Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 10

Ku Tuna da Matar Lutu

Ku Tuna da Matar Lutu

Lutu ya zauna da kawunsa Ibrahim a ƙasar Kan’ana. Daga baya, sai Ibrahim da Lutu suka sami dabbobi da yawa kuma wurin da suke ya yi musu kaɗan. Ibrahim ya gaya wa Lutu cewa: ‘Ba zai yiwu mu ci gaba da zama tare ba. Don Allah a cikin wuraren nan, ka zaɓi wanda ka fi so.’ Ibrahim bai yi son kai ba, ko ba haka ba?

Lutu ya ga wani wuri mai kyau kusa da wani birnin da ake kira Saduma. Akwai ruwa da kuma ciyawa mai kyau da dabbobi za su ci. Sai ya zaɓi wurin kuma ya ƙaura da iyalinsa zuwa wurin.

Mutanen birnin Saduma da Gwamarata ba sa yin abu mai kyau. Jehobah ya ce zai halaka su don muguntarsu. Amma Jehobah ya aika mala’iku biyu don su ceci Lutu da iyalinsa. Sai mala’ikun suka ce: ‘Ka tashi! Ka fita daga birnin nan! Jehobah zai halaka shi.’

Lutu bai bar birnin da sauri ba. Yana ta ɓata lokaci. Sai mala’ikun suka riƙe hannayensa da na matarsa da kuma na yaransa, suka fitar da su daga birnin kuma suka gaya musu cewa: ‘Ku gudu! Kada ku kalli baya don ku tsira. Idan kuka juya, za ku mutu!’

Sa’ad da suka kai wani birni mai suna Zoar, sai Jehobah ya sa wuta ta halaka Saduma da Gwamarata. An halaka biranen nan gabaki ɗaya. Da matar Lutu ta ƙi yin biyayya kuma ta juya baya, sai ta zama tarin gishiri! Amma Lutu da yaransa sun tsira don sun yi biyayya ga Jehobah. Babu shakka, sun yi baƙin ciki don rashin biyayyar da ta yi. Amma sun yi murna don sun yi abin da Jehobah ya gaya musu.

“Ku tuna da matar Lutu.”​—Luka 17:32