yi hakan kuma yana wa Allah biyayya a koyaushe. (Yohanna 8:28, 29) Yesu ya kuma yi wa’azi don ya ji tausayin mutane. (Karanta Matta 9:35, 36.) Ya lura cewa shugabannin addinan ba sa koyar da gaskiya game da Allah da kuma Mulkinsa. Saboda haka, ya so ya taimaka wa mutane da yawa su ji bishara.

18. Waɗanne cikin halayen Yesu ne ka fi so?

18 Yesu mai ƙauna ne da kuma mai kula da mutane. Shi mai kirki ne da kuma fara’a. Yara ma sun so kasancewa tare da shi. (Markus 10:13-16) Yesu bai wulaƙanta mutane ba. Ya tsani cin hanci da rashin adalci. (Matta 21:12, 13) Ya yi rayuwa a lokacin da mata ba su da ’yanci kuma ba a ɗaukan su da wani muhimmanci. Amma a koyaushe, Yesu yana mutunta mata. (Yohanna 4:9, 27) Yesu kuma mai tawali’u ne sosai. Alal misali, Yesu ya wanke kafaffun manzanninsa, kuma wannan aiki ne da bayi suke yi a lokacin.—Yohanna 13:2-5, 12-17.

Yesu ya yi wa’azi a duk inda ya ga mutane

19. Wane misali ne ya nuna cewa Yesu ya san abin da mutane suke bukata kuma yana so ya taimaka musu?

19 Yesu ya san abin da mutane suke bukata kuma yana so ya taimaka musu. An ga wannan dalla-dalla sa’ad da Yesu ya yi amfani da ikon Allah wajen yin mu’ujiza. (Matta 14:14) Alal misali, akwai lokacin da wani kuturu ya roƙi Yesu, ya ce: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Yesu ya ji tausayin mutumin nan da yake wahala kuma ya so ya taimake shi. Sai Yesu ya miƙa hannunsa ya riƙe shi, ya ce masa: “Na yarda; ka tsarkaka.” Nan da nan mutumin ya warke. (Markus 1:40-42) Babu shakka, mutumin ya yi farin ciki sosai, ko ba haka ba?

YA YI BIYAYYA GA UBANSA A KOYAUSHE

20, 21. Me ya nuna cewa Yesu ya kafa misali mafi kyau na yin biyayya?

20 Yesu ya kafa mana misali mafi kyau a yin biyayya ga Allah. Ya kasance da aminci ga Ubansa duk da abubuwan da maƙiyansa suka yi masa. Alal misali, Yesu bai yi zunubi ba sa’ad da Shaiɗan ya so ya yaudare shi. (Matta 4:1-11) Wasu cikin danginsa ba su yarda cewa shi ne Almasihu ba kuma sun ce “ya ruɗe.” Duk da haka, Yesu ya ci gaba da yin nufin Allah. (Markus 3:21) Sa’ad da maƙiyansa suka yi masa mugunta, Yesu bai rama ba amma ya kasance da aminci.—1 Bitrus 2:21-23.

21 Yesu ya kasance da aminci ga Jehobah, har a lokacin da ya sha wulaƙanci da azaba kafin ya mutu. (Karanta Filibiyawa 2:8.) Ka yi tunanin irin wahalar da ya sha kafin ya mutu. An kama shi, aka masa sharri kuma alƙalai masu cin hanci suka hukunta shi, taron ’yan iska suka yi masa dariya, kuma daga baya sojoji suka kafa shi a kan gungume. Sa’ad da ya kusan mutuwa, ya yi kuka ya ce: “An gama”! (Yohanna 19:30) Bayan Yesu ya yi kwana uku a cikin kabari, Jehobah ya ta da shi da jiki na ruhu. (1 Bitrus 3:18) ’Yan makonni bayan da aka ta da Yesu, ya koma sama “ya zauna ga hannun dama na Allah” kuma yana jira Allah ya naɗa shi Sarki.—Ibraniyawa 10:12, 13.

22. Wane bege ne muke da shi a yau domin Yesu ya kasance da aminci ga Ubansa?

22 Yesu ya kasance da aminci sosai ga Ubansa, hakan ya sa mu kasance da begen yin rayuwa a duniya har abada yadda Jehobah ya nufa tun asali. A babi na gaba, za mu tattauna yadda mutuwar Yesu ta ba mu damar yin rayuwa har abada.

^ sakin layi na 11 Ba zai dace ba a ce Allah yana da ɗa ta wurin jima’i da mace ko kuma ya yi aure ya samu yara ba. Domin Allah Ruhu ne. Kalmomi kamar su “ɗa” da “ɗan’uwa” da kuma “uba” da dai sauransu suna iya kasance da wata ma’ana dabam. Alal misali, manya suna iya kiran mutanen da ke ƙasa da su ɗana ko ’yata, amma hakan ba ya nufin cewa su suka haife su. “Ɗan ƙasa” ba ya nufin cewa ƙasar ce ta haifi mutumin ba, amma ƙasar haihuwarsa ce. Ana kiran Jehobah Uba a cikin Littafi Mai Tsarki domin shi ne Mahalicci. (Ishaya 64:8) Ana kiran Yesu Ɗan Allah don Jehobah ne ya halicce shi. Ana kuma kiran mala’iku da mutane ’ya’yan Allah.—Ayuba 1:6; Romawa 8:14.