Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA TAKWAS

Mene ne Mulkin Allah?

Mene ne Mulkin Allah?

1. Wace addu’a ce za mu tattauna yanzu?

MILIYOYIN mutane sun san addu’ar da ake kira Addu’ar Ubangiji. Yesu ya yi wannan addu’ar ne don ya koya wa almajiransa yin addu’a. Mene ne ya ambata a addu’ar? Kuma me ya sa addu’ar take da muhimmanci a gare mu?

2. Waɗanne muhimman abubuwa uku ne Yesu ya ce mu roƙa?

2 Yesu ya ce: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.” (Karanta Matta 6:9-13.) Me ya sa Yesu ya ce mu yi addu’a a kan waɗannan abubuwa uku?—Ka duba Ƙarin bayani na 20.

3. Me muke bukata mu sani game da Mulkin Allah?

3 Mun koyi cewa sunan Allah shi ne Jehobah. Ƙari ga haka, mun tattauna dalilin da ya sa Allah ya halicci mutane da kuma duniya. Amma me Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Mulkinka shi zo”? Bari mu tattauna ma’anar Mulkin Allah da abin da zai yi da kuma yadda zai tsarkake sunan Allah.

MENE NE MULKIN ALLAH?

4. Mene ne Mulkin Allah, kuma waye ne sarkin Mulkin?

4 Jehobah ya kafa gwamnati a sama kuma ya naɗa Yesu ya yi sarauta. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan gwamnatin Mulkin Allah. Yesu ne “Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji.” (1 Timotawus 6:15) Yesu ya fi kowane sarkin da ya taɓa sarauta a wannan duniyar iko, don haka, zai iya yin abin da sarakunan duniya duka ba za su iya yi ba.

5. Daga ina ne Mulkin zai yi sarauta? Kuma zai yi sarauta bisa ina?

5 Yesu ya koma sama bayan kwana arba’in da ya tashi daga mutuwa. Bayan haka, Jehobah ya naɗa shi ya zama Sarkin Mulkinsa. (Ayyukan Manzanni 2:33) Mulkin Allah yana sama kuma zai yi sarauta bisa duniya. (Ru’ya ta Yohanna 11:15) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira Mulkin Allah ‘Mulkin sama.’—2 Timotawus 4:18.

6, 7. Me ya sa Yesu ya fi kowane sarki da ya taɓa sarauta a duniya?

6 Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya fi kowane sarki da ya taɓa sarauta a duniya girma don shi ne “kaɗai marar mutuwa.” (1 Timotawus 6:16, Littafi Mai Tsarki) Dukan sarakuna a duniya suna mutuwa, amma Yesu ba zai taɓa mutuwa ba. Dukan alherin da Yesu zai yi mana za su dawamma har abada.

7 Annabcin Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu zai zama nagarin Sarki da kuma mai tausayi: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun ilimi da na ganewa, ruhun shawara da iko, ruhun sani da na tsoron Ubangiji: jin daɗinsa kuma za ya kasance a cikin tsoron Ubangiji: ba za ya yi shari’a bisa ga abin da ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka magana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba: amma da adalci za ya yi wa talakawa shari’a.” (Ishaya 11:2-4) Shin za ka so Sarkinku ya kasance da irin waɗannan halayen?

8. Ta yaya muka sani cewa Yesu ba zai yi sarauta shi kaɗai ba?

8 Allah ya zaɓi wasu mutane daga duniya su yi sarauta tare da Yesu a sama. Alal misali, manzo Bulus ya gaya wa Timotawus: “Idan mun jimre, za mu kuma yi mulki tare da shi.” (2 Timotawus 2:12) Mutane nawa ne za su yi sarauta tare da Yesu?

9. Mutane nawa ne za su yi sarauta tare da Yesu? Yaushe ne Allah ya soma zaɓansu?

9 Kamar yadda muka tattauna a Babi na 7, an saukar wa manzo Yohanna wahayi kuma ya ga Yesu a matsayinsa na Sarki a sama tare da abokan sarautarsa dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu. Su waye ne waɗannan mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu? Yohanna ya bayyana cewa suna da ‘sunan [Yesu], da sunan Ubansa, a rubuce bisa goshinsu.’ Bugu da ƙari, ya ce: ‘Su ne sukan bi Ɗan rago [wato, Yesu] inda ya tafi duka.’ Su ne aka zaɓa “daga cikin mutane.” (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:1, 4.) Mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu, shafaffun Kiristoci ne da Allah ya zaɓa don su yi “mulki bisa duniya” tare da Yesu. Idan suka mutu, ana ta da su zuwa sama. (Ru’ya ta Yohanna 5:10) Jehobah ya soma zaɓan Kiristoci masu aminci tun ƙarni na farko don su cika adadin sarakunan nan dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu.

10. Me ya sa yadda Jehobah ya zaɓi Yesu da kuma mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu su yi sarauta bisa duniya ya dace?

10 Jehobah yana ƙaunarmu sosai shi ya sa ya yi shirye-shirye don mutane su yi sarauta da Yesu. Yesu zai zama nagarin sarki domin ya fahimci yanayinmu sosai. Ya taɓa rayuwa a duniya, don haka ya san yadda ake shan wahala. Manzo Bulus ya ce Yesu ya san yanayinmu, “shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne” kuma an “jarabe shi ta kowace hanya da aka jarabce mu.” (Ibraniyawa 4:15; 5:8, LMT) Waɗannan mutane dubu ɗari da dubu arba’in da huɗu ma sun san yanayin mutane. Kuma su ma sun yi fama da ajizanci da ciwo. Saboda haka, muna da tabbaci cewa Yesu da waɗannan abokan sarautarsa za su fahimci yanayinmu da kuma matsalolin da muke fama da su sosai.

MENE NE MULKIN ALLAH ZAI YI?

11. Me ya sa Yesu ya ce almajiransa su yi addu’a don a yi nufin Allah a sama?

11 Yesu ya ce almajiransa su yi addu’a don a yi nufin Allah a sama. Me ya sa? Mun tattauna a Babi na 3 cewa Shaiɗan ya yi tawaye ga Jehobah. Bayan haka, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan da miyagun mala’iku ko kuma aljannu su kasance a sama na ɗan lokaci. A lokacin, ba kowa ne a sama yake yin nufin Allah ba. A Babi na 10, za mu sami ƙarin bayani game da Shaiɗan da aljannu.

12. Waɗanne abubuwa biyu masu muhimmanci ne aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 12:10?

12 Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu zai yi yaƙi da Shaiɗan jim kaɗan bayan an naɗa shi Sarkin Mulkin Allah. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 12:7-10.) Aya ta 10 ta kwatanta abubuwa guda biyu masu muhimmanci. Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah a matsayin Sarki kuma an jefo da Shaiɗan daga sama zuwa duniya. Waɗannan abubuwan sun riga sun faru, kamar yadda za mu tattauna.

13. Mene ne ya faru a sama bayan da aka jefo Shaiɗan zuwa duniya?

13 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta irin farin cikin da mala’iku masu aminci suka yi bayan da aka jefo Shaiɗan da aljannunsa zuwa duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi farin ciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Yanzu akwai matuƙar farin ciki da haɗin kai a sama don kowa a wurin yana yin nufin Allah.

Mutane suna shan wahala a duniya tun lokacin da aka kori Shaiɗan da aljanunsa daga sama. Wannan wahalar za ta ƙare nan ba da daɗewa ba

14. Me ke faruwa a duniya don an jefo Shaiɗan daga sama?

14 Amma rayuwa yanzu a duniya tana da wuya. Munanan abubuwa suna faruwa “domin Shaiɗan ya sauko” kuma “hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Shaiɗan yana fushi sosai. An fitar da shi daga sama kuma ya san cewa nan ba daɗewa ba, za a halaka shi. Yana iya ƙoƙari don ya tayar da fitina da ciwo da kuma wahala a duniya.

15. Me ya sa Allah ya halicci duniya?

15 Amma dalilin da ya sa Allah ya halicci duniya bai canja ba. Har ila, yana so mutane su yi rayuwa a duniya har abada. (Zabura 37:29) Ta yaya Mulkin Allah zai sa hakan ya yiwu?

16, 17. Mene ne Daniyel 2:44 ya ce game da Mulkin Allah?

16 Annabcin da ke Daniyel 2:44 ya ce: “A cikin zamanin waɗannan sarakuna kuwa, Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar wa wata al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” Mene ne wannan annabcin ya koya mana game da Mulkin Allah?

17 Da farko, mun koya cewa Mulkin Allah zai soma sarauta a “zamanin waɗannan sarakuna.” Hakan yana nufin cewa wasu gwamnatoci za su riƙa sarauta a lokacin da za a kafa Mulkin Allah. Na biyu, mun koya cewa Mulkin Allah zai dawwama har abada kuma babu wani mulkin da zai sauya shi. Na uku kuma, Mulkin Allah zai yaƙi gwamnatocin ’yan Adam. Mulkin Allah zai yi nasara, kuma shi kaɗai ne zai yi sarauta bisa duniya. Bayan haka, ’yan Adam za su sami gwamnati mai kyau irin wanda ba a taɓa yi ba.

18. Mene ne sunan yaƙin ƙarshe da za a yi tsakanin Mulkin Allah da kuma gwamnatocin ’yan Adam?

18 Ta yaya Mulkin Allah zai kawar da sarautar ’yan Adam a duniya? Kafin a yi yaƙin ƙarshe da ake kira Armageddon, aljanu za su yaudari “sarakunan dukan duniya, garin su tattara su zuwa yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” Babu shakka, sarakunan ’yan Adam za su yi yaƙi da Mulkin Allah, amma Mulkin Allah zai yi nasara.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; ka duba Ƙarin bayani na 10.

19, 20. Me ya sa muke bukatar Mulkin Allah ya yi sarauta bisa duniya?

19 Me ya sa muke bukatar Mulkin Allah? Domin aƙalla dalilai uku. Na farko, mu masu zunubi ne, don haka muna ciwo da kuma mutuwa. Amma Littafi Mai Tsarki ya ce za mu rayu har abada a ƙarƙashin Mulkin Allah. Hakika, Yohanna 3:16 ya ce: “Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya halaka, sai dai ya sami rai madawwami.”

20 Dalili na biyu da ya sa muke bukatar Mulkin Allah shi ne don mugayen mutane sun cika duniya. Mutane da yawa suna yin ƙarya da cuwa-cuwa da kuma lalata. Allah ne kaɗai yake da iko ya halaka su. Za a halaka mutanen da suka ci gaba da yin munanan abubuwa a yaƙin Armageddon. (Karanta Zabura 37:10.) Dalili na uku da ya sa muke bukatar Mulkin Allah shi ne don gwamnatocin ’yan Adam azzalumai ne kuma sun lalace. Ba sa so su taimaka wa mutane su yi wa Allah biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce idan waɗansu sun ‘sami mulki, waɗansu kuwa suna shan wuya a ƙarƙashinsu.’—Mai-Wa’azi 8:9; LMT.

21. Ta yaya Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya?

21 Bayan yaƙin Armageddon, Mulkin Allah zai sa a yi nufin Allah a duniya. Alal misali, zai cire Shaiɗan da aljanunsa. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) A hankali, ciwo da kuma mutuwa za su zama labari. Fansar Yesu za ta sa ya yiwu dukan masu adalci su yi rayuwa a Aljanna har abada. (Ru’ya ta Yohanna 22:1-3) Mulkin zai tsarkake sunan Allah. Mene ne ma’anar hakan? Hakan yana nufin cewa a lokacin da gwamnatin Allah za ta yi sarauta bisa duniya, dukan mutane za su ɗaukaka sunan Jehobah.—Ka duba Ƙarin bayani na 21.

YAUSHE NE YESU YA ZAMA SARKI?

22. Ta yaya muka san cewa Yesu bai zama Sarki sa’ad da yake duniya ba ko kuma nan da nan bayan da aka ta da shi daga mutuwa?

22 Yesu ya ce almajiransa su yi addu’a cewa: “Mulkinka shi zo.” Hakan ya nuna sarai cewa a nan gaba, za a kafa gwamnatin Allah. Da farko, Jehobah zai kafa gwamnatinsa kuma ya naɗa Yesu ya zama Sarki. Shin da zarar Yesu ya koma sama ne aka naɗa shi sarki? A’a, ya ɗan jira tukuna. Bayan da aka ta da Yesu daga mutuwa, Bitrus da Bulus sun bayyana hakan sa’ad da suka ce Zabura 110:1 tana magana ne game da Yesu. A annabcin Jehobah ya ce: “Ka zauna ga hannun damana, har in maida maƙiyanka matashin sawayenka.” (Ayyukan Manzanni 2:32-35; Ibraniyawa 10:12, 13) Har tsawon wane lokaci ne Yesu zai jira kafin Jehobah ya naɗa shi Sarki?

Mulkin Allah zai sa a yi nufin Allah a duniya

23. (a) Yaushe ne Yesu ya soma sarauta a Mulkin Allah? (b) Mene ne za mu koya a babi na gaba?

23 Shekaru da yawa kafin 1914, wani rukunin Kiristoci sun san cewa wannan shekarar za ta kasance shekara ta musamman a annabcin Littafi Mai Tsarki. Abubuwan da ke faruwa a duniya tun daga shekara ta 1914 sun tabbatar da hakan. Yesu ya soma sarauta a wannan shekarar. (Zabura 110:2) Jim kaɗan bayan haka, Yesu ya jefo Shaiɗan zuwa duniya kuma yanzu, “zarafinsa kaɗan ya rage.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12) A babi na gaba, za mu ga ƙarin abubuwan da suka nuna cewa muna rayuwa ne a wannan lokacin. Za mu kuma koya cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin zai sa a yi nufin Allah a duniya.—Ka duba Ƙarin bayani na 22.