Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 6

Ta Yaya Zan Ki Matsi Daga Tsarana?

Ta Yaya Zan Ki Matsi Daga Tsarana?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Idan ka ƙi matsi daga tsaranka, hakan zai nuna cewa kai kake yanke wa kanka shawara ba wasu ba.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Brian ya tsorata sa’ad da ya ga wasu ’yan makarantarsu guda biyu sun nufo inda yake. Sau biyu a wannan makon sun yi ƙoƙarin matsa masa ya sha taba. Wannan shi ne na uku.

Yaro na farkon ya ce:

“Yau ma kai kaɗai ne? Bari in nuna maka wani abu.”

Sai ya kashe ido, ya ciro wani abu daga aljihunsa kuma ya miƙa wa Brian.

Brian ya ƙara tsorata sa’ad da ya ga sigari a hannun yaron.

Brian ya ce: “Ku yi haƙuri. Na riga na gaya maku cewa ba na . . .”

Sai yaro na biyun ya katse maganarsa kuma ya ce: “Ka daina wawanci mana!”

Da gaba gaɗi Brian ya ce: “Ni ba wawa ba ne.”

Sai yaro na biyun ya ɗora hannunsa a kafaɗar Brian kuma ya ce masa da murya mai daɗi: “Ka karɓi sigarin.”

Yaro na farko ya matso da sigarin kusa da fuskar Brian kuma ya ce: “Ba za mu gaya wa kowa ba. Babu wanda zai sani.”

Da a ce kai ne Brian, mene ne za ka yi?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Tsaran Brian sun san abin da suke yi kuwa? Shin su suka yanke wa kansu wannan shawarar? Da ƙyar. Su ma shawarar wasu suka bi. Saboda suna so su karɓu a wajen tsararsu, hakan ya sa su barin tsaransu su gaya musu abin da za su yi.

Idan ka fuskanci irin wannan yanayin, ta yaya za ka yi abin da ya dace kuma ka ƙi matsi daga tsaranka?

  1. KA YI TUNANIN ABIN DA ZAI IYA FARUWA

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali yakan hangi masifa, ya ɓuya: Amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya.”—Misalai 22:3.

    A yawancin lokaci, kana iya hangen masifa. Alal misali, a ce ka ga wasu ’yan makarantarku suna zuwa kuma suna shan sigari. Idan ka yi tunanin abin da zai iya faruwa, hakan zai sa ka kasance a shirye.

  2. KA YI TUNANI

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku . . . kasance da lamiri mai kyau.”—1 Bitrus 3:16, Littafi Mai Tsarki.

    Ka tambayi kanka, ‘Yaya zan ji idan na bi ra’ayin mutane?’ Hakika, kana iya yin abin da tsaranka suke so don ka sami karɓuwarsu na ɗan lokaci. Amma ya za ka ji daga baya? Shin za ka so ka yi abin da ba shi da kyau don ka faranta wa ’yan ajinku rai?—Fitowa 23:2.

  3. KA YANKE SHAWARA

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai hankali yana lura.”—Misalai 14:16, LMT.

    A kwana a tashi, za mu yanke shawara kuma mu fuskanci sakamakon. Littafi Mai Tsarki ya ambaci mutane kamar Yusufu da Ayuba da Yesu da suka yanke shawara mai kyau. Ƙari ga haka, ya ambaci Kayinu da Isuwa da Yahuda, waɗanda ba su yanke shawara mai kyau ba. Wace shawara ce kai za ka yanke?

Littafi Mai Tsarki ya ce: Ka kasance da “aminci.” (Zabura 37:3) Idan ka riga ka yi tunani a kan sakamakon kuma ka yanke shawara, gaya wa tsaranka game da matsayinka zai kasance da sauƙi kuma za ka amfana.

Kada ka damu, ba sai ka yi wa tsaranka wani dogon jawabi ba. Idan ka ce A’A da gaba gaɗi, hakan ma ya isa. Ko kuma idan kana so ka bayyana musu matsayinka dalla-dalla, kana iya cewa:

  • “Ba ruwa na!”

  • “Ba na yin irin wannan abin!”

  • “Haba, kai ma ka san cewa ba na sha!”

Abin da ya kamata ka yi shi ne ka gaya musu matsayinka nan da nan kuma da gaba gaɗi. Idan ka yi hakan, za ka yi mamaki cewa tsaranka za su daina matsa maka!

ABIN DA ZA KA YI IDAN AKA YI MAKA BA’A

Idan kana yin abin da tsaranka suka matsa maka ka yi, za ka zama kamar bawansu

Me za ka yi idan tsaranka suka yi maka ba’a? Idan suka ce, “Me haka, kana tsoro ne?” Ka san cewa suna faɗin hakan don su matsa maka ka yi abin da bai dace ba. Mene ne za ka yi idan hakan ya faru? Kana da zaɓi biyu.

  • Kana iya yarda da abin da suka ce. (“E, ina jin tsoro!” Bayan hakan, sai ka gaya musu dalilin da ya sa kake jin tsoro.)

  • Kana iya mai da martani. Ka gaya musu dalilin da ya sa ka ƙi, kuma ka faɗa musu abin da zai sa su tunani. (“Na zata ka fi ƙarfin shan sigari!”)

Idan tsaranka suka ci gaba da yi maka ba’a, ka yi tafiyar ka! Ka tuna cewa, idan ka tsaya a wurin, za su ci gaba da matsa maka. Amma idan ka bar wurin, hakan zai nuna cewa ka ƙi barin tsaranka su rinjaye ka.

Hakika, ba za ka iya guje wa matsi daga tsaranka ba. Amma za ka iya yanke shawara a kan abin da za ka yi. Ka bayyana ra’ayinka kuma ka yi abin da ya dace. A ƙarshe, dabara ta rage ga mai shiga rijiya!—Joshua 24:15.