Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 8

Me Ya Kamata In Sani Game da Cin Zarafi ta Hanyar Lalata?

Me Ya Kamata In Sani Game da Cin Zarafi ta Hanyar Lalata?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Ana cin zarafin miliyoyin mutane ta wajen yi musu fyaɗe ko kuma ta wata hanya dabam a kowace shekara, kuma matasa ne suka fi fuskantar wannan mugun yanayin. *

MENE NE ZA KI YI?

Wani mutum ya kama Annette kuma kafin ta sani, ya kayar da ita a ƙasa. Ta ce: “Na yi iya ƙoƙarina in kāre kaina. Na yi ƙoƙarin yin ihu, amma na kasa. Na yi ƙoƙarin in ture shi, kuma ina ta naushe-naushe. Ina cikin yin hakan, sai ya soke ni da wuƙa, kuma na sume.”

Idan kika sami kanki a irin wannan yanayin, mene ne za ki yi?

KI DAKATA KI YI TUNANI!

Idan kin fita daddare, ki riƙa lura sosai domin abin da ba ki yi zato ba zai iya faruwa. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsere, ba mai-sauri ke ci ba; yaƙi kuma, ba ga ƙarfafa yake ba; abinci kuma, ba ga masu-hikima ba; arziki kuma, ba ga masu-azanci ba; tagomashi kuma, ba ga masu-gwaninta ba: amma ga dukansu lokacinsu da zarafinsu sukan zo.”—Mai-Wa’azi 9:11.

Kamar Annette, wasu matasa suna fuskantar irin wannan cin zarafin ne daga mutanen da ba su taɓa gani ba. Wasu kuma abokansu ko kuma wani daga iyalinsu ne yake cin zarafinsu. Wani matashi da ke zama kusa da gidansu Natalie ya ci zarafinta sa’ad da take ’yar shekara goma. Ta ce: “Da farko kunya da tsoro sun kama ni kuma na kasa gaya wa kowa.”

BA LAIFIN KI BA NE

Har yanzu, Annette tana ganin cewa abin da ya faru da ita laifinta ne. Ta ce: “Ina ta tunanin abin da ya faru da ni a daren. Ina gani kamar da na daɗa ture shi da ƙarfi sosai. Amma gaskiyar ita ce, sa’ad da ya soke ni da wuƙa, sai jikina ya mutu gaba ɗaya. Na kasa yin kome, amma har yanzu ji nake da na yi wani abu.”

Natalie ma tana ganin laifinta ne. Ta ce: “Da na sani da ban yarda da shi ba, iyayena sun kafa doka cewa a duk lokacin da na je wasa a waje, in tabbata cewa ina tare da ƙanwata, amma ban saurare su ba. Saboda haka, ina ganin ni ne na ba wa maƙwabcinmu damar cin zarafina. Abin da ya faru ya shafi iyalina kuma hakan ya sa su baƙin ciki sosai. A ganina, laifina ne. Abin yana damuna sosai.”

Idan kina irin tunanin da Annette ko Natalie suke yi, ki tuna cewa duk wadda aka yi wa fyaɗe ba da son ta aka yi mata ba. Wasu mutane suna ganin wannan al’amari ba wani abin tayar da hankali ba ne, sukan ba da hujjar cewa matan ne suka jawo hakan. Amma babu macen da ta cancanci a yi mata fyaɗe. Idan an taɓa yi miki fyaɗe, ba laifinki ba ne!

Gaskiyar ita ce, bai da sauƙi mutum ya amince cewa “ba laifinsa ba ne.” Wasu da aka ci zarafinsu ba sa gaya wa kowa abin da ya faru. Saboda haka, suna fama da baƙin ciki don suna ganin cewa laifinsu ne. Amma wane ne zai cutu idan kika yi shiru, ke ce ko kuma wanda ya ci zarafinki? Kina bukatar ki ɗauki mataki nan da nan.

KI GAYA WA MUTANE ABIN DA YA FARU

Littafi Mai Tsarki ya ce lokacin da amintaccen bawan Allah Ayuba yake shan wahala, ya ce: “Zan . . . yi magana cikin ɓācin raina.” (Ayuba 10:1) Gaya wa wanda kika amince da shi abin da ya faru zai sa ki rage baƙin ciki kuma za ki amfana.

Bai kamata ki yi shiru kuma ki riƙa fama da baƙin ciki ba. Ki gaya wa wadda kika amince da ita, kuma hakan zai taimaka miki

Annette ta shaida cewa hakan gaskiya ne. Ta ce: “Na gaya wa wata abokiyata abin da ya faru kuma ta ce in gaya wa dattawan ikilisiyarmu. Na yi hakan. Sun tattauna da ni sau da sau kuma suka gaya min cewa abin da ya faru ba laifina ba ne sam.”

Natalie ta gaya wa iyayenta game da yadda aka yi mata fyaɗe. Ta ce: “Sun ƙarfafa ni. Sun ce in riƙa tattauna batun a kai a kai kuma hakan ya taimaka min in rage baƙin cikin da nake yi.”

Ƙari ga haka, Natalie tana yin addu’a kullum kuma ta sami ƙarfafawa a sakamakon hakan. Ta ce: “Yin addu’a yana taimaka min, musamman ma a lokutan da nake ganin ba zan iya gaya wa mutane abin da ya faru ba. Idan na yi addu’a, hakan yana taimaka min in faɗi abin da ke zuciyata. Hakan ya sa na kasance da kwanciyar hankali.”

Ke ma za ki ga cewa akwai “lokacin warkarwa.” (Mai-Wa’azi 3:3) Ki kula da kanki da kyau. Ki riƙa hutawa. Mafi muhimmanci, ki dogara ga Jehobah don shi ne mai ƙarfafa mu a dukan wahalar da muke fuskanta.—2 Korintiyawa 1:3, 4.

IDAN KIN ISA SOMA FITA ZANCE

Idan ana matsa miki ki yi abin da bai dace ba, kina iya cewa, “Ka daina!” ko kuma “Kada ka sake taɓa ni!” Kada ki yi shiru saboda kina tsoron kada saurayinki ya bar ki. Idan ya rabu da ke don haka, ki san cewa bai kamata ki fita zance da shi ba! Kina bukatar namiji mai hankali, wanda zai daraja ki da kuma ra’ayinki.

WASA KWAKWALWA GAME DA CIN ZARAFI TA HANYAR LALATA

Coretta ta ce: “A makarantar sakandare, wasu samari sukan ja rigar mamata daga baya kuma suna zolayata, wai zan ji daɗi idan suka kwana da ni.”

Kana jin cewa waɗannan samarin suna

  1. Zolayarta ne?

  2. Yi mata kwarkwasa?

  3. Cin zarafinta?

Candice ta ce: “Wani yaro ya soma gaya mini maganar banza a cikin bas kuma ya rungume ni. Na buge hannunsa kuma na ce masa ya bar inda nake. Sai ya soma kallo na kamar ni wata mahaukaciya ce.”

Me kake tsammanin wannan yaron yake yi wa Candice?

  1. Zolayarta ne?

  2. Yi mata kwarkwasa?

  3. Cin zarafinta?

Bethany ta ce: “Shekarar da ta shige, wani yaro yana ta gaya mini cewa yana so na kuma yana so mu fita zance duk da cewa na sha gaya masa a’a. Wasu lokatai, yana shafa hannuna. Na gaya masa ya daina, amma ya ƙi. Wata rana sa’ad da nake ɗaure igiyar takalmata, sai ya bugi ɗuwawuna.”

A ra’ayinka, wannan yaron yana:

  1. Zolayarta ne?

  2. Yi mata kwarkwasa?

  3. Cin zarafinta?

Amsar dukan tambayoyin nan ita ce na 3.

Ta yaya cin zarafi ya bambanta da kwarkwasa ko zolaya?

Wanda yake cin zarafin mace yana yin hakan ne ba da son ranta ba. Yakan ci gaba da yin hakan duk da cewa ta gaya masa ya daina.

Cin zarafi mugunta ne. Kuma zai iya kai ga fyaɗe.

[Ƙarin bayani]

^ sakin layi na 4 Ko da yake an yi magana ne a kan ’yammata kawai, maza ma za su iya amfana daga ƙa’idodi da kuma taimakon da ke cikin wannan talifin.