Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI 9

Sun Haifi Da!

Sun Haifi Da!

Ibrahim da Saratu sun daɗe da yin aure. Sun bar gidansu mai kyau da ke ƙasar Ur kuma yanzu suna zama a cikin tanti. Duk da haka, Saratu ba ta yi gunaguni ba domin ta dogara ga Jehobah.

Saratu ta so ta samu nata yaro har ta gaya wa Ibrahim cewa: ‘Idan baiwata Hajaratu ta haifi yaro, yaron zai zama kamar nawa.’ Daga baya, sai Hajaratu ta haifi yaro mai suna Isma’ilu.

Bayan shekaru da yawa, sa’ad da Ibrahim ya kai ɗan shekara 99, Saratu kuma tana da shekaru 89, sai wasu baƙi uku suka zo gidansu. Sai Ibrahim ya ce su zo su huta a ƙarƙashin bishiya kuma ya ba su abinci. Ka san ko su waye ne waɗannan baƙin? Mala’iku ne! Sun gaya wa Ibrahim cewa: ‘Shekara mai zuwa a daidai wannan lokacin, kai da Saratu za ku haifi ɗa.’ Saratu kuma tana cikin ɗaki tana jin abin da mala’ikun suke faɗa. Sai ta soma dariya a cikin zuciyarta tana cewa: ‘Zai yiwu tsohuwa kamar ni in haihu?’

Bayan shekara ɗaya, sai Saratu ta haifi yaro kamar yadda Jehobah ya ce. Ibrahim ya ba shi suna Ishaƙu kuma ma’anar sunan shi ne “Dariya.”

Sa’ad da Ishaƙu ya kai ɗan shekara biyar, Saratu ta lura cewa Isma’ilu yana yawan tsokanarsa. Sai Saratu ta gaya wa Ibrahim cewa ya kori Hajaratu da Isma’ilu daga gidan domin ba ta son kome ya sami yaronta. Ibrahim bai ji daɗin maganar ba. Amma Jehobah ya ce wa Ibrahim: ‘Ka yi abin da Saratu ta ce. Zan kula da Isma’ilu. Amma ta hanyar Ishaƙu ne zan cika alkawuran da na yi.’

‘Ta wurin bangaskiya, Saratu da kanta ta sami ikon yin juna biyu . . . tun da ta san mai-aminci ne wanda ya yi alkawari.’​—Ibraniyawa 11:11