Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 1

Allah Ya Yi Sama da Duniya

Allah Ya Yi Sama da Duniya

Jehobah ne ya yi mu. Ban da haka ma, shi ya yi dukan abubuwan da za mu iya gani da waɗanda ba za mu iya gani ba. Ya fara yin mala’iku da yawa kafin ya yi abubuwan da za mu iya gani. Ka san su waye ne mala’iku? Mala’iku halittu ne da Allah ya yi kuma suna da irin jikinsa. Ba za mu iya ganin su ba, kamar yadda ba za mu iya ganin Allah ba. Mala’ika na farko da Jehobah ya yi ne ya zama mataimakinsa. Wannan mala’ikan ne ya yi aiki tare da Jehobah wajen yin taurari da rana da sauran abubuwa. Ɗaya daga cikin abubuwan da suka yi shi ne wannan duniyar mai kyau da muke ciki.

Bayan haka, sai Jehobah ya shirya duniya don mutane da dabbobi su ji daɗin zama a ciki. Ya sa rana ya yi haske a duniya. Ya yi duwatsu da teku da kuma koguna.

Mene ne ya faru bayan haka? Jehobah ya ce: ‘Zan yi ciyayi da bishiyoyi.ʼ Sai ’ya’yan itatuwa da ciyayi da fulawa iri-iri suka soma fitowa a ƙasa. Bayan haka, Jehobah ya yi dukan dabbobi. Ya yi waɗanda suke tashi a sama da masu tafiya a ruwa da kuma waɗanda suke tafiya a ƙasa. Ya yi ƙananan dabbobi kamar su zomo da kuma manyan dabbobi kamar su giwa. Wace dabba ce ka fi so?

Sai Jehobah ya gaya wa mala’ika na farko da ya yi cewa: “Bari mu yi mutum.” Mutane za su bambanta da dabbobi domin za su iya yin abubuwa iri-iri. Za su iya yin magana da dariya da kuma wasa. Su ne za su kula da duniya da kuma dabbobin da ke cikinta. Shin ka san sunan mutumin da Allah ya fara yi? Bari mu gani.

‘A farko Allah ya halicci sama da ƙasa.’​—Farawa 1:1