Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 5

Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?

Me Zan Yi Idan Aka Zolaye Ni a Makaranta?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Abin da ka yi zai iya sa a daina zolayarka ko kuma a ƙara zolayarka.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Thomas ba ya son zuwa makaranta kuma. A cikin watanni uku da suka wuce, ya samu kansa a cikin wani irin yanayi in da abokan makarantarsu suka yaɗa jita-jitar ƙarya game da shi. Sai suka soma kiransa da wasu sunaye. A wasu lokatai, wani zai kaɗe littattafan Thomas daga hannunsa kuma su zube amma mutumin zai yi kamar ba da gangan ya yi hakan ba. Ƙari ga haka, wani zai zo daga bayansa ya ture shi, amma idan Thomas ya juya, ba zai ga wanda ya tura shi ba. Jiya abin ya wuce gona da iri sa’ad da Thomas ya sami wani saƙon barazana a kwamfutarsa cewa . . .

Mene ne za ka yi idan ka sami kanka a yanayin da Thomas yake ciki?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Za ka iya yin wani abu! Ka san cewa za ka iya dūkan mai zolayarka ba tare da ka yi amfani da hannunka ba? Ta yaya za ka yi hakan?

  • KA ƘYALE SU. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wawa yakan furta dukan fushinsa; amma mai-hikima yakan danne shi ya kwaɓe shi.” (Misalai 29:11) Idan ba ka ce musu kome ba, waɗanda suke zolayarka za su daina.

  • KADA KA RAMA. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta.” (Romawa 12:17) Ramuwa za ta sa su ci gaba da zolayarka.

  • KADA KA JEFA KANKA CIKIN MATSALA. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali yakan hangi masifa, ya ɓuya.” (Misalai 22:3) Idan zai yiwu, ka guji mutanen da za su jefa ka cikin matsala da kuma yanayin da zai sa a zolaye ka.

  • KA BA SU AMSAR DA BA SA ZATO. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mayar da magana da taushi yakan juyar da hasala.” (Misalai 15:1) Kana iya faɗin abin ban dariya. Alal misali, idan mai zolayarka ya ce kana da ƙiba sosai, kana iya cewa, “Kar ka damu, zan rage ƙibar!”

  • KA BAR WURIN. Nora ’yar shekara 19 ta ce: “Idan ka yi shiru, hakan zai nuna cewa ka manyanta kuma ka fi wanda yake zolayarka hikima. Ƙari ga haka, yana nufin cewa kana kame kanka, halin da wanda yake zolayarka bai da shi.”—2 Timotawus 2:24.

  • KA KASANCE DA GABA GAƊI. Masu zolaya sun san waɗanda suke damuwa da abubuwan da suke musu da kuma waɗanda ba za su rama ba. Ƙari ga haka, masu zolaya za su daina yin hakan idan suka ga ba sa sa ka fushi.

  • KA GAYA WA WANI. Wani malamin makaranta a dā ya ce: “Zan shawarci wanda ake zolayarsa ya gaya wa wani. Abin da ya dace ke nan, kuma hakan zai iya hana zolayar.”

Kasancewa da gaba gaɗi zai ba ka ƙarfin zuciyar da mai zolayarka ba shi da shi