Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 4

Fushi Ya Jawo Kisan Kai

Fushi Ya Jawo Kisan Kai

Adamu da Hauwa’u sun haifi yara da yawa bayan da aka kore su daga lambun Adnin. Kayinu ne yaronsu na farko, kuma shi manomi ne. Na biyun kuma mai suna Habila, yana kiwon dabbobi.

Wata rana sai Kayinu da Habila suka yi wa Jehobah hadaya. Ka san abin da hadaya take nufi? Wata irin kyauta ce da ake ba Allah. Jehobah ya karɓi hadayar Habila amma bai karɓi na Kayinu ba. Sai Kayinu ya yi fushi sosai. Jehobah ya ja kunnen Kayinu kuma ya gaya masa cewa idan bai bar fushin nan ba, zai yi wani abin da ba kyau. Amma Kayinu bai ji ba.

Maimakon haka, ya gaya wa Habila: ‘Ka zo mu je gona tare.’ Da suka je gonar kuma Kayinu ya ga ba kowa a wurin, sai ya kashe ƙaninsa Habila. Mene ne Jehobah ya yi? Jehobah ya hukunta Kayinu, kuma ya kore shi zuwa wani wuri mai nisa. Bai yarda Kayinu ya sake dawowa wurin ’yan’uwansa ba.

Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? Za mu iya yin fushi idan ba a yi mana abubuwan da muke so ba. Idan mun ga cewa mun soma yin fushi ko kuma idan wasu sun ga muna fushi kuma suka gaya mana mu daina, zai yi kyau mu daina fushin don kada mu yi laifi.

Da yake Habila ya ƙaunaci Jehobah kuma ya yi abin da yake da kyau, Jehobah ba zai taɓa mantawa da shi ba. Allah zai tayar da Habila a lokacin da aka mayar da duniya aljanna.

‘Ka je ku shirya da ɗan’uwanka, sa’an nan ka zo ka miƙa hadayarka.’​—Matta 5:24